Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 5 da za ku yi la'akari wajen zaɓen ɗantakara a 2027
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da aka buɗe ƙofar yaƙin neman zaɓe a Najeriya, ƴan siyasa sun fara baza komar su tare da ƙoƙarin jan hankalin masu zaɓe.
Ana yi wa masu zaɓe alƙawura da dama domin neman ƙuri'unsu, ciki har da wasu alkawuran da ake ganin zai yi wuya a iya cika su.
An buɗe yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027a hukumance ranar 19 ga Agusta 2026, gabanin zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairu 2027.
Ƴan takarar sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, inda suka yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana tare da mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi al'umma.
Hakan ya sa ake kira ga masu zaɓe da su duba ƴan takara da alƙiblarsu fiye da jam'iyyunsu ko kuma kallon tawagar da ke halartar tarukan gangaminsu ko taken yaƙin neman zaɓensu.
To wadanne abubuwa ya kamata masu zaɓe su kalla kafin su kaɗa ƙuri'arsu ga wani ɗantakara?
Abin da ɗantakara ya taɓa yi
Masana na ganin idan ya taɓa riƙe wani matsayi na gwamnati ko aka taɓa ba shi damar jagoranci, masu zaɓe na iya komawa baya su binciki yadda ya yi amfani da damar da aka ba shi, irin manufofin da ya aiwatar da kuma irin tasirin da ayyukansa suka yi ga al'ummar da ya jagoranta.
Dakta Babayo Sule, mataimakin farfesa kuma mai bincike kan siyasa da manufofin gwamnati a Jami'ar Namibia, ya ce yana da muhimmanci masu zaɓe su duba nagartar ɗan siyasar da ya taɓa samun damar mulki kafin su sake ba shi wata dama.
Ya ce ya kamata a tambayi ko ɗan takarar ya cika alƙawuran da ya yi a baya, da irin nasarorin da ya samu, da kuma abubuwan da bai iya cimmawa ba.
A cewarsa, idan kuma ɗan takarar sabo ne da bai taɓa riƙe mukamin siyasa ba, masu zaɓe su duba abubuwan da ya aikata a baya waɗanda za su iya nuna kishin ƙasa, ƙwazo da kuma yadda yake kallon buƙatun al'ummar da yake son wakilta.
"Dama shi zaɓe tukuici ne ko kuma horo, wanda ya yi abin kirki a ba shi tukuici, wanda ya saɓa a ba shi horo," in Dakta Babayo.
Ya ce ya kamata masu zaɓe su yi la'akari da irin alƙawuran da ɗan takarar ya yi, sannan su kwatanta su da abubuwan da ya taɓa yi a baya, domin fahimtar ko akwai yiwuwar ya cika sababbin alkawuran da yake yi.
Yanayin da al'umma ke ciki
Masanin ya ce ya kamata masu zaɓe su tambayi kansu ko suna jin daɗin yanayin da suke ciki, tare da duba irin abubuwan da suka fuskanta a cikin shekaru huɗun da suka gabata.
Ya ce ya kamata kowane mutum ya yi la'akari da abin da ya gani da kuma abin da ya ɗanɗana a lokacin wa'adin da ya gabata, kafin ya yanke shawarar wanda zai zaɓa.
Ya ƙara da cewa ya kamata masu zaɓe su tuna cewa wannan na iya zama damar da suke da ita ta ƙarshe kafin su sake samun irin wannan dama bayan wasu shekaru huɗu.
Saboda haka, ya ce ya kamata su yi nazari kan manufofi da alkawuran ƴan takara, su duba waɗanda za su fi amfanar da su da al'umma a shekaru huɗu masu zuwa.
Manufofin ɗantakara
Dakta Babayo ya ce a duk lokacin da ɗan takara ya je yaƙin neman zaɓe, ya kamata masu zaɓe su yi amfani da damar wajen tambayarsa tare da neman cikakken bayani kan manufofinsa da abubuwan da ya shirya yi wa al'umma.
A irin yanayin Najeriya, ya ce ya kamata masu zaɓe su kalli abin da ƴan takara ke shirin yi game da matsalolin tsaro, tattalin arziki, samar da ayyukan yi da sauran ƙalubalen da ke addabar al'umma.
Ya ce bai kamata masu zaɓe su tsaya ga sauraron jawabai ko kallon yawan mutanen da suka halarci gangamin ɗan takara kawai ba, domin hakan ba ya nuna irin abin da zai iya yi idan aka ba shi mulki.
Masanin ya ce idan masu zaɓe suka biye wa ruɗin siyasa a wajen gangami, ba tare da sun tambayi ɗan takara kan manufofinsa da hanyoyin da zai magance matsalolin da ke damun jama'a ba, akwai yiwuwar su yi nadamar zaɓensu bayan an kammala zaɓe.
Banda kallon addini da ƙabila
Amfani da addini ko ƙabilar da ɗantakara ya fito na taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, inda wasu masu zaɓe ke la'akari da asalin ɗantakara wajen yanke shawarar wanda za su mara wa baya.
Sai dai Dakta Babayo Sule ya ce idan masu zaɓe na son samun ɗan takara mai nagarta, bai kamata su mayar da addini ko ƙabilar da ya fito daga cikin abubuwan da za su yi la'akari da su ba.
A cewarsa, bai kamata ɗan siyasa ya nemi ƙuri'ar jama'a ta hanyar amfani da bambancin addini ko ƙabila ba, domin hakan na iya karkatar da hankalin masu zaɓe daga ainihin manufofin da ya kamata su duba.
"Duk wanda ya zo maka da batun addini a takara, to ruɓaɓɓen ɗansiyasa ne," in ji shi.
Ya ce ƴan siyasar da ke amfani da addini ko ƙabilanci wajen neman ƙuri'a na iya yin hakan ne saboda sun kasa gamsar da masu zaɓe da ayyukansu ko manufofinsu.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin irin waɗannan 'yan siyasa, da zarar sun samu nasarar zaɓe, ba sa cika kula da al'ummar da suka yi amfani da addininsu wajen neman goyon bayansu.
A ganinsa, manufofin da ɗan takara ya gabatar wa masu zaɓe da irin shirin da yake da shi na inganta rayuwar jama'a su ne ya kamata su kasance a sahun gaba wajen tantance wanda za a zaɓa.
Kauce wa siyasar kuɗi
A lokutan zaɓe, wasu ƴan takara kan yi amfani da kuɗi wajen jan hankalin masu kaɗa ƙuri'a, musamman a lokacin da ake dab da akwati.
Wasu kuma kan raba kayan abinci, tufafi ko wasu kayayyaki kyauta, domin samun goyon bayan jama'a.
Dakta Babayo Sule ya ce idan masu zaɓe suka yi watsi da kwaɗayin samun kuɗi ko kyaututtuka na ɗan lokaci, za su iya zaɓar ɗan takarar da ya dace da su.
A cewarsa, duk da cewa mai kaɗa ƙuri'a na iya ganin karɓar kuɗi daga ɗan takara ba laifi ba ne, hakan na iya yin illa ga tsarin zaɓe, domin yana ba da damar zaɓar wanda ya fi ƙarfin kuɗi maimakon wanda ya fi cancanta.