Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda na yi auren Mutu'a na tsawon shekara biyu'
Yayin da ake ci gaba da musayar yawu dangane da halasci ko rashin halascin auren mutu'a wata wanda ta yi auren mutu'a na tsawon shekara biyu ta shaida wa BBC yadda al'amarin ya faru.
A ƙarshen makon da ya gabata ne dai wani bidiyo na limamin babban masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maƙari ya nuna yadda malamin ke magana kan wata amsar tabbaya da ya ce ya bai wa ɗalibansa da ke harkokin rayuwa a ƙasar waje.
A cikin bidiyon malamin ya ce ya ba su fatawar yin aure na wani lokaci "mu'aqqad" amma "ba Mutu'a" ba duk da cewa a gaba Farfesa ya ce "wasu malaman Sunna sun tafi a kan halascin auren na Mutu'a".
Wannan ne dai ya janyo musayar yawu a tsakanin malamai da ma mabiya, al'amarin da ya ɗumama kafar sada zumunta.
BBC ta tattauna da wata wadda ta yi auren na Mutu'a sannan ta tattaro ra'ayin malaman Sunna da Shi'a kan halasci ko haramcin auren na Mutu'a.
'Na yi auran Mutu'a duk da ni ba ƴar Shi'a ba ce'
Rabi wadda ba sunanta na gaskiya ba ne mai shekara 39 ƴar jihar Katsina ce ta shaida wa BBC dalilinta na yin auren na Mutu'a, bayan rabuwarta da mijinta na farko.
"Soyayya muke da shi, kuma ba ya da ƙarfin da zai auri mace biyu a lokaci ɗaya saboda an masa baiko da ita, tun da ni na taɓa aure sai ya ba mu shawarar yin auren gudun ka da mu afkawa yin zina, tun da idan akwai so dole da sha'awa.
Daga farko auren sati ɗaya muka yi, tun da ba gari ɗaya muke ba, daga baya ya nemi da mu ƙara zuwa shekara biyu," in ji Rabi.
Dangane da batun wurin da Rabi ta samu fatawar da ta ba ta damar yin auren na Mutu'a, ta ce:
"Ni ba ƴar Shi'a ba ce ni, amma na kasance ina da ƙoƙarin neman ilimi da sani daga ɓangarorin addinin Musulunci. Sannan a wajen karance-karance na fahimci an yi zancen auren har a Ƙur'ani, sanan har annabi ya bar duniya ba a haramta ba,
"tsaƙanin sahabbai - wani ya haramta shi, kuma na fahimci sun yi hakan ne saboda idan jahilai suka samu ilimin za su yi amfani da shi sosai su cutar da mata."
Iya malaman Shi'a na tambaya, su ma sun faɗa min ba kowa suke bari yana auren ba sai da hujja mai ƙarfi," in ji Rabi.
'Yadda aka ɗaura mana aure"
Rabi ta ƙara haske dangane da yadda aka ɗaura musu wannan aure.
"Tsakanin ni da shi muka yi siga, abokinsa ne shaidunsa, ni kuma akwai wani ɗana da nike riƙo wanda ya san sirrikana shi na sanar ya zamar min shaida."
Rabi ta kuma yi ƙarin bayani kan da yadda zaman auren nasu ya kasance alhali mijin nata je-ka-da-kwari yake yi zuwa Katsina inda take.
"Auren farko sati ɗaya ne, sai muka ƙara sabunta yarjejeniyar har tsawon shekara 2, ba gari daya muke ba. Lokaci zuwa lokaci muke haɗuwa. Amma ina sanar da kowa ina da aure."
Dangane kuma da zamantakewa, Rabi ta ce " Toh ba yabo ba fallasa, kamar dai yanda ka san zaman mata da miji wanda ba sa rayuwa a gari ɗaya. Amma dai yana ba ni kulawa ta abinci da sutura dai-dai karfinsa, wurin zama ni yake samu inda nike."
Lokacin rabuwa
Kasancewar auren an ƙulla shi ne akan shekaru biyu hakan na nufin a ƙarshen shekarun ma'auratan za su rabu da juna ko kuma su sabunta yarjejeniyar.
To sai dai Rabi ta ce ta nemi mijin ya sawwaƙe mata ne tun kafin ƙarewar wa'adin sakamakon gano cewa akwai cutarwa bayan da ya yi aure.
