Takaicin kasa kokari daga tawagar Tunisia a gasar kofin duniya ya tabbata, bayan shan kashi 4-0 a hannun Japan, wanda ya tabbatar da cewa ba za su wuce matakin cikin rukuni ba.
Shi ne wasa na 1,000 da aka buga a gasar cin kofin duniya a tarihi tun daga lokacin da aka fara wasannin cin kofin babbar gasar tamaula ta duniya.
Tunisa ta fara wasan farko a cikin rukuni da shan kashi 5-1 a hannun Sweden daga nan ta kori koci, Sabri Lamouchi tare da nada tsohon kocin Saudi Arabia Herve Renard, bai wuce mintuna hudu ba suka fara karbar kwallaye a wasan da aka buga a Guadalupe, Mexico.
Japan, wacce ta yi wasa cikin tsari mai kyau, ta bude tamaula ta hanyar kai harin gaggawa, wanda ya kare da dan wasan Crystal Palace Daichi Kamada ya zura kwallo daga kusa a filin wasa na Monterrey.
Japan ta mamaye komai fiye da Tunisia a kowane bangare a wasan, kuma ba ta fuskanci wata babbar barazana ba daga Tunisia wacce ta yi wasa cikin sauki, kuma ta dinga dakile duk wata barazana tun kan akai ga gidanta..
Da wannan sakamakon, Japan na da maki hudu yanzu kuma ana sa ran za ta iya tsallakawa a kalla a matsayin daya daga cikin mafi kyawun ƙungiyoyin matsayi na uku, amma za ta yi kokarin samun tabbacin gurbi a zagayen ƴan 32 idan suka kara da Sweden a ranar Juma’a a wasan rukuni na karshe.
Tunisia kuma za ta kara da Netherlands, wacce ke saman rukunin, a lokaci guda.