Da gaske ne an daina amfani da takardar naira 100?

Da gaske ne an daina amfani da takardar naira 100?
An wallafa

A baya-bayan nan ƴan Najeriya sun shiga ruɗani game da sahihancin takardar kuɗi ta naira 100.

Rahotonni daga wasu yankunan ƙasar sun nuna cewa wasu a ƙasar sun daina karɓar tsohuwar takardar kuɗi ta naira 100.

Najeriya na amfani da nau'uka biyu na takardar kuɗi ta naira 100, waɗanda duk hukumomin sun amince da su.