Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake muzguna wa direbobi don bayar da cin hanci a Najeriya
A Najeriya, direbobi da 'yan kasuwa da kuma masu motocin sufuri sun koka kan yadda jami'an tsaro da ma'aikatan da kan sa ido a manyan hanyoyin kasar, kan addabe su da karbar na goro ba bisa ka'ida ba.
Inda suke zargin ana tilasta masu kashe makudan kudade a duk rana a kan hanyoyin kasar, don guje wa cin zarafi ko asarar kadarori da ma ta rayuka.
Masu harkokin sufurin a Najeriya sun yi zargi cewa, hanyoyin kasar sun zame masu wani indararo da ke antayar masu da makudan kudade a duk rana.
Hassan Umar Mali, wani direba da ya kwashe shekara fiye da hamsin yana jan motar jigilar kaya a kasar, ya bayyana irin kalubalen da suke fuskanta yau da kullum:
''In mun dauko kaya zamu kai Abuja irinsu yalo da rake da lemu da sauran abubuwa, toh duk shingen da mu ka tarar da masu tsare mana dazuzzaka sai mun bada naira dubu a takaice''
''Idan ba'a bada, fakawa mu ake, a ci mutunci mu wallahi, a ajiye ka komin girman ka ka zo kana magana da yaro karami, ya yi ta gaya ma magana ya ce shi fa kudinsa naira dubu ne, toh jami'ai tsaron rike da bindiga a daji, ya za ka yi?'' in ji shi
Malam Hassan ya ce muddin ka bada kudin za a baka damar wucewa ba tare da an yi la'akari da abin ka dauko a cikin motar ba
Ya ce sukan ware naira dubu 40 ko 50 ko 35 ga wadannan mutane domin su iya wucewa.
Malam Muhammad Shu'aibu, wanda shi ne sakataren kungiyar masu motocin sufuri ta NARTO a yankin Kafancan na jihar Kaduna, ya ce wannan matsala ta karbar na-goro a hanyoyi, ta kai innataha:
''Saboda kowani lungu yanzu direba in ya taho da mota, kawai ana dauka inda ka san kamar ka dauko kayan sata ne''
''Daga yanayin kayan da ka dauko, in ka dauko kayan mai tsada to yanayin cajin da zaa yi maka kennan''
''Ta kai ga in har Shannu mutum ya dauko, sai an kirga yawan shannun, a yiwa kowane sa kudi sannan ka biya, musaman kudin hanya ware shi ake yi daban watau wurin gudanar da binciken ababen hawa saboda in ba bu shi aikin ma ba zai yu ba''
''Akwai mai karamar mota ta J5 da zai tashi kamar nan ya tafi Lagos kudin hanya kawai ba mai zai iya kashe kamar dubu 150 kuma idan ba ka bayar ba za a ci maka mutunci sai su iyaka saka ka kwana daya ko kwana biyu a check point din'' in ji shi
Wadannan korafe-korafe dai wasu matsaloli ne da ke bukatar hukumomin da abin ya shafa, su yi azamar daukar matakan da suka kamata tun kafin lamarin ya kai ga rincabewa.