Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa kan yaƙin Iran da Amurka da sauran batutuwa, Litinin 13/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 13/07/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Fiye da mutum 2,700 sun mutu saboda zafin rana a Ingila da Wales

    Wani bincike ya bayyana cewa sama da mutum 2,700 , sun mutu sakamakon tsananin zafin da aka fuskanta a Ingila da Wales a tsakanin watan Mayu da Yunin da suka wuce.

    Masu bincike daga Jami'ar Imperial College da ke Landan, da Hukumar Kula da Yanayi ta Birtaniya da kuma Makarantar Koyar da kula da lafiyar al'umma ta London sun ce yanayin zafi da sauyin yanayi sun taka muhimmiyar rawa wajen yawan mutuwar mutanen.

    Rahoton ya ce mafi yawan mace-macen, sun faru ne a lokacin da aka fuskanci tsananin zafi a watan Yuni, wato lokacin da girman zafin da ya kai digiri 37.7 a ma'aunin Celsius.

    Masu binciken sun ce tsananin zafin ya ƙara nuna irin tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga lafiyar dan adam. break

  2. Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin WAEC da NECO

    Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban sakandire ta ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ilimin ƙasar ta fitar, ta ce an dakatar da shirin ne domin sake shawara game da shi da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki.

    Tun da farko ma'aikatar ta ce za ta ƙara yawan kuɗin jarrabawar biyu daga naira 27,000 zuwa 50,000 daga shekarar 2027 mai kamawa.

    Ma'aikatar ilimin ta bayyana dalilai na tattalin arziki, inda ta ce a halin tattalin arzikin da ake ciki 27,000 ba zai iya biyan buƙatun jarrabawa ba.

    Matakin ya haifar da suka da muhawara daga ƴanƙasar da dama, waɗanda ke ganin shirin zai ƙara yawan kuɗin jarrabawar zai ƙara yawan ɗaliban da za su daina zuwa makaranta.

    Inda aka riƙa kiraye-kiraye ga gwamnati da ta jingine shirin nata.

    Ma'aikatar ta ce ta yaba wa shawarwarin da ta samu kan batun daga ƴanƙasar.

  3. An yanke wa shugaban RSF hukuncin ɗaurin rai da rai a Sudan

    Wata kotu a jihar Port Sudan, da ke ƙasar Sudan ta yanke wa jagoran RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da ''Hemedti", hukuncin ɗaurin rairai da rai.

    A wata shari'a da aka yi a bayan Hemedti, wanda bai halarci kotun ba, an same shi da laifin aikata kisan ƙare dangi da laifukan yaƙi da laifukan jin ƙai da kuma hare-hare kan fararen hula.

    Hukuncin kotun da aka yanke ranar Lahadi 12 ga watan Yulin 2026, shi ne mafi girma da aka yi wa jagoran na RSF tun bayan fara yaƙin a 2023.

    Shari'ar ta mayar da hankali ne kisan da aka yi w gwamnan Yammacin Darfur, Khamis Abbakar, a shekarar 2023.

    An zargin garkuwa da shi sannan aka kashe shi bayan da ya zargi dakarun RSF da aika kisan ƙare dangi.

    Hukuncin ya kuma haɗa da wasu manyan jami'ar RSF, ciki har da ƴan'uwan Hemedti, Abdelrahim Dagalo da Algoney Dagalo, duk a bayan idonsu.

  4. Mun kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran ta ce ta kai hari kan wata cibiyar kula da jiragen yaƙin Amurka da ke Bahrain.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, IRGC ta ce ta kai hare-hare kan cibiyar gyaran jirage masu saukar ungulu da jiragen yaƙi na P-8 da kuma cibiyar kula da jirage marasa matuƙa da ke sansanin sojojin Amurka na Sheikh Issa da ke Bahrain.

    Haka kuma rundunar juyin juya halin ta ce ta kai hari kan tankokin mai da ke sansanin sojin saman Amurka na Prince Hassan da ke ƙasar Jordan.

    ''Haka kuma mun kai hari kan na'urorin tsaron samaniya da ke sansanin Ali Salem a ƙasar Kuwait da kum sansanin sojin sama na Ahmed Al-Jaber.

    Zaman ɗarɗar tsakanin Iran da Amurka kan iko da mashigar Hormuz na ci gaba da ƙaruwa a ƴankwanakin nan.

  5. Amurka na da damar ƙwace mashigar Hormuz - CENTCOM

    Tsohon babban kwamandan rundunar sojin Amurka mai aiki da Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, Janar Frank McKenzie (mai ritaya) ya ce sojojin Amurka na da ƙarfin da za su ƙwace iko da mashigar Hormuz, idan shugaban Amurka ya ga damar yin hakan.

    Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta CBS, tsohon janar ɗin ya ce samun iko da mashigar Hormuz na buƙatar aika jiragen ruwan Amurka, yana mai cewa ''sojojin ruwan Amurka ba su ga damar yin hakan ba ne, amma suna da ƙarfin hakan''.

    Msita McKenzie na kalaman ne a matsayin martani da iƙirarin da iran ta yi cewa ta rufe mashigar Hormuz tare da kai hare-hare kan jiragen ƴan kasuwa.

    Toshon Janar ya kuma bayar da shawawar ƙwace iko da tsibirin Kharg domin samun damar tattaunawa da Iran don ta buɗe mashigar ta Hormuz.

  6. Farashin mai ya fara tashi bayan musayar wutar Amurka da Iran

    Farashin ɗanyen mai ya fara ƙaruwa bayan shafe kwanaki ana musayar wuta tsakanin Amurka da Iran, da kuma samun saɓanin bayanai kan halin da ake ciki a mashigar Hormuz.

    Farashin ɗanyen mai ya ƙaru da kusan kashi uku cikin ɗari, yayin da kasuwannin hannayen jari a sassan Asiya suka fara faduwa.

    Taƙaddamar da ake yi kan iko da mashigar Hormuz ta daƙile yunƙurin da ake na kawo ƙarshen rikicin da ake tsakanin ɓangarorin biyu.

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta kai hare-hare kan wurare da dama a cikin dare, da nufin rage ƙarfin Iran na kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci da ke bi ta mashigar Hormuz.

    A nata ɓangaren, rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran, ta ce ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke Jordan da Bahrain da kuma Kuwait.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoroki, kamar yadda Hausa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.