Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka yi bikin Ronaldo da amaryarsa Georgina a Portugal
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo ya auri abokiyar zamansa ta shekaru da dama, Georgina Rodríguez, wadda ta yi suna a matsayin abin koyi da kuma mai tasiri a shafukan sada zumunta, a wani bikin auren kotu da aka gudanar a Portugal.
Tauraron ɗan wasan na Portugal ya sanar da labarin ne ta shafinsa na Instagram, inda ya wallafa hoton hannaye biyu sanye da zobban aure, waɗanda ake kyautata zaton nasa ne da na amaryar tasa.
Kafofin yaɗa labarai na Portugal sun bayyana bikin a matsayin "auren da ya fi kowanne a shekarar nan", inda suka ce ma'auratan sun ɗaura aurensu ne a ranar 11 ga Agusta a garin Cascais da ke bakin teku kusa da Lisbon. Rahotanni sun ce 'ya'yansu biyar sun halarci bikin.
Sakon da Ronaldo ya wallafa a Instagram ya samu fiye da miliyan uku na so cikin mintuna 30 kacal.
Ronaldo da Rodríguez sun shafe shekaru goma tare. Sun haɗu ne a wani shagon Gucci a Madrid, inda Rodríguez ke aiki a lokacin da Ronaldo ke taka leda a kulob ɗin Real Madrid na Spain.
Ma'auratan sun sanar da ɗaurin aurensu a ranar 11 ga Agustan bara. A lokacin, Rodríguez ta wallafa hoton wani babban zoben lu'u-lu'u tare da rubutawa da harshen Sifaniyanci cewa: "Na amince. A wannan rayuwar da duk wata rayuwata."
Ronaldo yana da yara biyar inda biyu daga cikinsu na Rodríguez ne. Ita ma ta taka muhimmiyar rawa wajen renon sauran 'ya'yansa uku. A yanzu iyalan na zaune ne a birnin Riyadh na Saudiyya.
'Yarsu ta farko tare, Alana Martina, an haife ta ne a shekarar 2017. Ƙaramar 'yarsu Bella kuwa an haife ta a watan Afrilun 2022, tare da ɗan'uwan tagwaitakarta wanda ya rasu bayan haihuwa.
Wace ce Georgina Rodríguez?
Tun bayan rabuwar Cristiano Ronaldo da tsohuwar budurwarsa, Irina Shayk, Georgina Rodríguez ta zama abokiyar rayuwarsa, lamarin da ya ja hankalin duniya.
Ronaldo ya taɓa bayyana a wata hira da Piers Morgan cewa yana matuƙar son Georgina kuma yana son su yi rayuwa tare har ƙarshen rayuwarsu.
A wani bikin ranar haihuwarta, ya haskaka wasu manyan gine-gine a Dubai da hotunanta domin nuna irin ƙaunar da yake mata.
Kafin Georgina, Ronaldo ya shafe shekara biyar yana soyayya da fitacciyar kwararriyar mai tallan kayan sawa ta Rasha, Irina Shayk.
Lokacin da aka sanar da rabuwarsu a 2015, 'yar'uwar Ronaldo, Elma, ta ce "Komai ƙaddara ne daga Allah."
Mutane da dama sun fassara wannan a matsayin cewa babu yiwuwar su sake komawa tare.
Ana kuma cewa Ronaldo ba ya da halin komawa ga macen da ya taɓa rabuwa da ita.
Haka kuma an ce baya son zama da macen da ba ta girmama mahaifiyarsa.
Nasarorin Ronaldo
Ronaldo ya taka leda a wasu daga cikin manyan kulob ɗin duniya, ciki har da Sporting Lisbon, Manchester United, Real Madrid, Juventus da Al Nassr. Ya zura kusan kwallaye 1,000 a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Kyaftin ɗin tawagar Portugal yana ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan da suka fi samun nasara a tarihin ƙwallon ƙafa. Ya lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar, yayin da Lionel Messi na Argentina ne kawai ya fi shi da nasarori takwas.
Kulob din Al Nassr ya sanar a bara cewa Ronaldo ya sabunta kwantaraginsa na tsawon shekaru biyu, wanda zai ci gaba da tsare shi a kulob din na Saudiyya har zuwa shekarar 2027.
A cewar Bloomberg Billionaires Index, an kiyasta darajar dukiyar Ronaldo a bara zuwa dala biliyan 1.4 (£1.04bn), lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya kai matsayin attajirin biloniya.