Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona na tattaunawa da Borussia Dortmund kan Adeyemi,Tottenham na harin Muani
Tottenham na son ɗan wasan tawagar ƙasar Faransa, Randal Kolo Muani, wanda ya buga mata wasa a zaman aro a kakar da ta gabata. Sai dai ana ganin Juventus, wadda itama ya yi wa wasa a matsayin aro, ita ce ke kan gaba wajen samun sa hannun ɗan wasan gaba na Paris Saint-Germain mai shekara 2. (Tuttosport - in Italian), external
Arsenal na shirin kammala cinikin fam miliyan 35 domin ɗaukar ɗan wasan gefe na kungiyar Brugge da tawagar ƙasar Girka, Christos Tzolis, mai shekara 24.(Sun), external
Barcelona ta fara tattaunawa da Borussia Dortmund kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gefe na tawagar Jamus, Karim Adeyemi, mai shekara 24.
Wannan matakin ya ƙara haifar da tambayoyi kan makomar ɗan wasan gaba na Ingila, Marcus Rashford, mai shekara 28, a Nou Camp bayan wa'adin zaman aronsa ya kare.(Sky Germany), external
Manchester United na shirin ɗaukar ɗan wasan Faransa, Manu Koné, wanda ke da sha'awar gwada ƙarfinsa a gasar Firimiya ta Ingila.
Haka kuma, Juventus a shirye take ta sayar da ɗan wasan mai shekara 25 idan aka gabatar mata da tayin da ya dace.(Teamtalk), external
Liverpool da Arsenal sun kasance a shirye, ko da ba da cikakkiyar niyya ba, wajan amincewa a mayar da ɗan wasan tsakiya na Morocco, Ayyoub Bouaddi, mai shekara 18, aro zuwa Lille idan suka samu damar ɗaukarsa a wannan bazarar.
Hakan na zuwa ne saboda ƙungiyar Lille na son ta ci gaba da riƙe ɗan wasan na karin kakar wasa guda. (Football Insider), external
Dan wasan gaba na Ingila, Mason Greenwood, na daf da komawa kungiyar Fenerbahce, bayan da kungiyar ta Turkiyya ta gabatar da tayi ga Marseille da kuma wakilan dan wasan mai shekara 24.(Sky Italy), external
Crystal Palace da Fulham na iya yin yunƙurin ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Southampton da tawagar Arewacin Ireland, Shea Charles, mai shekara 22, bayan da Leeds United ta gaza samun sa hannunsa duk da tayi biyu da ta gabatar.(Sky Sports), external
Aurelien Tchouameni, wanda Manchester United ke zawarci, ya yanke shawarar ci gaba da zama a Real Madrid, inda ake sa ran ɗan wasan tsakiya na tawagar Faransa mai shekara 26 zai tsawaita kwantiraginsa da shekara biyar.
Rahotanni sun ce Real Madrid ta ƙi amincewa da yunƙurin da Manchester United ta yi na neman ɗaukar ɗan wasan. (AS - in Spanish), external
Nottingham Forest ta tattauna da Feyenoord kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tawagar 'yan ƙasa da shekara 21 ta Netherlands, Givairo Read, mai shekara 20, wanda shi ma ke cikin jerin 'yan wasan da Manchester City ke sa ido a kansu. (Mail), external
Mai tsaron ragar Brazil da Leeds United, Lucas Perri, mai shekara 28, da kuma mai tsaron ragar Southampton da tawagar Ingila, Aaron Ramsdale, mai shekara 28, na jan hankalin ƙungiyar Torino ta gasar Serie A ta Italiya, wadda ke sha'awar ɗaukarsu a matsayin aro. (Sky Italy), external
Brentford da Tottenham na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na ƙasar Guinea, Ousmane Diabate, mai shekara 18.
Kungiyoyin biyu na ganin za su iya samun sa hannun ɗan wasan daga ƙungiyar Genclerbirligi ta Turkiyya kan kusan fam miliyan 3, tare da wasu ƙarin kuɗaɗe da za a biya idan sun cika wasu sharudda . (Mail), external
Coventry City na shirin ɗaukar ɗan wasan baya na ƙasar Switzerland Aurèle Amenda mai shekara 22, daga Eintracht Frankfurt a cinikin da darajarsa ta kai fam miliyan 17. (Bild via SportWitness), external
Ana sa ran Aston Villa za ta tsaya kan matsayarta game da mai tsaron ragar ƙasar Argentina, Emiliano Martinez, mai shekara 33, duk da cewa Juventus na zawarcinsa.(Birminghamworld), external