Arsenal ta lashe Premier karon farko cikin shekara 22

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta lashe gasar Premier ta bana karon farko cikin shekaru 22, bayan nasarar da ta yi 2-1 kan Crystal Palace a filin wasa na Selhurst Park da ke Lonodn.
Gunners wadda ta yi nasarar kaucewa rikicin lashe kofin a ranar ƙarshe tun a wasan da City ta yi canjaras da Bournemouth a farkon makon nan, sun yi farin cikin cin kofin ba a gida ba amma dai a birnin London ne, tun da yanzu London ta zama jajawur.
Gabriel Jesus ne ya fara jefa kwallo a wasan a minti na 41 abin da ya baiwa Gunners damar shiga gaba a wasan kenan a matsayinta na baƙuwa.
Noni Madueke ne ya ƙara ta biyu mintina uku bayan dawowa hutun rabin lokaci, wani abu ƙara baiwa Arsenal jin kwarin gwiwa da kuma mamaye wasan.
Jean-Philippe Mateta ya farkewa Palace ɗaya a minti na 89, inda suka samu ƙwarin gwiwar za su iya juya akalar wasan sai dai kuma a haka aka tashi.
Cikin tsarin murnar da aka yi magoya bayan Arsenal 1,000 ne suka yi layi damun yi wa tawagar ƙungiyar barka da zuwa, da kuma mamallakanta Stan Kroenke da ɗansa Josh waɗanda suka halarci wajen wasan mai cike da tarihi.
Masoyan ƙungiyar sun yi layi na kusan mil 15 daga arewaci kusa da filin wasa na Emirate, wasu sun fara bin dogon layin ne tun 9 na safe, domin ganin yadda ƙungiyar za ta ɗaga kofin da rabonta da shi tun shekara 20 bayan Arsene Wenger da ya ci a 2004.
Wata rana ce da za a ci gaba da tunawa da ita musammam a wajen Max Dowman. Matashin ɗan wasan da bai je atisaye ba a wannan makon saboda kammala karatunsa - wanda ya zama ɗan wasan da ya fi kowanne ƙarancin shekaru da ya fara Premier. Kuma ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya samu kyatar lashe Premier.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan kakar na ɗaya daga cikin wadda za ta shiga tarihi ga ƙungiyar, wadda ta yi ta zuwa ta biyu sau uku a jere, amma juriya ta kai ta ga nasara a ƙarshe.
Tunanin mafi yawan 'yan wasan ƙungiyar zai sauya ne saboda wannan nasara, kazalika idan sun dawo kaka mai zuwa za su fito da sunan zakarun gasar Premier.
Arsenal ta ƙare kakar da tazarar maki bakwai tsakaninta da City da ta zo ta biyu, wadda ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa gwarzuwar gasar Europa.
A nan gaba Arsenal za ta yi bikinta na nasara a cikin birnin Landan, ta zagaya da kofin magoya bayanta su ftio su tare ta da murna.
Yanzu Arsenal na da wasa mai muhimmanci a gabanta, wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai.
Ta buga wasan tun daga rukuni zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta samu nasara a kanta.
A ranar 30 ga watan Mayun nan za a yi wasan tsakaninta da PSG ta Faransa da ta doke Bayern Munich a wasan kusa da na ƙarshe.










