Aston Villa na zawarcin Endrick, Liverpool na son ɗaukar Bernal

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na Brazil mai shekara 20, Endrick, a matsayin aro daga Real Madrid a watan Janairu. (Football Insider)
Ana ta rade-radin cewa tsohon kocin Jamus Julian Nagelsmann zai iya komawa RB Leipzig, amma shugaban sashen ƙwallon ƙafa na Red Bull, Roger Schmidt, ya musanta hakan tare da nuna goyon bayansa ga kocin ƙungiyar na yanzu, Martin Demichelis. (Sky Sports Germany)
Liverpool na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Barcelona da Spain mai shekara 19, Marc Bernal. (Fichajes)
Arsenal da Aston Villa da Newcastle United na zawarcin ɗan wasan gaba na Norway, Antonio Nusa, wanda RB Leipzig ta sanya wa farashin fam miliyan 60. (Ekrem Konur)
Ɗan wasan gaba na Ingila mai shekara 29, Dominic Solanke, ba shi da shirin barin Tottenham, duk da cewa ƙungiyar na shirin ƙara ƙarfin ɓangaren ƴan wasanta na gabaa watan Janairu. (Football Insider)
Aston Villa ta ware kuɗin da za ta iya amfani da su wajen miƙa tayin fam miliyan 18 domin sayen Kevin Viveros, ɗan wasan gaba na Athletico Paranaense kuma ɗan ƙasar Colombia mai shekara 26. (RTI Esporte)
Everton ce ke da matuƙar sha'awar sayen Esteban Lepaul, ɗan wasan gaba na Rennes, duk da cewa Aston Villa, da Brentford, da Brighton da Leeds United suma suna sa ido kan ɗan wasan na Faransa mai shekara 26. (Teamtalk)
























