Jihohin arewacin Najeriya 8 da zaɓen gwamnansu zai ɗauki hankali a 2027

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da aka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamnoni a hukumance a Najeriya, alamu sun fara bayyana kan irin jihohin da ka iya zama cibiyar zazzafar fafatawa tsakanin manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya.

Masana da masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wasu jihohin za su fi ɗaukar hankali saboda sauye-sauyen siyasa da sauya sheƙar manyan ƴan siyasa zuwa wasu jam'iyyu da kuma ƙulla sabbin ƙawance.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu gwamnoni ke shirin kammala wa'adinsu na biyu, lamarin da ke buɗe kofar neman sababbin shugabanni, yayin da a wasu wuraren kuma jam'iyyun adawa ke ƙoƙarin ƙwace iko daga hannun masu mulki.

Duk da cewa har yanzu ana kan shirye-shiryen cikin gida na jam'iyyu, tuni masu neman takara da magoya bayansu suka fara nuna sha'awar shiga fafatawar, abin da ke ƙara nuna yiwuwar samun gasa mai ƙarfi.

Farfesa Abubakar Kari, mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya, kuma malami a Jami'ar Abuja ya ce siyasar jihohin za ta ɗauki hankali ne la'akari da ƙarfin siyasar jihohin.

Kano

Ana ganin zaɓen gwamnan Kano na 2027 zai kasance cikin mafi ɗaukar hankali a Najeriya saboda ƙarfin siyasar jihar, wadda ake yi wa kallo da cibiyar siyasar arewacoin Najeriya.

Fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kuma NDC, ta Dr Rabiu Kwankwaso mai matu kar tasiri a jihar.

Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na APC, wanda tsohon ɗan kwankwansiyya ne zai fafata da tsohon mataimakinsa , Comrd Aminu Abdussalam na NDC.

Tasirin manyan jiga-jigan siyasa da muhimmancin jihar a siyasar Arewa ma na daga cikin abubuwan da ke ƙara ɗaga zafin takarar.

Farfesa Kari ya ce zaɓen gwamnan Kano zakaran gwajin dafi ne na nuna ƙarfi ta tasirin Kwankwaso.

''Ƴan Kwankwasiyya na ganin zaɓen a matsayin lokacin ramako na abin da gwamna Abba ya yi musu, wanda suke ganin kujerar gwamnan tasu ce amma Abba ya kai wa APC'', in ji masanin siyasar.

Kaduna

Ita ma jihar Kaduna na daga cikin jihohimn da ake ganin siyasarta za ta yi zafi a zaɓen 2027.

Farfesa Kari ya ce gwamnan jihar Uba Sani, wanda takarar wa'adinsa na biyu a APC, na fuskantar babban ƙalubale daga masu hamayya, musamman na jam'iyyar ADC.

''Ko a zaɓen 2023 daƙayr Uba Sani ya ci zaɓe, kuma a yanzu ma zai yi takarar ne da wanda suka fafata a 2023, wanda a yanzu ke jam'iyyar ADC, tare da El-Rufai, mutumin da ya tsaya wa Uba Sani a zaben da ya gabatan'', in masanin siyasar.

Malamin Jami'ar ya ce akwai mutanen da ke ganin ya ɓata wa tsohon maigidan nasa, da waɗanda ke ƙullace da shi saboda ɗaukar mataimaki daga kudancin jihar.

Kebbi

A jihar Kebbi fafatwar za ta fi zafi ne tsakanin gwamnan jihar Comrd Nasir Idris da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami da ke takara a ADC, wanda kuma shi ke da tarin mabiya da tasiri a siyasar jihar.

''Abubakar Malami na da tasiri sosai a siyasar Kebbi, kuma ya fito yanki ɗaya ne da gwamnan jihar, wato masarautar Gwandu wanda hakan zai ƙara raba kan siyasar yankin'', in ji shi.

Malamin Jami'ar ya ce wasu masarautun jihar sun jima suna korafin mayar da su saniyar ware a gwamantin APC, da kuma rashin ɗaukar matakan magance matsalolin tsaron yankunan.

Gombe

Tuni jihar Gombe da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar ta fara ɗaukar hankalin ƴansiyasa da masu lutra da al'amuran siyasa.

Zaɓen gwamnan jihar na zuwa ne bayan kammala wa'adi biyu na mulkin Gwamna Inuwa Yahaya.

Ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin ɗantakarar APC, Jamilu Isiyaku Gwamna da tsohon ministan sadarwar ƙasar, Farfesa Ali Isa Pantami na PDP.

Farfesa Kari ya ce dama a duk lokacin da gwamna ya kammala wa'adinsa biyu, to komai zai iya faruwa.

