Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta fasa ɗaukar Alvarez, Liverpool ba zata siyar da Wirtz ba
Barcelona ta fasa siyen ɗan wasan Ajantina da Julian Alvareza watan Janairu, inda yanzu zai jira ya ga ko Paris St-Germain ko Arsenal za su yi zawarcinsa, ko ya yi zamansa. (Fichajes - in Spanish)
Liverpool ta fasa siyar da Florian Wirtiz ga Bayern Munich a watan Janairu inda an buɗe kakar siyar da ƴan wasa, yayin da Munich ke duba yiwuwar ɗaukar nasa a kaka mai zuwa, inda Michael Olise ya ƙi amince wa da sabon tayin da aka yi masa. (Christian Falk - Bayern Insider/Bild)
Ɗan wasan Bournemouth Alex Scott da takwaansa na Crystal Palace Adam Wharton, na daga cikin yan wasan da Chelsea ke son ɗauka, bayan fasa ɗaukar ɗan wasan Monaco Lamine Camara. (CaughtOffside)
Aston Villa na son ɗan wasan Ajantina Emi Buendia, ya ci gaba da zama a ƙungiyar, bayan sun sabaunta masa kwantaraginsa a matsayin tukuici, saboda irin ƙwazon da ya yi. (Mail)
Ɗan wasan Ingila Luke Shaw, zai iya barin Manchester United idan kwantaraginsa, ya ƙare a kakar wasa na gaba. (Teamtalk)
Udinese ta shirya siyen ɗan wasan Austria David Alaba, da ya bar Real madrid a wannan kaka. (Fabrizio Romano)