Yaya kamannin ɗan'adam za su sauya a shekaru masu zuwa?

    • Marubuci, Catherine Heathwood
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Har yanzu mutane ƙara bayyana? Shin sabbin halittunmu na gaba za su kasance dogaye ko gajeru, suka da fasali daban-daban ko za su riƙa kamanni da iyeyensu?

Kamar yadda ci gaba zamani ke haɓaka, haka ma nau'ikan halittun mutane ke sauyawa lokaci zuwa lokaci.

Cutuka da dama da yunwa da mummunan yanayin sun ragu sakamakon magunguna da tsaftar muhalli da kuma watuwar abinci.

Amma Dr Jason Hodgson, ƙwararren masanin asalin ɗan'adam a Jami'ar Anglia Ruskin da ke Birtaniya, ya ce ko kokwanto babu halittar ɗan'adam abu ne da ke ci gaba da bayyana.

''Muna faɗin haka ne saboda wasu ƙwayoyin halittar gadon na yaɗuwa tsakanin al'umomi, sai dai hakan na faruwa ne tsawon ƙarnuƙa, don haka ba wanda zai iya ganin canjin a lokacin rayuwarsa'', kamar yadda ya bayyana.

Bambance-bambancen halitta

Briana Pobiner, ƙwararriya a fannin ilimin sanin ɓurɓushin halittu - da ke aiki a wani gidan tarihin Amurka - ta ce abinci ya taka muhimmiyar rawa a sauyin halittarmu na baya-bayan nan.

"Kusan kashi ɗaya bisa uku na mutanen da ke duniya a yanzu na iya narkar da madara a cikinsu idan suka sha a lokacin da suka manyanta'', in ji ta.

''Amma a shekara 5,000 zuwa 10,000 baya manyan mutane ba su iya narkar da madara idan suka sha, ka ga wannan ya taka muhimmiyar rawa sauya kamannin halittun mutane'', in ji ƙwararriyar.

Hakan ya faru ne bayan da ɗan'adam ya fara kiwon dabbobi masu madara, a lokatun tsananin yunwa, sai wasu da ke iya narkar da madara a cikin suka fara shanta - kasancewar tana cike da maiƙo da sinadaran gina jiki - hakan ya sa suka samu wasu ƙwayoyin halitta a jikinsu, suka kuma riƙa gadar da su ga zuri'arsu har zuwa halittarmu ta yau cikin sauri,'' a cewar Pobiner.

Haka kuma muhallin ɗan'adam na taka muhimmiyar rawa wajen sauyawar kamannin ɗan'adam.

A lokacin da halittunmu suka yi hijira daga Afirka zuwa sassan duniya daban-daban dubban shekaru da suka gabata, sun fuskanci sauyin yanayin wurin zama, don haka halittunsu suka canja.

Alal misali an samu mutane masu hasken fata a muhallin da ke da ƙarancin hasken UV, domin taimakaingwa wajen samar da sinadarin Vitamin D.

An samu bambancin nau'in halittu ''daga mutanen da suka rarrabu da juna,'' a cewar Hodgson.

''A yanzu kuma mun sake haɗewa a siffofi daban-daban - ta hanyar hijira da kuma dunƙulewar duniya wuri guda da sauran hanyoyi''.

Wannan tsari na dunƙulewar dunƙule warduniya na nufin za a iya ganin bambancin siffofin halittun mutane na raguwa

Masu bincike sun ce halittar ƴaƴan da ma'aurata za su haifa na da nasaba da irin halittar iyayensu a wasu lokuta.

''Idan kai namiji da matarsa duka dogaye ne, akwai yiwayuwar ƴaƴansu ma haka,'' kamar yadda suka yi bayani.

"Tsayi da nauyi da tsarin fuska da kowane nau'in abubuwa an nuna suna da alaƙa a wasu rukunin mutane, amma ba koyaushe ba," in ji shi, wanda "a ƙarshe yana tasiri ga yawan ƙwayoyin halitta".

Wasu daga cikin wannan ya faru ne saboda dalilai na zamantakewa da al'adu - misali, mutanen da ke aure a cikin ƙabilarsu. Kuma waɗannan abubuwan na iya canzawa a wasu al'ummomi.

Tasirin tiyatar kwaskwarima

Amma akwai wasu zaɓuka da muke yi da ba sa shafar halittarmu.

Alal mkisali, "idan kana zuwa motsa jiki kuma kana yawan tafiya a ƙafa domin gina tsokoki, hakan ba ya nufin za ka isar da wasu ƙwayoyin halittar manyan tsokokin ga jikokinka ba'', in ji Pobiner.

A yanzu akan yi mafani da hanyoyi da dama, ciki har da likitanci da tsarin kwaskwarima jiki, don canza siffar halaittar ɗan'adam zuwa yadda ake so a zamantakewa maimakon zaɓin yanayi.

A duka faɗin duniya, an yi tiyatar kwaskwarimar jiki miliyan 38 da wasu hanyoyin ƙawata halitta a 2024, kuma hakan ƙarin kashi 40 cikin 100 ne na alkaluman da aka samu a 2020, a cewar ƙungiyar tiyatar kwaskwarimar jiki ta duniya (ISAPS).

Sabbin halittu?

Farfesa masanin bayanan halitta a Jami'ar Aarhus da ke Denmark ya ce yana da wuya a iya hasashen yadda halittar ɗan'adam za ta koma nan da wasu shekaru masu zuwa, ba tare da hakaito yadda muhalli zai sauya ba.

Idan za mu yi magana a kan yadda halittarmu za ta koma nan gaba, to dole yi magana kan muhallinmu.

Shekara miliyan ɗaya da suka gabata

Shekaru miliyan ɗaya da suka wuce, nau'in dan Adam kamar Homo erectus sun wanzu a doron ƙasa.

Namu nau'in halittar ta fara wanzuwa ne a doron ƙasa shekara 300,000 da suka gabata.

"Don haka nan da wasu shekara miliyan ɗayan halittar ɗan'adam za ta suaya zuwa halittun na daban,'' a cewar Mailund.

Ko da a lokacin, an yi gargaɗin, bambance-bambancen da ke tsakanin nau'ikan halittun na iya zama fiye da yadda muke zato.

Akwai kuma yiwuwar nau'in halittunmu zai iya rabuwa zuwa gida biyu, alal misali idan wasu daga cikinmu za su sake muhalli.

"Idan kana rayuwa a duniyar wata, akwai ƙarancin gravity. Dole ka saba da hakan," in ji Mailund.

Don ganin sabon nau'in halitta, waɗannan al'ummomin suna buƙatar ware su gaba ɗaya daga waɗanda ke cikin duniya zuwa zuri'a masu yawa.