Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa kotu ta soke hukuncin sanya Hijabi a makaranta da ke Oyo
Kotun daukaka kara da ke Ibadan a kudancin Najeriya, ta soke hukuncin da kotun jihar Oyo, da ke kudu maso yammacin ƙasar, da ta bai wa dalibai mata musulmai na makarantar International School (ISI) damar sanya hijabi tare da kayan makaranta.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma'a, bayan ta saurari karar da shugaban makarantar ya shigar kan hukuncin kotun jihar da aka yanke a ranar 22 ga Mayu, 2024.
Lamarin ya samo asali ne daga karar da dalibai mata Musulmai 11 suka shigar, inda suka zargi makarantar da tauye musu 'yancin su na hana su sanya hijabi a matsayin kayan makaranta.
Mai shari'a Biobele Georgewill, tare da goyon bayan mai shari'a K.I. Amadi, sun ce makarantar ISI ta Ibadan makaranta ce mai zaman kanta, ba ta cikin jerin makarantun gwamnati da hukuncin kotun koli kan sanya hijabi ya shafa.
Mai shari'ar ya bayyana cewa hukuncin kotun kolin da ya amince da sanya hijabi ya shafi makarantar gwamnati a jihar Legas, ba makarantu masu zaman kansu ba.
Ya kara da cewa 'yancin yin addini abu ne na mutum, wanda za a iya a takaita shi da yardar mai shi.
A cewarsa, dalibai sun amince da bin dokokin makarantar, ciki har da tsarin tufafi, tun lokacin da suka yi rijistar shiga makarantar.
Sai dai mai shari'a Fadawu Umar, ya yi watsi da hukuncin, inda ya ce karar da shugaban makarantar ya shigar ba ta da tushe, sannan ya goyi bayan hukuncin kotun jihar Oyo da ya amince da 'yancin dalibai matan na sanya hijabi a makarantar.