"Kamar yadda na sanar da kai cewa an yi masa baiko da wata yarinya, to bayan auren sai ya zama hankalinsa ya koma kanta. Sannan kuma ni na rasa mahaifina saboda haka ina cikin yanayin damuwa alhali babu wanda zai lallashe ni.
Saboda haka lokacin rabuwa ma bai ba na ce dan Allah ya yassare min ragowar kwanakin tunda ba saki ake yi ba. Ya so daga baya mu sake ƙulla sabuwar yarjejeniya amma ban yarda ba."
Rabi ta ƙara da cewa duk da musayar yawun da ake yi kan auran Mutu'a hakan bai sa ta ji cewa ta aikata laifi ba.
"Gaskiya ban ji na aikata laifi ba, sai dai na ce na kiyaye kaina daga aikata zina, duk da cewar ba wai dan sha'awa muka yi auren ba, gujewa dai faruwar barna yasa muka yi," in ji Rabi.
"A fahimtar mazhabar Ahlulbait AS auren Mutu'a halal ne har zuwa ranar ƙiyama."
"Abin da aka tafi a kai wanda kuma kamar yadda yake a littafin Sayyidul Murtadha wanda za ku ga bayanan cewa abin da ya tabbata shi ne lokacin manzon Allah SAW ana Mutu'a har zuwa lokacin da ya koma ga Allah."
"Sannan an ci gaba har zuwa lokacin Khalipha Abubakar da ma farkon khalifancin Umar kafin ya haramta," in ji Dakta Shu'aibu Muhammad Abdullahi, shugaban cibiyar nazarin kimiyyar addinin Musulunci ta Khatamul Anbiya Institute of Islamic Sciences da ke Kano
Dakta Shu'aibu ya ce wani dalilin shi ne duk masu cewa an haramta auren Mutu'a ba su kawo ayar da ta goge wadda ta halasta auren ba.
"Duk masu haramtawa sun yarda da cewa aya ta 24 a Suratul Nisa'i ita ce ta halasta auren Mutu'a amma kuma har yau ba su kawo wata ayar da ta soke wannan ɗin ba.
"Ko kuma ana nufin hadisi yana goge aya ne? Shi kansa hadisin bai kai haddin tawatur ba. Bai kai yanayin da malamai suka yarda zai goge aya ba. Ballantana ma akwai hadisan da suka saɓa wa hadisin."
Bugu da ƙari, Dakta Shu'aibu ya ƙara haske kan haramta auren na Mutu'a.
"Sannan idan mutum ya duba ruwayoyin da ake cewa manzon Allah ya hana zai gan su daban-daban masu karo da juna. Wannan su ce an hana ne lokaci kaza, waɗannan ma su ce an hana ne a wani lokaci daban."
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda shi ma wani tsohon bidiyonsa ya rinƙa yawo a kafafen sada zumunta inda yake cewa akwai sahabin da har ya rasu yana halasta auren Mutu'a.
To sai dai a wani saƙon wa'azi da ya wallafa a shafinsa na Facebook mai kama da goge waccan magana da ya yi a baya ya ce auren Mutu'a haramun ne.
"Auren Mut'ah (auren da ake ɗaura shi na wani ƙayyadadden lokaci) mafi yawan malamai na Ahlus-Sunnah sun yi ittifāƙi cewa haramun ne, saboda an halatta shi na ɗan lokaci a farkon Musulunci, sannan Manzon Allah ﷺ ya haramta shi har zuwa Ranar Alƙiyama," kamar yadda Sheikh Daurawa ya wallafa.
Sheikh Daurawa ya lissafa wasu hujjoji da ya ce ya dogara da su:
- Hadisin Sahih Muslim, inda Annabi ﷺ ya ce: "Na taɓa ba ku izinin yin auren mut'ah, amma yanzu Allah Ya haramta shi har zuwa Ranar Alƙiyama."
- Hadisin Ali ibn Abi Talib cewa: "Manzon Allah ﷺ ya hana auren Mut'ah a ranar Khaibar."
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya kuma kawo dalilai guda uku da ya ce su ne suka sa aka haramta auren na ƙayyadajjen lokaci:
- Ya saɓa da manufar aure a Musulunci wadda ta ginu kan zaman dindindin, soyayya, da gina iyali.
- Yana jawo rikice-rikice wajen nasaba, gado, da haƙƙoƙin ma'aurata.
- Ya buɗe ƙofar amfani da mata ta hanyar da ta yi kama da lalata.