Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu biyu da ke hana sababbin jaruman Kannywood haskawa
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Shekaru da dama ana ta samun koke-koke a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kan yadda ake yawan maimaita amfani da wasu fitattun fuskoki, yayin da sababbin jarumai ke fama da ƙarancin damar nuna bajintarsu.
A cikin masana'antar da ta shafe shekaru tana samar da manyan taurari, har yanzu ana yawan ganin jaruman da suka daɗe suna kan gaɓa, ciki har da waɗanda suka shafe sama da shekaru 20 suna haskawa a fagen fim.
Daga cikin waɗanda suka daɗe suna jan zarensu a masana'antar akwai irin su Ali Nuhu da Yakubu Muhammad da Adam A. Zango da wasu mata da za a iya cewa sun ga jiya sun ga yau.
Fina-finai masu dogon zango da masana'antar ta koma yi ne aka yi tunanin za su kasance dama ga sababbin jarumai, musamman tun bayan nasarar da fim ɗin "Izzar So" ya samu wajen fitar da jarumai.
Wannan ne ya sa wasu ke ganin cewa matasan da ke da baiwa ba su samun cikakkiyar damar da za su nuna kansu.
Sai dai manyan sun sha nanata cewa masana'antar na da faɗi, inda suke cewa idan kowa ya dage, ya kuma yi haƙuri akwai damarmaki da kowa zai iya samu domin nuna fasaharsa.
Laifin waye?
Sai dai masu ruwa da tsaki a harkar sun daɗe suna tafka muhawa kan asalin abin da hana sababbin jaruman samun damar yin rawar gaban hantsinsu, musamman afina-finai masu ƙarfi da tasiri.
Dokta Muhsin Ibrahim, malami ne a Jami'ar Cologne da ke Jamus, kuma masani kan harkokin Kannywood, wanda ya bayyana cewa akwai wasu dalilai da ke hana sababbin jarumai samun irin wannan dama.
Ya ce matasan jaruman masana'antar suna da ƙoƙari sosai idan aka ba su dama, amma dai a cewarsa akwai abubuwa biyu da ke kawo cikas wajen samun wannan damar.
Masanin ya ce akwai wasu abubuwa guda biyu da yake tunani suna haifar da haka:
"Dalili na farko shi ne tsoron masu shirya fina-finai na gwada sabbin fuskoki saboda harkar fim sana'a ce ta kasuwanci," in ji shi.
A cewarsa, masu zuba jari a fim suna kashe makudan kuɗaɗe wajen shirya fim, don haka a cewarsa suke son amfani da jaruman da suka riga suka samu karɓuwa a wajen jama'a domin rage hatsarin asarar kuɗinsu.
"Masu shirya fim suna kallon fuskar jarumi a matsayin wani ɓangare na kasuwanci. Idan ka saka fuskar da mutane suka sani, akwai yiwuwar fim ɗin ya samu masu kallo. Amma idan ka saka sabuwar fuska da ba a sani ba, akwai fargabar ko kuɗin da aka kashe zai dawo."
Ya ƙara da cewa dalili na biyu shi ne ko a lokutan da ake ba sababbin jarumai dama, wasu lokuta ba a yin hakan bisa cikakken tsarin tantance ƙwarewa.
A cewarsa, a Kannywood akwai abin da ake kira "gidaje" ko alaƙa da ke tasiri wajen samun dama. Wasu jarumai na iya samun damar shiga manyan fina-finai saboda kusancinsu da wasu fitattun mutane a masana'antar.
"Wani lokaci ana duba ko jarumi yana cikin gidan wani fitaccen mutum ne ko a'a. Idan ba ka da wannan alaƙar, ko da kana da ƙwarewa, zai iya zama da wahala a gwada ka."
Ya bayyana cewa a wasu lokuta ba ƙwarewa kaɗai ake dubawa ba, har da irin dangantakar da ke tsakanin jarumi da mai shirya fim, da kuma irin shaharar da jarumin yake da ita a lokacin.
"Akwai abin da ake kira 'celebrity capital' — wato darajar jaruman ke da ita a idon jama'a. Wannan ma yana taka muhimmiyar rawa wajen samun damar shiga manyan ayyuka."
Sai dai masu sukar wannan tsarin na ganin cewa yawan dogaro da tsoffin taurari na iya rage damar gano sabbin hazaka da za su iya zama manyan taurari a nan gaba.
Yayin da masana'antar Kannywood ke ci gaba da sauyawa, tambayar da ke ci gaba da jan hankali ita ce: shin akwai buƙatar ƙarin bude ƙofa ga sababbin jarumai domin su maye gurbin tsoffin taurari, ko kuwa kasuwar fim za ta ci gaba da dogaro da fitattun fuskokin da jama'a suka riga suka sani?
Yaya makomar masana'antar?
Wani babban abin da ke jan hankalin masu ruwa da tsaki a masana'antar shi ne makomar Kannywood ɗin idan ba a riƙa amfani da sababbin jarumai ba domin shirya su maye gurbin manya.
Dr Muhsin ya yi gargaɗin cewa rashin bai wa sababbin jarumai isasshen dama na iya jefa masana'antar cikin matsala a nan gaba.
A cewarsa, idan aka ci gaba da dogaro da tsoffin taurari ba tare da horas da sabbin fuskoki ba, za a iya shiga wani yanayi da za a nemi matasa cikin gaggawa lokacin da manyan jarumai suka rage tasiri wataƙila saboda shekaru.
Ya bayyana cewa baiwa matasa dama tun da wuri na ba su damar samun gogewa, ƙwarewa da kuma fahimtar yadda masana'antar ke aiki.
"Akwai matsala idan ba a damawa da matasan jarumai. Za a zo lokacin da shekaru za su yi wa manyan jarumai tasiri, sai a koma neman matasa cikin gaggawa alhali ba su samu isasshen gogewa ba. Wannan na iya zama babbar matsala ga makomar masana'antar."
Ya yi kira ga masu shirya fina-finai da su riƙa samar da tsari na bai wa sabbin jarumai dama domin tabbatar da ci gaban Kannywood da kuma samar da taurarin da za su maye gurbin wadanda suka dade suna kan gaba, inda ya ƙara da cewa, "muna fata za su gyara."