''Gwamnan na so Jamilu Gwamna, wanda ya jima yana burin kujerar, a gefe guda kuma PDP ta tsayar da Farfesa Pantami, fitaccen malamin mai ɗumbin mabiya a fadin jihar'', in ji shi.

Masanin siyasar ya kuma ce akwai ƴansiyasar da ke adawa da Gwamna Inuwa da ke ganin za su yi matsa yankan baya.

Adamawa

Kamar dai Gombe, jihar Adamawa ma gwamnanta mai ci zai kammala wa'adin mulkinsa ne.

Masana siyasa na kallon jihar Adamawa a matsayin cibiyar siyasar arewa maso gabashin Najeriya.

A farkon wannan shekara ne gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC, wani abu da ya sauya lissafin siyasar jihar.

Farfesa Kari ya ce Adamawa jihar Atiku ce, kuma duka gwamnonin jihar shi ke kawo su, ciki har da Gwamna Fintiri mai barin gado.

''Matsalar APC a jihar ita ce shi kansa gwamnan ana zargin cewa ba wanda yake so ya tsayar ba, don haka komai zai iya faruwa'', in ji masanin siyasar.

A Adamawa akwai manyan ƴantakara huɗu masu ƙarfi da kowannensu zai iya cin zaɓen gwamnan jihar.

Baya ga ɗantakarar, APC, NDC ta tsayar da Aisha Ahemd Binani, da ake ganin tana da ɗimbin magoya baya a jihar.

Haka kuma LP ta tsayar Ishaku Elisha Abbo, wanda shi ma yana da tarin , yayain da ADC ta tsayar da Alhaji Suleiman Omar.

Bauchi

Bauchi na daga cikin jihohin da za a kai ruwa rana a zaɓen gwamna, kamar yadda Farfesa Kari ya yi bayanai.

''Tarihi ya nuna cewa a duk lokacin da gwamna uya gama wa'adinsa to jam'iyyarsa ba ta samun nasara a jihar Bauchi'', in ji shi.

Jihar da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na da yantakara guda huɗu, da suka haɗa da na APM da na APC da PRP da ADC da kuma PRP.

''Kuma duka waɗannan jam'iyyu sun tsayar da fitattun yantakara, waɗanda kowannensu zai iya cin zaɓen gwamnan jihar'', in malamin Jami'ar.

Kwara

Jihar Kwara na daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiyar Najeriya da siyasarsu ta fi ɗaukar hankali.

Jam'iyyar APC ta tsayar da Yakubu Danladi-Salihu, wanda shi ne Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, yayin da jam'iyyar NDC ta ke neman ƙwace mulki da ɗan takararta Abdulmumin Yinka Ajia, sannan ADC ta tsayar da Zakari Muhammed.

Kasancewar Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq zai kammala wa'adinsa na biyu ya buɗe filin zafin fafatawa kan wanda zai gaje shi.

Farfesa Kari ya ce duka ƴan jam'iyyar APC na jihar ba su ji dadin bai wa Danladi takara ba da gwamnan jihar ya yi.

"Don haka ne ma suka kafa wata ƙungiya da nufin yaƙar zaɓin gwamnan, kuma kungiyar na kara yin karfi sosai'', in ji shi.

Malamin jami'ar ya ce Danladi ya fito ne daga arewacin Kwara, yankin da ya fi kowane karancin masu kaɗa ƙuri'a.

''Yankin tsakiyar jihar, wato Ilorin ne ya fi kowane yanki yawan masu kaɗa ƙuri'a, kuma yansiyasar yankin sun bijire wa zaɓin gwamnan, wannan ya sa ake ganin zai fuskanci babban ƙablubale'', in ji shi.

Bisa tarihin siyasar jihar, Kwara na daga cikin jihohin da sakamakon zaɓe kan kasance mai wahalar hasashe idan manyan jam'iyyu suka shiga fafatawa.

Nasarawa

Nasarawa na daga cikin jihohin da gwamnoninsu ke kammala wa'adin mulkinsu na biyu.

Tuni manyan jam'iyyu suka tsayar da fitattun ƴan takara masu tasiri da mabiya a jihar.

APC ta tsayar da Ahmed Aliyu Wadada, yayin da PDP ke neman sake ƙwace mulki ta hannun Emmanuel David Ombugadu, sannan ADC ta tsayar da Musa Adamu Angbazo.

Farfesa Kari ya ce jihar Nasarawa akwai batutun da dama da ke tasiri a siyasar jihar, kamar ɓangaranci da addini da ƙabila da kuma ''ƴansiyasar Abuja''.

Sakamakon zaɓukan baya-bayan nan a jihar ya nuna cewa tazarar ƙuri'u tsakanin manyan jam'iyyu kan kasance kaɗan, lamarin da ke sa sakamakon zaɓe ya kasance mai wahalar hasashe.