Mata 6 da suka fi tasiri a nahiyar Afrika a 2026

Asalin hoton, Getty Images
Mujallar Forbes ta wallafa jerin sunayen mata 100 da suka fi ƙarfin iko da tasiri a duniya, ida ta nuna yadda suka shawo kan matsalolin da suka riƙa tararwa a lokutan da suke aiki da kuma tasowa.
Rahoton da mujallar ta wallafata nuna yadda kamfanoni suka rage taimaka wa mata a lokacin da suke aiki idan aka kwatanta da shekaru huɗu da suka gabata.
A cewar Kamfanin McKinsey da Lean, kashi 54 ne kawai na kafanoni suka mayar da burin ma'aikatansu na riƙe matsayin manajoji wani abu mai muhimmanci a wajensu, idan aka kwatanta da kashi 90 da ake da shi a baya.
Matan da ke Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi gargaɗi kan yadda ake samun ƙaruwar cin zarafi mai alaƙa da jinsi.
Majalisar ta ce yaɗuwar irin waɗannan kalaman da ake samu a intanet sun fara janyo wuraren aiki sun fara sauya yadda suke kallon mata.
Sai dai mata a faɗin duniya sun ƙi yadda gwiwarsu ta sare, ko kuma su bada kai bori ya hau.
Mo Abudu (Najeriya)

Asalin hoton, Getty Images
Mo Abudu ƴar Najeriya ce da ta yi shuhura a ɓangaren kasuwanci a ɓangaren kafafen yaɗa labarai da al'adu wadda ta sauya yadda ake bayyana labaran nahiyar Afrika ta sabuwar hanyarta da ta ƙirƙira da kuma aikin da ta ke yi zuwa ga faɗin duniya.
Ita ce ta ƙirƙiri kuma shugabar EbonyiLife Media, wadda aka fi sani da EbinyiLife Group, tana da Talabijin da ɓangaren shirya fim da na nuna salon rayuwa da kuma na kai tsaye da take yi.
A ƴan shekarun baya-bayan nan tasirin Mo Abudu ya ƙaru, saboda dogon burin da take da shi na aikin.
A 2025, mujallar TIME ta sanya ta cikin fitattun mata 100 a faɗin duniya, saboda gudunmowar da take bayarwa wajen ciyar da nahiyar Afrika gaba da yadda take fito da ayyukan basirar da mutane yankin ke yi da waɗanda ke zaune a ƙasashen ƙetare.
Tana kuma samar da wasu ci gaba da ake samu ta kafar EbonyLIfe, ciki har da shirin Afro Film, wanda ya samu kuɗin ɗaukar nauyinsa da aka yi da suka kai dala miliyan 50 somin shirya fim ɗin mai dogon zango, wanda ake yi domin masu kallo na ciki da wajen nahiya, wanda aka buɗe a birnin London.
Mary Vilakazi (Afirka ta Kudu)

Asalin hoton, Getty Images
Mary Vilakazi, da aka haifa a watan Agustan 1977, yar ƙasar Afrika ta Kudu ce da ta yi fice a fannin tattalin arzikin ƙasar.
Ta fara aiki ne a wani kamfanin bincike kuɗi na ƙasar da ake kira PwC, inda cikin gaggawa ta samu ɗaukaka cikin shekaru tana 'yar shekara 27, ɗaya daga cikin abokan hulɗar kamfanin mafi ƙarancin shekaru.
Ta kware sosai a fannin cibiyar binciken kuɗaɗe.
Da riƙe manyan muƙamai a lokacin, ciki har da ta jami'ar da ke shugabantar ɓangaren kuɗi na kamfanin Ma'adanai, kafin daga baya ta koma kamfanin MMI Holdings, inda ta riƙe muƙamin mataimakiyar shugaban kamfanin.
A 2018, Madam Vilakazi ta koma kamfanin FirstRand a matsayin shugaban fannin gudanarwa.
A watan Afrilun 2024, Ta kafa tarihin zama mace ta farko kuma baƙa ta farko da ta shugabanci kamfanin FirstRand cikin shekaru 185.
Kamfanin FirstRand shi ne mafi girman kamfanin hada-hadar kuɗi a Afrika ta Kudu ta ɓangaren ƙarfin jari a kasuwanni.
Judith Suminwa Tuluka (DRC)

