Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran ta yi atisaye a Washington

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran da ta isa Amurka da safiyar yau ta gudanar da atisaye domin shirin tunkarar wasan da za ta yi da Masar ranar Asabar a filin wasa na Jami'ar Washington da ke Seattle.

    Hukumar ƙwallon ƙafar Iran ba ta fitar da cikakkun bayanai kan wannan atisayen ba, amma ƴan wasa 29 ne suka halarta.

    Kamfanin yaɗa labarai na Iran ya ruwaito cewa, a gobe Juma'a ne tawagar ƙasar Iran za ta gudanar da atisaye a filin wasan da za ta fafata da tawagar ƙasar Masar ranar Asabar.

    Wasan da za ta yi da ta Masar a ranar Asabar, zai yanke hukunci kan makomar tawagar ƙwallon ƙafar Iran a gasar cin kofin duniya.

    Iran ta buga wasanninta biyu na farko ne a Los Angeles (Southern California), amma wasanta da Masar za a yi ne a Seattle (jihar Washington) da ke kusa da iyakar Amurka da Kanada.

  2. Masu aikin ceto na fautukar gano waɗanda suka tsira daga girgizar ƙasar Venezuela

    Akalla mutum 164 ne suka mutu yayin da wasu 700 suka jikkata bayan girgizar ƙasa guda biyu suka afku cikin ƙanƙanin lokaci tsakanin juna a babban birnin ƙasar Venezuela ranar Laraba, in ji shugaban rikon ƙwarya Delcy Rodríguez.

    Girgizar ƙasa ta biyu ta kasance ɗaya daga cikin girgizar ƙasa mafi ƙarfi da ta afku a ƙasar ta Kudancin Amurka cikin ƙarni guda, inda ta kai maki 7.5.

    Gine-gine sun ruguje, mazauna yankin kuma sun kwararo kan tituna domin tsira da rayukansu yayin da tagwayen girgizar ƙasar suka afku.

    Rodríguez ya ayyana dokar ta ɓaci sannan ta ce an dakatar da ayyuka a filin tashin jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa da sauran harkokin sufuri.

    Masu aikin ceto na fafutukar nemo waɗanda suka tsira da rayukansu da ka iya kasancewa a maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, ana kuma fargabar adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa.

  3. Ɗan takarar shugaban ƙasa a Colombia ya amince da shan kaye

    Ɗan takarar jam'iyya mai sassaucin ra'ayi a zaɓen shugaban ƙasar Colombia, Iván Cepeda, ya amince da shan kaye kwanaki uku bayan da al'ummar Colombia ta kaɗa ƙuri'u.

    Sakamakon farko da aka fitar sa'o'i bayan rufe rumfunan zaɓe ya nuna cewa Cepeda ya sah kaye ne da ƙasa da kashi ɗaya a hannun abokin hamayyarsa, ɗan kasuwa mai ra'ayin mazan jiya Abelardo de la Espriella.

    Da farko Cepeda ya ce zai jira ƙidaya na ƙarshe bisa doka - wanda har yanzu ke ci gaba da gudana - amma a ranar Laraba ya sanar da cewa "ya yanke shawarar karɓar sakamakon".

    Ya soki shugaban Amurka Donald Trump saboda goyon bayan abokin hamayyarsa de la Espriella.

  4. Trump ya buƙaci Majalisa ta amince masa kashe dala biliyan 67 kan tsaro

    Fadar White House ta buƙaci ƴan majalisar su amince ta kashe dala biliyan 87.6, akasari kan abin da ta kira "buƙatun gaggawa" da ke da alaka da yaƙin da Amurka ke yi da Iran, kwana guda bayan da majalisar dokokin ƙasar ta zartar da wani kuduri na tsawatarwa kan yaƙin.

    Galibin kuɗin - $67bn - na Ma'aikatar tsaro ta Amurka ne, in ji Fadar White House.

    Amma buƙatar na fuskantar ƙalubale a Majalisa.

    Rikicin na Iran dai na fuskantar suka daga masu kaɗa ƙuri'a gabanin zaɓen tsakiyar wa'adi na Amurka da za a yi a watan Nuwamba, ko da yake a halin yanzu tsagaita wuta na aiki.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma samu saɓani tsakaninsa da wasu ƴan jam’iyyarsa ta Republican kan batun Iran, kuma an ruwaito cewa ya yi sa-in-sa da wani sanata a ranar Laraba.

