Me ya sa wasu yaran ba su kai saura fahimta ba a makaranta?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Raliya Zubairu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Sau da yawa ko a cikin yaranmu mukan fahimci cewa wasu sun fi saura ƙarancin gane karatu, iya rubutu ko fahimtar abin da ake koya musu.
Hakan na faruwa duk kuwa da cewa suna samun koyarwa iri ɗaya da ta saura.
Wasu iyayen kan shiga damuwa ko ɗimuwa kan yadda irin hakan ke faruwa, har ya kasance suna nuna ƙosawa kan irin waɗannan yara.
Sai dai a wani lokacin ba laifin iyayen, malamai ko kuma yaran ba ne, wani abu ne da yake da alaƙa da halitta, inda yara kan kasance suna da lalurar da a turance ake kira Dyslexia.
Sau da yawa iyaye da kuma malamai ba su fahimtar irin waɗannan yara da kuma lalurar da suke fama da ita.
Mece ce Dyslexia?
Dyslexia wata lalura ce ta koyo da ke da alaƙa da yadda ƙwaƙwalwa ke bunƙasa, wadda ke shafar iya karatu da rubutun yara da kuma a wasu lokutan manya.
Wannan matsala kan sa ya fi wuya ga ƙwaƙwalwa ta haɗa haruffa da sautukan da suka dace da su.
Dakta Mimi Osamwonyi ƙwararriyar likitar ƙwaƙwalwa a birnin Abuja da ke Najeriya ta ce: ''Idan aka ce mutum na da dyslexia, hakan na nufin yana da matsala wajen danganta haruffan da yake gani da sautukan da ya kamata su bayar, lamarin da ke sa karatu da rubutu su zama ƙalubale gare shi''.
''Misali, idan mutum wanda ba ya da dyslexia ya ga kalmar "cat" (wato mage), nan take ƙwaƙwalwarsa za ta haɗa haruffan C-A-T da sautukan da suke wakilta, sannan ya gane ma'anar kalmar''.
''Sai dai wannan ba abu ne mai sauƙi ba ga mai fama da dyslexia. Mai irin wannan lalura zai iya daukar tsawon lokaci da ƙoƙari kafin ya iya haɗa haruffan da sautukansu domin gane kalmar''.
Yadda za a gane mai lalaurar dyslexia
Masana lafiya sun ce Dyslexia galibi tana fara bayyana ne tun lokacin ƙuruciya, amma tana iya ci gaba har zuwa girma. Wato mutum na iya fuskantar ta tun daga lokacin makaranta har zuwa lokacin da ya zama babba.
Sai dai abin da ake gani shi ne, idan an ba yaro taimako da hanyoyin koyarwa da suka dace tun da wuri, zuwa lokacin da ya girma alamomin matsalar na iya raguwa sosai ko kuma su daina fitowa fili.
Saboda haka, lokacin da mutum ya girma, mai yiwuwa ba a iya gane cikin sauƙi cewa yana da dyslexia, duk da cewa matsalar tana nan.
Dakta Osamwonyi ta bayyana alamomin lalurar kamar haka:
- Wahalar karatu
- Yawan kuskure wajen rubuta kalmomi
- Rashin iya rubutu yadda ya kamata
Ko dyslexia na nufin ƙarancin basira?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Osamwonyi ta ce yana da muhimmanci a fahimta cewa dyslexia ba matsala ce da ke da alaƙa da ƙarancin basira ba.
''Mutanen da ke da dyslexia na iya kasancewa masu cikakkiyar basira kamar kowa, amma suna fuskantar ƙalubale ne wajen sarrafa kalmomi da haɗa haruffa da sautukan da suke wakilta yayin karatu da rubutu''
''Abu mafi muhimmanci shi ne a fahimci cewa dyslexia ba tana nufin yaro ba zai iya koyo ba ne. Maimakon haka, tana nufin yaron na iya buƙatar wata hanya ta daban wajen koyo da fahimtar darussa''
''Dukkan waɗannan matsalolin na iya bayyana ko da yaron yana da basira kuma yana samun koyarwar da ta dace''
''Ga manya kuwa, lamarin na iya ɗan bambanta. Bayan wani lokaci, galibi sukan koyi yadda za su daidaita kansu da matsalar, musamman idan sun samu taimako da hanyoyin koyarwa da suka dace tun da wuri''.
''Duk da haka, suna iya ci gaba da fuskantar ƙalubale wajen yin karatu, da kuma yin rubutu cikin sauri''
''Sai dai waɗannan ƙalubalen ba sa nuna cewa mutum ba shi da basira, illa dai yadda ƙwaƙwalwarsa ke sarrafa haruffa da kalmomi ne ya bambanta da na sauran mutane''.
