Abubuwa 7 da suka taimaka wa Adeleke lashe zaɓen Osun

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar da Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.

Adeleke ya fafata ne da sauran ƴan takara 14, ciki har da ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Oyebamiji, wanda shi ne babban abokin hamayyarsa a zaɓen.

Babban jami'in zaɓen da ya sanar da sakamakon a safiyar ranar Lahadi, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya ce Adeleke ya samu ƙuri'a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815, inda Adeleke ya samu tazarar ƙuri'a 66,252.

To, mene ne ya taimaka wa Adeleke samun nasarar komawa kujerar gwamnan Osun? Muhawarar da ake yi ke nan ganin gwamnan wanda zai koma karo na biyu ba ɗan jam'iyya mai Mulki a matakin tarayya ba ne

Dokta Murtala Adogi Mohammed, masanin harkokin siyasa ne da tsare-tsaren kasuwanci, ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa guda bakwai da suka taimaka wa gwamnan sake samun nasara.

A cewarsa, ''Daga shekarar 2016 zuwa 2021, yayin da nake aiki da ofishin shiyya na UNICEF na Kudu maso Yamma a Akure, na gudanar da wasu nazarce-nazarce kan yanayin siyasa da tattalin arziki a jihohin Kudu maso Yamma guda shida. Daga abubuwan da na fahimta a lokacin, ga wasu daga cikin abubuwan da nake ganin suka taka muhimmiyar rawa wajen sakamakon zaɓen Osun da aka kammala."

Tausayin jama'a

A cewar Murtala, yadda aka yi amfani da ƙarfin gwamnatin tarayya da siyasa a lokacin yaƙin neman zaɓen ya haifar da wani yanayi da ya sa ake kallon Gwamna Ademola Adeleke da al'ummar Osun a matsayin waɗanda ake takala da neman takawa daga sama.

Wannan yanayi, a ganinsa, ya haifar da tausayi a tsakanin jama'a tare da ƙarfafa kishin jihar.

A maimakon hakan ya raunana Adeleke, "sai ya mayar da zaɓen tamkar wata fafutukar kare martabar jihar da ƴancin jama'ar Osun," in ji Dr Murtala.

Tasirin mawaƙi Davido

Mawaƙi Davido ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen ƙara tagomashin yaƙin neman zaɓen.

Murtala ya ce shaharar mawaƙin da kuma yadda yake iya jawo ɗimbin jama'a sun taimaka matuƙa wajen tabbatar da Gwamna Adeleke ya sake samun nasara a zaɓen.

An dai ga yadd mawaƙin, wanda ɗa yake wajen gwamnan yake ta fafutika a lokacin yaƙin zaɓen.

Ko a kusa da zaɓen, matashin mawaƙi ya rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban ƙasar Amurka Donald Trump a shafin X game da zaɓen.

Rawar da al'ummar Osun suka taka

Wani abu da Murtala ya ce ya yi tasiri sosai shi ne abin da ya kira jarumtar al'ummar Osun.

A cewarsa, masu kaɗa ƙuri'ar sun nuna jajircewa wajen fuskantar duk wani yunƙuri na tsoratar da su.

Sai dai ya ce duk da haka, sun tsaya kai fata wajen tabbatar da cewa sun yi zaɓe, sun kare ƙuri'arsu har aka ak samu nasara.

Dabarun yaƙin zaɓe daga tushe

Masanin harkokin gwamnatin ya ce al'ummar jihar sun yi amfani da barkwanci da waƙoƙi da habaici wajen isar da saƙonnin siyasa da nuna ƙorafe-ƙorafensu cikin nasara.

A cewarsa, irin waɗannan dabaru sun taimaka wajen ƙara kuzarin magoya bayan Adeleke tare da raunana wasu daga cikin saƙonnin yaƙin neman zaɓen abokan hamayyarsa.

Ayyukan raya ƙasa

Murtala ya kuma alaƙanta nasarar Adeleke da yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ƙaddamar da ayyuka da dama gabanin zaɓen.

A ganinsa, ƙaddamar da ayyukan sun ƙara wa gwamnan damar bayyana irin abubuwan da gwamnatinsa ta ce ta cimma, tare da ƙarfafa fahimtar cewa akwai ayyukan da ake gani a ƙasa.

Shiri domin muhawara

Wani muhimmin abu da ya yi nuni da shi shi ne yadda tawagar Adeleke ta shirya shi domin muhawarar 'yan takara.

Ya ce masu ba shi shawara sun inganta saƙonnin da yake son isarwa, sun yi hasashen tambayoyi da ƙalubalen da zai iya fuskanta, sannan suka shirya shi yadda ya kamata su yi.