    Sanatan, Bill Cassidy na Louisiana, na ɗaya daga cikin tsirarun ƴan jam’iyyar Republican da suka bijire wa shugaban ƙasar a ranar Talata ta hanyar jefa ƙuri’a don zartar da wani mataki na neman ya dakatar da yaƙin ko kuma ya nemi amincewar majalisa kafin ya ci gaba da ɗaukar matakin soji.

  5. An jibge ƴansanda a Nairobi kan zanga-zangar matasa a Kenya

    Ƴansanda a Kenya sun rufe wasu muhimman titunan da ke shiga tsakiyar birnin Nairobi gabanin zagayowar cika shekara biyu da gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka yi a ƙasar ƙarkashin jagorancin ƙungiyar matasa ƴan bana-bakwai.

    Dubban ƴan ƙasar Kenya ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da shirin ƙara harajin da aka yi a watan Yunin 2024, wanda ya kai ga yin kutse zuwa cikin harabar majalisar dokokin ƙasar, inda daga bisani aka janye ƙudirin dokar.

    Masu zanga-zangar sun ce suna neman a hukunta masu hannu a kisan fiye da mutane 80 tare da jikkata wasu da dama yayin zanga-zangar ta 2024 da kuma zanga-zangar tunawa da ranar da aka yi a bara.

    Mutane da dama sun maƙale a kan hanya da safiyar ranar Alhamis bayan da jami’an tsaro suka tare hanyar shiga tsakiyar birnin, yayin da aka rufe kasuwanni da makarantu da dama.

    Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar da aka tsara a kan shafukan sada zumunta na intanet a manyan garuruwan da suka haɗa da Nairobi da Mombasa da kuma wasu sassan tsakiyar ƙasar Kenya.

  6. Farashin man fetur ya faɗi zuwa matakin da yake kafin yaƙin Iran

    Farashin man fetur ya faɗi zuwa matakin da ba a taɓa ganin irin sa ba tun kafin yaƙin Iran, yayin da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ke ci gaba da farfaɗowa sannu a hankali.

    Ɗanyen mai nau'in Brent ya faɗi zuwa ƙasa da dala 72.48, farashin da ya kasance a ranar da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu.

    Farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi tun lokacin da Iran ta mayar da martani ga hare-haren ta hanyar rufe mashigar ruwan da ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar mai da iskar gas a duniya.

    Farashin danyen man fetur ya ragu matuƙa tun bayan da Amurka da Iran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a ranar 17 ga watan Yuni wadda ta tanadi wa'adin kwanaki 60 don tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran ɗin da sauran matakan kawo ƙarshen yaƙin.

    Wakilan ɓangarorin biyu sun gana a ƙasar Switzerland a ƙarshen makon da ya gabata domin tattaunawa da niyyar kawo ƙarshen yaƙin, wanda ya sa Amurka ta ɗage wani ɓangare na takunkumin da ta ƙaƙaba wa Iran ɗin.

  7. Girgizar ƙasa ta kashe aƙalla mutum 32 a Venezuela, tare da jikkata 700

    Wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta afku a ƙasar Venezuela, inda ta kashe aƙalla mutum 32, yayin da wasu 700 kuma suka jikkata ta kuma lalata gine-gine a Caracas babban birnin ƙasar.

    Shaidun gani da ido sun an ji ce girgizar kasar mai ƙarfin maki 7.1 har zuwa makwabciyarta Colombia, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Tun da farko dai Hukumar gargaɗi kan guguwarTsunami ta Amurka ta fitar da sanarwar yiwuwar afkuwar guguwar a Venezuela, da tsibirin Virgin Islands da kuma British Virgin Islands, amma yanzu ta janye gargaɗin.

    Hotunan da wakiliyar BBC Vanessa Silva ta ɗauka, sun nuna yadda masu aikin ceto ke neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan wani ginin bene da ya ruguje a yankin arewacin Caracas na San Bernardino.

    Rahotannin da ba a tabbatar ba sun nuna cewa aƙalla mutum ɗaya ya mutu a unguwar.

  8. Assalamu Alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kamar yadda aka sani za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.