End of Wasu ƙarin labaran da za ku so karantawa:
Mene ne adadin yara masu dyslexia a Najeriya?
An yi kiyasin cewa kusan kashi bakwai cikin ɗari na ɗaliban makarantun firamare na fama da dyslexia a duniya baki ɗaya. Wannan na nufin kusan yaro ɗaya cikin kowane yara 14 na fama da wannan lalura.
Dr Naja'atu Hamza ƙwararriyar likitar ƙwaƙwalwa ce a babban birnin Najeriya, Abuja, ta ce: ''Dyslexia na shafar kusan kashi 20 cikin ɗari na al'ummar duniya. Duk da haka, ana ganin wannan adadi ma bai kai ainihin yawan masu fama da ita ba, domin mutane da yawa masu dyslexia kan kasance ba a gano matsalarsu ba, ana ɗaukar su a matsayin malalata ko waɗanda ba sa son su mayar da hankali wajen karatu''.
''A Birtaniya kuwa, an yi kiyasin cewa mutum ɗaya cikin kowane mutum 10 na rayuwa da dyslexia''.
Wannan ya nuna cewa matsalar ta zama ruwan dare fiye da yadda mutane da dama ke zato, duk da cewa har yanzu ana yawan rashin fahimtar ta a sassa daban-daban na duniya.
A Najeriya, an gudanar da wasu bincike-bincike a wurare dabam-dabam, amma har yanzu ba a samu cikakken bayanin da zai nuna yawan masu fama da matsalar a faɗin ƙasar baki ɗaya ba.
Har yanzu ba a cika gano masu fama da dyslexia a Najeriya ba, kuma akwai kyamar da ake yi wa masu wannan lalura. Ana hasashen cewa tsakanin kashi 10 zuwa 20 cikin ɗari na al'ummar ƙasar na iya kasancewa suna da ita, amma har yanzu ba a amince da ita a hukumance a matsayin lalurar koyo a manufofin ilimi na ƙasa ba.
Yawancin yara da ke nuna alamun matsalar karatu da rubuta kalmomi ana yi masu kallo a matsayin waɗanda suka ƙi mayar da hankali a karatu , ko masu taurin kai ko marasa basira daga malamai da iyaye, maimakon a gano cewa suna da wata matsala da ta shafi yadda ƙwaƙwalwarsu ke sarrafa harshe tare da ba su taimakon da ya dace.
Shin ko ana gadon Dylexia?
Bincike ya nuna cewa dyslexia na da alaƙa da gado kuma sau da yawa tana bayyana a cikin iyalai. Idan ɗaya daga cikin iyaye ko kuma ɗan'uwa ko ƴar'uwa na da dyslexia, akwai yiwuwar tsakanin kashi 40 zuwa 50 cikin ɗari cewa sauran ƴan'uwa ma za su fuskanci irin wannan ƙalubalen karatu.
Sai dai kasancewar mutum ya fito daga iyalin da ake da masu dyslexia ba yana nufin lallai zai kamu da ita ba, domin yadda matsalar ke bayyana na iya bambanta daga mutum zuwa mutum.
''A wasu lokuta, dyslexia na iya kasancewa abin da ake gada a cikin dangi, duk da cewa yadda alamominta ke bayyana kan bambanta daga mutum zuwa mutum, har ma a tsakanin ƴan gida ɗaya'' in ji Dakta Hamza.
Ko ana magance lalurar?
Masu fama da lalurar dyslexia ba za su iya warkewa gaba ɗaya ba, domin ba cuta ko rashin lafiya ba ce, illa wata matsala ce da ta shafi yadda ƙwaƙwalwa ke sarrafa harshe tun daga lokacin bunƙasarta.
Sai dai, masu fama da dyslexia na iya inganta ƙwarewarsu ta karatu, rubutu da haruffanta kalmomi sosai idan suka samu tallafin da ya dace da kuma hanyoyin koyarwa na musamman in ji Dakta Hamza.
''A likitance, ba za a iya warkar da dyslexia gaba ɗaya ba ta yadda matsalar da ke da alaƙa da bunƙasar ƙwaƙwalwa za ta shuɗe ɗungurungum. Sai dai ana iya sarrafa ta cikin nasara sosai ta hanyar hanyoyin da suka dace''.
''Saboda haka, yaro mai dyslexia na iya koyon karatu da rubutu yadda ya kamata. Abin da yake buƙata shi ne kulawa ta musamman, tallafin da ya dace da kuma koyarwa da ta dace da buƙatunsa''.
''Idan aka ba shi wannan taimako tun da wuri, zai iya koyon karatu da rubutu cikin inganci tare da samun nasara a rayuwarsa kamar sauran mutane''.