A cewar Dr Murtala, yadda Adeleke ya gudanar da muhawarar ya wuce abin da wasu daga cikin jama'a suka yi tsammani, lamarin da ya taimaka wajen ƙalubalantar masu shakku kan ƙwarewarsa da iya shugabancinsa.

Daɗaɗɗiyar ƙauna ga iyalan Adeleke

A cewar Murtala, nasarar Adeleke ba ta ta'allaƙa kawai da shi kaɗai ba, inda ya ƙara da akwai daɗaɗɗen tarihin alaƙa mai kyau tsakanin iyalan Adeleke da al'ummar Osun.

Ya ce wannan ƙauna ta samo asali tun kafin zamanin Ademola Adeleke, kuma ta ci gaba daga tsara zuwa tsara.

Darasin da aka koya

A ƙarshe, Murtala ya ce babban darasin da zaɓen ya nuna shi ne cewa ba lallai ne ƙarfin siyasa kaɗai ya isa wajen lashe zaɓe ba.

A cewarsa, nasara na iya dogara ne kan amincewar jama'a, alaƙar ɗan takara da masu kaɗa ƙuri'a, shiri mai kyau, ayyukan da ake iya gani da kuma jajircewar al'umma wajen kare zaɓin da suka yi.

Wasu dalilan

Bayan waɗannan dalilan da Dr Murtala ya bayyana, wasu na ganin akwai wasu abubuwa da suka taka rawa.

Daga cikin akwai rahotannin da ke nuna cewa gwamnan ya yi ƙoƙari matuƙa wajen biyan albashin ma'aikata da walwalarsu.

Haka kuma an yaba wa ƙoƙarin INEC, musamman wajen amfani da na'urar BVAS wajen tattara sakamakon zaɓen, wanda ake tunanin ya taimaka wajen rage maguɗin zaɓe.

Wane ne Ademola Adeleke?

Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar Osun a halin yanzu, an haife shi ne a ranar 13 ga Mayun 1960 a garin Ede, jihar Osun.

Ya fito daga cikin iyali mai tasiri a siyasa - Mahaifinsa shi ne Sanata Raji Ayoola Adeleke, yayin da mahaifiyarsa, Nnenna Esther Adeleke, ta fito daga yankin Akwete da ke ƙaramar hukumar Ukwa West a jihar Abia.

Ademola Adeleke ya shiga harkar siyasa a shekarar 2001 tare da ɗan'uwansa, Sanata Isiaka Adeleke, wanda ya rasu a watan Afrilun 2017.

Bayan rasuwar ɗan'uwansa, Ademola Adeleke ya tsaya takarar kujerar Sanatan Osun ta Yamma , inda ya samu nasara a zaɓen cike gurbi na shekarar 2017 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Kafin komawarsa PDP a watan Afrilun 2017, Adeleke ya kasance mamba a jam'iyyar APC.

Daga baya, ya shiga takarar gwamnan jihar Osun, inda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyarsa bayan ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Akin Ogunbiyi, da ƙuri'u bakwai kacal. Bayan haka ya tsaya takarar gwamna a zaɓen da aka gudanar a ranar 23 ga Yulin 2018.

A watan Disamban 2025, Adeleke ya koma jam'iyyar Accord, inda ya samu tikitin takarar gwamna domin neman wa'adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar Osun.

A ranar 22 ga Maris, 2019, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar zaɓe ta ƙasar ta ce bai kammala ba. Amma daga bisani, a ranar 5 ga Yulin 2019, Kotun Ƙolin Najeriya ta soke wannan hukunci tare da tabbatar da Gboyega Oyetola a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun na 2018.

A zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga Yulin 2022, Adeleke ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, inda ya samu nasara kan gwamna mai ci a wancan lokaci, Gboyega Oyetola.

Adeleke ya samu ƙuri'u 402,979, yayin da Oyetola ya samu 375,027, abin da ya ba shi damar lashe zaɓen.

Ademola ya yi karatun Kimiyyar Siyasa (Political Science) a Jami'ar Jacksonville State University da ke jihar Alabama, Amurka.

Ademola Adeleke fitaccen ɗan kasuwa ne kuma ƙwararren mai gudanarwa.

A cewar bayanan da aka bayar, ya riƙe mukamin Babban Darakta na kamfanin Guinness Nigeria Plc tsakanin shekarun 1992 zuwa 1999.

Haka kuma, ya kasance Babban Daraktan kamfanin Pacific Holdings Limited daga shekarar 2001 zuwa 2016. Kafin wannan, ya yi aiki da kamfanin Quicksilver Courier da ke Atlanta, jihar Georgia ta Amurka tsakanin 1985 zuwa 1989.

Adeleke ya kuma yi aiki da kamfanin Origin International LLC da ke Atlanta, Georgia, inda ya riƙe mukamin mataimakin shugaban kamfanin tsakanin 1990 zuwa 1994.