Asalin hoton, Ministère du Plan de la RD Congo/X
Judith Suminwa Tuluka ƴarsiyasa ce kuma ƙwararriya kan harkokin tattalin arziƙi a ƙasar Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, wadda a watan Yunin 2024 ta kafa tarihin zama Firaiminista ta farko mace a ƙasar.
Ta fara rayuwar aikinta ne a wani kamfanin harkokin kuɗi, ta riƙe manyan muƙamai a gwamnati, sannan daga baya ta koma aiki da shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na ci gaban ƙasashe, UNDP.
Tana da ƙwarewa kan tafiyar da kuɗaɗen al'umma, yadda ake bin ƙwaƙƙwafi da tafiyar da gwamnati da kuma harkokin kasafin kuɗi.
A watan Maris 2023, gwamnatin lokacin ta naɗa ta ministar shirye-shirye.
A ranar 1 ga watan Afrilun 2024, aka naɗa ta Firaiminista, karon farko a tarihin DRC aka kuma rantsar da ita a ranar 12 ga watan Yunin 2024 bayan majalisar ƙasar ta amince da naɗin nata.
Ngozi Okonjo-Iweala (Najeriya)

Asalin hoton, Getty Images
Ngozi Okonjo-Iweala ta kasance ɗaya daga cikin fitattun masana tattalin arziƙi da kuma masu yanke hukunci kan harkokin kasuwanci a faɗin duniya.
A 2010, ta jagoranci wani kamfanin samar da kuɗaɗen tallafi, inda aka samar da dalar Amurka biliyan 49.3 na taimako da kuma kuɗaɗen da za a bayar bashi ga ƙasashe matalauta.
Bayan lokacin da ta ɗauka a gwamnati, ta koma harkokinta a matsakin duniya, inda ta jagoranci ƙungiyoyi irinsu Gavi, na rigakafi, daga 2016 zuwa 2020.
Ta jagoranci Hukumar sauyin yanayi ta duniya tare da koƙarin kawo ƙarshen matsalar sauyin yanayi.
A ranar 1 ga watan Maris ɗin 2021, aka naɗa ta shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, inda ta zama mace ta farko daga Afirka da ta riƙe matsayin.
Yadda ta yi shugabancin ya sa an sake ba ta damar jagorancin wajen karo na biyu a jere.
A ƙarshen 2024 mambobin Hukumar suka sake zaɓenta, wanda hakan ya nuna ƙwarin gwiwar da suke da shi a kanta.
Netumbo Nandi-Ndaitwah (Namibia)

Asalin hoton, Getty Images
Netumbo Nandi-Ndaitwah 'yar siaysa ce a Namibia kuma jami'ar diflomasiyya, a ranar 21 ga watan Maris 2025 ta kafa tarihin zama shugabar ƙasar Namibia ta farko.
Ta yi aikin a gwamnatin ƙasar sama da shekara 20 tare da jam'iyya mai mulki SWAPO, inda ta zama mamba tun lokacin da aka samu juyin juya halin masu sassaucin ra'ayi.
A yayin da lokacin da take aiki a matsayin 'yar siyasa da aikin gwamnati, ta riƙe matsayi daban-daban daga ministar harkokin waje zuwa mataimakiyar Firaiminista da kuma mataimakiyar shugaban ƙasa.
Mpumi Madisa (Afirka ta Kudu)

Asalin hoton, Forbes
Mpumi Madisa ta fara aiki ne a ɓangaren inshora kafin daga baya ta koma aiki a kamfanin Bidvest a 2003.
A wajen ta riƙe matsayi da dama ciki har da na shugabar alaƙa da abokan huldar kamfanin, Daraktar kula da harkokin cibiyar, Daraktar kasuwanci da sayar da kayayyaki, ta kuma riƙe shugabar da ke kula da ci gaban kasuwanci.
A Maris 2019, aka naɗa ta shugaban kamfanin na Bidvest, ta zama baƙa ta farko da ta jagoranci kamfanin cikin jerin kamfanoni 40 da ke Johannesburg.
A ƙarƙashin jagorancinta kamfanin ya samu gagarumin ci gaba.
Yanzu kamfanin ya ɗauki mutum 130,000 aiki, kuma ya faɗaɗa ayyukansu zuwa ƙasahsen ƙetare, yana lura da sassa daban-daban kuma ya dawo kan turbar nasara da samun riba mai yawa bayan shekaru da ya kwashe na faɗuwa.











