Ƴanwasa mafi ƙwazo da marasa ƙoƙari a gasar Kofin Duniya 2026

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A gasar cin kofin duniya ta 2026, ta fara armashi da cin ƙwallaye.

Tuni aka fara samun nishadi a wasannin farko a cikin rukuni da abubuwan da ke jan hankali tun kan gasar ta yi nisa.

Daga cikin wasa 24 da aka fara, an zura ƙwallaye 75 jimilla, wanda ake cin matsakaicin ƙwallaye 3.125 a kowane wasa. Wannan shi ne mafi girman matsakaicin yawan ƙwallaye da aka zura a raga, bayan kammala zagayen farko a wasannin rukuni tun bayan gasar shekarar 1958.

Duk da damuwar da wasu suka nuna game da faɗaɗa gasar da ƙarin ƙasashen da ke halarta, ana buga karawa mai ban sha'awa da kuma cin ƙwallaye.

Daga cikin waɗanda aka, wasa tara sun ƙare da canjaras. Wannan yana nufin cewa kashi 37.5% na wasannin sun tashi babu wanda ya yi nasara.

Wannan adadi shi ne mafi girma a wannan mataki tun gasar 2010, lokacin da aka samu irin wannan kaso. Tun daga shekarar 1954, sau ɗaya kacal aka samu kaso mafi girma na yawan canjaras fiye da haka, bayan zagayen farko a wasannin rukuni.

Wadannan alkaluma suna nuna cewa gasar ta kasance mai cike da kalubale, inda tawagogi da dama ke fafatawa da juna ba tare da tazara mai girma ba a tsakaninsu a fannin taka leda.

Yanzu da aka kammala zagayen farko na wasannin rukuni, hankalin masu sha'awar ƙwallon ƙafa ya koma kan fitattun ƴan wasan da suka yi fice da kuma alkaluman da suka fi jan hankali a gasar kawo yanzu.

Waɗanda suka kan gaba a kai hare-hare kawo yanzu

Ƴan wasa shida sun kai harin cin ƙwallo sau shida a wasan farko a cikin rukuni, sai dai biyu daga cikinsu suka ƙwallo, wato Harry Kane na Ingila da kuma Lionel Messi na Argentina

Ƙwallo biyun da Kane ya ce ya sa ya yi kan-kan-kan da Gary Lineker a matakin wanda ke kan gaba a ci wa Ingila ƙwallaye a gasar cin kofin duniya mai 10 a raga.

Shi kuwa Messi da ya ci uku rigis a wasansa na farko, ya yi kafaɗa da da tsohon ɗan wasan Jamus, Miroslav Klose wanda shi ne kan gaba a tarihin cin kwallaye a gasar cin kofin duniya mai 16 a raga.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matashin ɗan wasan tawagar Turkiya, Arda Guler ya fi kowa yawan kai hare-hare kawo yanzu, wannan ya fayyace kokarin da ya sa a wasan farko a cikin rukuni a karawa da Australia.

Duk da cewa matashin ɗan wasan Real Madrid ya fi yawancin ƴan wasa hazaka da gogewa, irin damar kai hari da ya samu a wasan, ba su kasance masu sauƙin zura ƙwallo a raga ba.

Bisa ga bayanan ƙididdiga na ƙwallon ƙafa, irin waɗannan damar kai hari da ya samu yana daga cikin waɗanda a tarihi, zai iya zura ƙwallo ne sau ɗaya cikin kusan kai hari 31.

Ɗan wasan da bai tagaza ba a wasannin zagayen farko shi ne Son Heung-min wanda ya kai kari shida ba tare da cin ƙwallo ba - abin ya bayar da mamaki, domin kwarewar da yake da ita a Premier League ya kamata kwazonsa ya fi haka.

Ya zuwa yanzu a gasar Kofin Duniya ta 2026, akwai ƴan wasa 24 da ke da kashi 100 cikin 100 na cin ƙwallo daga duk kai hari, wato duk lokacin da suka buga ƙwallo sukan samu nasarar zura ta a raga.

Sai dai daga cikin waɗannan ƴan wasa 24, biyu kacal ne suka kai hari fiye da ɗaya.

Su ne:

Yasin Ayari na Sweden

Elijah Just na New Zealand

Haka kuma ƴan wasa bakwai sun samar da damar cin ƙwallaye a wasannin farko a cikin rukuni, sai dai Joshua Kimmich na Jamus shi ne kan gaba da ya bayar da ƙwallo biyu aka zura a raga daga 7-1 da suka caskara Curacao.

Su wane ne kan gaba a ƙirƙirar dama da yanka?

Ɗan wasan Sifaniya, Pedri ya yi duk yadda zai yi ya taimaki ƙasar ta ci Cape Verde, amma abin ya gagara duk da cewa shi ne kan gaba a yawan lailaya leda a wasan.

Ɗan ƙwallon Ivory Coast, Amad Diallo shi ne kan gaba a iya yanka a wannan gasar cin kofin duniya kawo yanzu.

Duk da cewa minti 34 da ya buga, sakamakon shiga wasan daga baya, ɗan wasan na Manchester United shi ne ya samu yin yanka yadda yake buƙata daga cikin ƴan wasa 32 da suka gwada haka fiye da sau biyar.

Vinícius Junior ya farkewa Brazil ƙwalon Morocco ta ci, amma ya kasa yanka ya wuce da ƙwallo daga tara daga ciki.

Kawo yanzu babu wanda ya gwada yin yanka sau huɗu ba tare da yin nasara ba kamar dan wasan Real Madrid ɗin kawo yanzu a gasar cin kofin duniya.

Waye kan gaba a iya ƙwace ƙwallo?

Idan aka zo batun ƙwace ƙwallo idan aka yi gaba da gaba to a bar wa ɗan wasan tawagar Panama, Jiovany Ramos da na Senegal, Krépin Diatta su ne kan gaba a wannan fannin a wasannin zagayen farko a cikin rukuni.

Daga cikin ƴan wasa 158 da aka yi gaba da gaba sama da 10, kuma suna nasarar ƙwace ƙwallo babu kamar ƴan wasan nan biyu.

Ɗan wasan ƙasar Bosnia and Herzegovina, Jovo Lukić, ya yi fice sosai a wasan da suka buga da Kanada ta hanyar nuna gogewa da ƙwarewa.

A wannan wasan, Lukić ya yi nasara a dukkan ƙwallo tara da ya ci kasuwar sama.

Wannan abin ya sa ya zama ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa a gasar kawo yanzu a wannan fannin, musamman idan aka kalli yadda yake iya sarrafa ƙwallaye tun daga sama.

Bisa ga ƙididdiga, babu wani ɗan wasa a wannan gasar da ya yi ƙoƙarin ƙwace ƙwallo sama da sau huɗu idan aka ci kasuwar sama — sai Lukić wanda ya yi hakan karo da dama.