Sarmat: Makamin linzamin Rasha mai tafiyar kilomita 35,000

Asalin hoton, Официальный канал Минобороны России
- Marubuci, پاول آکسیونوف
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, تحلیلگر نظامی بخش روسی بیبیسی
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A makon da ya gabata ne Rasha ta bayyana nasarar gwajin sabon makamin linzaminta na Sarmat, da zai iya tafiya daga wata nahiyar zuwa wata.
Babban kwamandan dakarun da ke kula da makaman linzamin ƙasar, Sergei Karakayev ya sanar wa Shugaba Putin matakin cikin wani rahoto da ya gabatar masa, a daidai lokacin da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar da bidiyon gwajin makamin.
Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta daga Ƙasashen Yamma da ta tabbatar da gwajin makamin. Kuma ba san inda makamin ya bi ba.
Wannan shi ne karo na biyu da ƙasar ta yi gwajin sabon babban makamin linzami cikin shekara huɗu, bayan da aka yi gwajin farko a 2022.
Da fari an tsara yin gwajin makamin Sarmat a 2024, daga sansanin Plesetsk, amma sai aka samu akasi na'urorin harba makamin suka lalace.
Daga bayanan da aka bayar game da makamin, Sarmat na ɗaya daga cikin makaman linzami mafiya girma a faɗin duniya, da ka ya yin tafiya daga wata nahiyar zuwa wata.
Cibiyar nazarin barazanar makaman linzami ta Amurka ta ce nauyin makamin Sarmat ya kai tan 10, wanda kuma shi ne mafi girma a cikin makaman linzami.
A lokacin da ak gabatar masa rahoton gwajin makamin, Shugaba Putin ya ce makamin ya ce tazarar makamin ta kai kilomita 35,000.
Shin ana buƙatar irin wannan makami?
Nisan tafiyar da makamin zai yi zai bayar da damar isa wurin da aka tura shi, ta yadda zai zagaya ta duk inda yake so domin kauce wa na'urorin kakkaɓo makamai, don isa inda aka tura shi, ba kuma dole sai ya bi ta gajerun hanyoyi ba.
Hakan zai sa ya zama mai wahalar kakkaɓowa ga na'urorin kakkaɓo makamai, saboda su an tsara su ne kawai ta taƙaitaccen wurin da makamin zai bi.
Girman makamin na bayar da damar saka masa kawuna masu yawa a lokaci, yayin da ake sauya wasu kawunan da wasu makaman masu ɓad-da-bami.
Waɗannan na'urorin masu ɓad-da-bami kan taimaka wa makamin wajen kauce wa kakkaɓowa.
Wani ƙarin abu shi ne makamin zai iya harba makamin supersonic glider.
Gliders, wasu makamai ne masu nauyin gaske da ake ɗaukar su zuwa sama sannan a sake su kan abin da ake so su faɗa a ƙasa.
Sukan taho ta ƙarfin gaske daga sama zuwa ƙasa cikin tsananin gudu, wani abu da ke sa wahalar kakkaɓo su.
Aikin da ya laƙume kuɗaɗe
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙera sabon makami, aiki ne mai cin kuɗi. Kuɗaɗen da aikin ya ci, da aka sirranta, sun ƙaru sosai musamman da yin gwajin.
But Sarmat is said to have only had three tests in total, only one of which has been successful so far.
"A lokacin tsohuwar tarayyar Soviet akan yi gwajin har sau aƙalla 10, ko ma fiye,'' a cewar Pavel Podvig, daraktan shirin makaman nukiliyar Rasha.
Masanin ya ƙara da cewa idan har aka yi gwajin makami irin wannan kuma aka amince a girke shi a rumbun makaman ƙasa, abin da hakan ke nufi shi ne an amince da ingancinsa.
Amma a yanzu an fi yin gwaje-gwajen ta bidiyo, kwamfuta ce ke lissafa yawan gudunsa da nisan da zai iya yi, kuma wannan ya sa an rage yawan gwajin da ake yi, kodayake ba su hana yin gwajin ba.
Sergei Karakayev ya shaida wa Mr. Putin cewa nan da ƙarshen shekarar 2026 za a girke makamin cikin rumbun ajiyar makaman ƙasar, kuma za a iya amfani da shi a kowane lokaci.
Ba a dan haƙiƙanin adadin makaman Sarmat da Rasha ke shirin ƙerawa ba. Amma a cewar Pavel Podvig, amma zai iya zama gommai.
Makamin na amfani da fetur?
Rasha ta fara ƙera sabbin manyan makaman linzami a farkon 2010.
Ɗaya daga cikin dalilan fara wannan aiki shi ne bijirewar da Ukraine ta yi na ci gaba da amfani da makaman linzamin Voivodeship da Rashart ta gadar mata, waɗanda ƙungiyar NATO ke kira 'sheɗanin makami'.
Waɗanan makamai na aiki da sinadarin man fetur da ya ƙunshi fetur ɗin kansa da kuma sinadarin oxidizer, waɗanda idan suka haɗu ke haifar da hayaƙi mai yawa.
Sai a hukumance ba a bayyana cewa Sarmat na amfani da man fetur ba.
Makaman da ke aiki da man fetur ana harba su ne daga wat tasha ta musamman kuma akan saka wa na'urorin harba su mai gabanin a harba makaman.
A cewar Pavel Podvig, aikin ƙera makamin Sarmat an yi shi "saboda siyasa."
"A magana da gaskiya wasu lokutan ƙera irin waɗannan makaman na da dalilai,'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa ba don kariya kawai rasha ke ƙera irin waɗannan makama ba
"Batun a ce da Rasha ba ta ƙera irin waɗannan makaman da tuni an ruguza ta, ba gaskiya ba ne''.










