Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana zargin an fesa wa masu haƙar ma'adinai wani abu kafin mutuwarsu- Bago
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya shaida wa BBC abin da ya faru a ƙarshen rayuwar wasu daga cikin mutum 37 da ake zargin masu haƙar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun hukumar tsaron farin kala ta Najeriya (NSCDC).
Gwamnan ya ce wasu daga cikin waɗanda suka tsira sun bayyana cewa an fesa wa mutanen da ake tsare da su wani abu da ba a gano ko mene ne ba kafin mutuwarsu a tsare.
"Wani wanda ya tsira kuma yake a wurin DSS ya ce wani mutum ya zo ɗakinsu inda aka tsare da su, ya fesa musu wani abu kamar turare, sai mutane suka fara tari da kuma shaƙewa," in ji shi.
Gwamna Bago ya shaida wa BBC cewa: "Wasu daga cikin mutanen da suka tsira sun ce an fesa musu wani abu kamar barkono. Wataƙila an yi amfani da hayaki mai sa hawaye ko wani abu makamancin haka... Wani mutum ya zo da wani abu kamar kwalbar turare ya fesa musu, sai mutane suka fara tari da kuma shaƙa."
Ya ce wasu kuma sun bayyana cewa numfashinsu sai da ya fara ɗaukewa saboda ƙarancin iska a ɗakin da aka tsare su.
BBC ba ta iya tabbatar da waɗannan bayanai da kanta ba.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin gano ainihin abin da ya faru. Ya kuma ce bai san da kama masu haƙar ma'adanan ba, ko kuma yanayin da aka tsare su a ciki ba.
Bai kamata a ɗaura mana laifi ba - Bago
Mista Bago ya ce bai kamata a ɗora wa gwamnatin jihar alhakin mutuwar mutanen ba, saboda NSCDC hukuma ce ta gwamnatin tarayya kuma ba gwamnatin jihar ce ke kula da ita ba.
Gwamnan jihar Neja ya bayyana cewa ya ga gawarwakin masu haƙar ma'adanai da suka kumbura, yayin da wasu kuma fatar jikinsu ke barewa, bayan labarin mutuwarsu ya fito.
A hirar da BBC, gwamnan ya ce bai san da kamen mutanen ba, sai bayan samun labarin mutuwarsu a wurin da ake tsare da su, inda ya garzaya wurin.
"Mutum 37 ne suka mutu. Da muka isa wurin, muka tabbatar da cewa sun mutu. Wasu daga cikin waɗanda muka gani fatarsu tana ɓarewa, wasu sun kumbura, wasu kuma kumfa tana fita daga bakinsu, yayin da wasu ke zubar da jini ta hancinsu da bakinsu. Wannan ya tayar da hankali.
"Saboda haka sai muka nemi taimakon likitoci. Aka kai gawarwakin ɗakin ajiye gawa na babban asibitin jihar, wanda na ba da izinin kai su. Daga nan aka yi gwajin gawarwaki kan wasu daga cikinsu, sannan tawagar likitoci ta ɗauki samfurori domin gano abin da ya haddasa mutuwar."
NSCDC ta kama mutanen da ake zargi da haƙar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a wani samame da ta kira "burst operation" a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026.
Sai dai washegari, 17 ga Satumba, hukumomin sun amince cewa da dama daga cikin mutanen da aka kama sun mutu a tsare.
Yayin da ake ci gaba da binciken musabbabin mutuwar, NSCDC ta danganta mutuwar da yiwuwar ɓarkewar wata cuta a lokacin da suke tsaren.
Sai dai Gwamna Bago ya ce bai san cewa NSCDC na kama mutane a jihar ba, kuma sai bayan ya ji labarin mutuwar ne ya ɗauki mataki ya kai gawarwakin asibiti.
Ya ce: "NSCDC ba ta buƙatar izinin gwamna domin kama mutane, musamman idan lamarin yana cikin hurumin aikinta.
"Haƙar ma'adinai da kuma yaƙi da haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba na daga cikin ayyukan NSCDC."
Jami'an NSCDC 20 da aka dakatar
Ma'aikatar Cikin Gida ta Najeriya ta sanar da dakatar da jami'ai 20 na hukumar bisa abin da ya faru a ranar Alhamis.
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana sunayensu a cikin wata sanarwa, inda ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka kan lamarin.
Ya kuma ce an dakatar da Kwamandan NSCDC na jihar Neja.
Jami'an da aka dakatar su ne:
- SC Usman Isah Ndamaka
- ASCI Hassan Mohammed
- CCA Bala Mohammed
- CSC Oluwadare Sunday
- DCC Obafemi Elvis
- CSC Annas Shitto Lamino
- DCC Philip Ajayi
- ACC Barr. Stephen Tsado
- ASCI Alhassan Mohammed
- IC Abdullahi Sale
- IC Mohammed Sonfada
- CAI Liman Abubakar
- CAI Bala Usman
- IC Mohammed Jiya
- DSC Isah Suleiman
- CAI Ahmed Wushishi
- IC Sale Adamu
- IC Haruna Mohammed
- ASCI Aliyu Sallah
- CAI Isah Sanusi
Matakan gwamnatin tarayya kan mutuwar mutanen
A halin da ake ciki, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bai wa wani kwamitin mutum 10 mai zaman kansa mako biyu domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da miƙa rahotonsa ga Ma'aikatar Cikin Gida.
A cewar sanarwar ma'aikatar, matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da kuma wanda ba za a yi masa katsalandan ba kan abin da ya faru ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa kwamitin mutum 10 mai zaman kansa domin binciken rahoton mutuwar mutane 37 da ke hannun rundunar NSCDC ta jihar Neja bisa zargin haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
Aikin kwamitin shi ne gano waɗanda suka mutu, da kuma binciken yadda aka kama su, yadda aka tsare su da kuma abin da ya haddasa mutuwarsu.
Kwamitin zai kuma binciki waɗanda ke da alhakin abin da ya faru, da gano ko an samu sakaci ko rashin ɗa'a, sannan ya bayar da shawarwari kan matakan da ya kamata a ɗauka kan waɗanda aka samu da hannu.
Haka kuma, kwamitin zai ba da shawarar yiwuwar biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa, da kuma matakan da za a ɗauka domin hana sake faruwar irin wannan lamari.
Ministan ya kuma umurci shugabannin NSCDC da su ba kwamitin cikakken haɗin kai wajen gudanar da binciken.
Membobin kwamitin
- Mista Jonathan Kure, mni, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS — Shugaban kwamitin
- Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN), tsohon Darakta-Janar na Makarantar Koyon Shari'a ta Najeriya — Sakatare
- AIG Hosea Hassan Karma (mai ritaya)
- Farfesa Olayinka Buhari, Farfesa a fannin Histopathology kuma tsohon Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ilorin
- Wakilin Majalisar Masarautar Minna
- Wakilin gwamnatin jihar Neja
- Alhaji Liman Sulaiman, Sakataren Ƙasa na Ƙungiyar Masu Haƙar Ma'adanai ta Najeriya
- Mista Deji Adeyanju, lauya kuma mai rajin kare haƙƙin bil'adama
- Madam Zainab Suleiman Okino ta jaridar Blueprint
- Dokta George Agbakahi, mai sharhi kan harkokin jama'a.