Dalilan da suka sa Atiku Abubakar ya yi zargin yin cushe a kasafin 2026

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam'iyyar ADC a Najeriya Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa a kasafin kuɗin ƙasar na 2026, an yi wani cushen da ya zarta naira tiriliyan 12 da har kawo yanzu ba a san ko na mene ne ba.
Atiku Abubakar, ya kuma bayyana cewa an jibge kasafin ne a ma'aikatun gwamnatin tarayya goma kacal tare da watsar da sauran ma'aikatu.
Kazalika Atikun, ya ƙara zargin cewa akwai wani gini na ɓoyayyen tsarin kashe kuɗi ba tare da cikakken bayani ba a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
AbdulRashid Uba Sharada, shi ne mai magana da yawun Atiku Abubakar, ya shaida wa BBC cewa, ba za su taɓa yin irin wannan zargi ba sai sun tabbatar da cewa suna da hujjoji.
Ya ce,"Tun da farko ita wannan gwamnati ta Tinubu dama tana da matsala wajen kasafin kuɗi, sannan ga yawancin ma'aikatun gwamnati duk sun durƙushe b asa aiki yadda ya kamata saboda rashin ware musu kasonsu a kasafin kuɗin ƙasa."
"Yanzu a cikin kasafin kuɗin 2026, an cusa wasu maƙudan kuɗaɗe da ba a yi bayanin na mene ne ba, don haka yakamata gwamnatin Tinubu ta fito ta yi bayanin wa za a biya kuɗi irin wannan?, kuma mene ne aikin wanda za a biya kuɗi irin wannan?."In ji shi.
Mai magana da yawun Atikun, ya ce, "Duk da wannan zargi da muka yi, har yanzu gwamnatin Tinubu ba ta fito ta ƙaryata ba,don yanzu ya kamata majalisun dokokin ƙasa sus ani cewa al'ummar Najeriya suke waklita, don haka su zauna su tabbata da cewa na yi ƙwaƙƙwaran bincike a game da waɗanan maƙudan kuɗaɗe fiye da naira tiliyan 12 da aka yi cushensu a kasafin kuɗin 2026."
To sai dai kuma a cewar Bala Ibrahim, daraktan watsa labarai na jam'iyyar APC, wannan zargi ne maras tushe da makancewa akan adawa ya haifar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa,tafiyar da gwamnati abu nem ai wuyar gaske, sannan kuma harka ce da ake yinta tare da ƴan adawa.
Ya ce," Suka abu ne da a kullum ake yinta, sannan ba bu wani ɓoye-ɓoye akan yadda ake sarrafa dukiyar jama'a, don haka wannan zargi abu ne da ƴan adawa suka saba yi, kuma hakan ba zai hana gwamnati sauke nauyin da ya rataya a kanta ba."
A Najeriya dai an jima ana zargin aikata ba daidai ba dangane da abin da ya shafi kasafin kuɗi kama daga zargin yin cushe da aikata wasu abubuwa na rashin gaskiya. Abin da gwamnatin shugaba Tinubu ta sha nanata cewa ba ta aikata wani mai kama da haka ba.
A watan Disambar 2025, ne shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ya gabatar da naira tiriliyan 58.47.
A kasafin, Tinubu ya tsara kashe naira tiriliyan 15.25 domin gudanar ayyukan yau da kullum na gwamnati, sannan ya ware naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da manyan ayyuka da more rayuwa a ƙasar.
Tinubu ya tsara kasafin ne a bisa hasashen farahin gangar ɗanyen man fetur a kan dala 64.85.
Haka an yi hasashen sama da gangar ɗanyen man fetur miliyan 1.84 a kullum, sannan ya ayyana canjin dala a kan naira 1,400.
Ma'aikatun da suka fi samun kasafi su ne:
Tsaro: Naira tiriliyan 5.41
Aikace-aikace: Naira tiriliyan 3.56
Ilimi: Naira tiriliyan 3.52
Lafiya: Naira tiriliyan 2.48












