Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kuɗin da Salah ke nema na sa shakku a komawarsa Saudiya, Munich na son Olise
Farashin da tohon ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah, ya sanyawa kan sa na iya sa komawarsa Saudiya ƙila-wa-qala , inda ƙungiyoyi ke kokawa kan ɓukatun na kudi da ya nema. (Sun)
Bayern Munich ta sanar da Real Madrid da ta manta da ɗaukar ɗan wasan Faransa Michael Olise, saboda ba za su siyar da shi ba a wannan kaka. (Marca)
Ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi, zai iya komawa Barcelona kan euro miliyan 31, kwatankwacin fam miliyan 26. (Bild - in German)
Arsenal da Liverpool na kokawar ɗaukar ɗan wasan RB Leipzig da Netherlands Lutsharel Geertruida, da ke mastyin dan wasan aro a Sunderland. (Caughtoffside)
Manchester City da Tottenham na son siyen dan wasan Portugal Francisco Trincao, 26, kan euro miliyan 50 dai dai da fam miliyan 42.6, da ke son komawa Al-Ahli da ke Saudiya daga Sporting. (Record via Sport Witness)
Barcelona sun fara shirin siyen ɗan wasan Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, bayan kamala gasar cin kofin duniya, kan euro miliyan 130 dai dai da dam miliyan 110. (Sport - in Spanish)
Hull City ta shigar da buƙatar ta na na dan wasan Mjallby da Swedish Elliot Stroud, 24. (Expressen - in Swedish)
Manchester United na duba yiwwuwar ɗaukar ƴan wasan tsakiya biyu, bayan sun kamala, siyen dan wasan Chelsea da Brazil Andrey Santos. (Football Insider)
Ɗan wasan bayan Greece Konstantinos Mavropanos, na ci gaba da ɗaukar hankula daga ƙungiyoyin Firimiya daban-daban da ƙarin wasu a Turai, bayan rawar da dan wasan ya taka a West Ham.(Sky Sports)
Como na fatan siyen ɗan wasan Colombia , sai dai Galatasaray na iya shiga gaban sui da tayin euro miliyan 30 kwatankwacin fam miliyan 25.. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchster United sun shiga kasuwa don siyen mai tsaron raga, da zai iya gogayya da Senne Lammens, da mai tsaron ragar Paraguay Orlando Gil, da aka fahimci sun fara tattuna kan farashin fam miliyan 5.2 daga ƙungiyar San Lorenzo da ke Argentina. (Manchester Evening News)
Fatan Newcastle United na ɗaukar, mai tsaron ragar Ingila James Trafford, daga Manchester City taƙaru, bayan da abokiyar gogayyarta Aston Villa ta mayar da hankali ci gaba da rike mai tsaron ragar ta ɗan wasan Argentina Emiliano Martinez. Haka ma dai Chealse itama na son mai tsaron ragar. (Chronicle)
Sabon mai horar da ƴan wasan Benfica Marco Silva na son ɗauko tsohon ɗan wasan Fulham Joao Palhinha, inda tuni suka ta ya shi kan euro miliyan 25 (Fam miliyan 21.3) daga Bayern Munich biyo baya aronsa da suka baiwa Tottenham a kakar da ta gabata. (Record - in Portuguese)