An ɓata min suna kan zargin rashawa - Diezani

.
Bayanan hoto, Diezani Alison-Madueke ce mace ta farko shugabar kungiyar kasashe masu fitar da danyen man fetur ta duniya
    • Marubuci, Steve Swann
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Society reporter
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tsohuwar ministar man fetur da aka wanke daga zargin karbar rashawa ta ce gwamnatin Birtaniya ta bata mata suna yayin shari’ar wadda ta bayyana a matsayin “mai wahala kuma mai tayar da hankali”.

Diezani Alison-Madueke ta ce ya kamata a ce an bi wata hanyar a maimakon shekara 13 da aka kwashe Hukumar Binciken Manyan Laifuka (NCA) ta kasar ta kwashe tana bincike kan lamarin.

A tattaunawar da ta yi da BBC, Diezani ta ce: “An haramta mini yin tafiya, an haramta mini yin aiki. Sun zubar min da mutunci da kimata.”

A ranar Laraba ne wata kotu a Birtaniya ta wanke tsohuwar ministar man fetur din ta Najeriya daga zarge-zarge biyar, wadanda suka hada da karbar rashawa da kuma hada baki wajen yin almundahana, a wata shari’a da aka faro ta tun watan Janairu.

Alison-Madueke, mai shekara 65 a duniya, ta kasance ministar man fetur ta Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, kuma ita ce mace ta farko shugabar kungiyar kasashen duniya masu fitar da man fetur, Opec.

”A lokacin da aka kwace maka ‘yancinka, wannan na yin illa a gare ka can cikin tunani da zuciyarka,” in ji ta.

”Na san cewa ban taba yin wani mummunan abu ba, ban taba aikata wani mugun abu ba da ale zargi na da shi.”

Tun a shekarar 2015 ne aka fara kama Diezani amma ba a gurfanar da ita a a kotu ba sai a shekarar 2023, bisa zargin karbar cin hanci daga manyan masu sana’ar mai, da kuma karbar kudi daga ‘yan kwangilar gwamnati, lamarin da ya sa ta rika yin “rayuwa ta alfarma”.

Cin hancin da ake zargin ta da karba sun hada da na kaya, wadanda darajarsu ta kai dala miliyan 2.65 daga kantin kayan alfarma na Harrods, da daukar ta a motocin alfarma da kuma zama a gidajen da kudinsu ya kai na miliyoyin fama-famai a biranen London da Buckinghamshire.

'Kowane bangare na da nasa laifin'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma tun daga farkon shari’ar a watan Janairu, masu kare Diezani sun nuna tababa kan adalcin kotu, inda suka yi zargin cewa wasu takardu da ke dauke da shaidun cewa Madueke ba ta da laifi sun bata a Najeriya.

Ta ce a cikin irin wadannan shaidu akwai akwatunan da ke kunshe da takardun rasidai na kudaden da aka mayar wa ‘yan kwangila bayan sun biya wasu kudade a madadinta.

”Hukumomin tattara bayanan sirri ne suka sace akwatunan’ daga gidanta na Abuja a shekara 2015, in ji ta, ta kara da cewa ba ta san ya aka yi da akwatunan ba.

Tsohon shugaban Nakeriya, Goodlick Jonathan, wanda shi ne ya nada Diezani a mukamin minista ya rubuta wa kotu wasika, inda ya ce a wasu lokutan wasu kamfanoni na biyan kudaden zirga-zirga da na wurin zaman ministoci lokacin da suka je yin wasu ayyuka a kasashen ketare.

Lokacin da aka tambayi Diezani kan ko wane ne ke da laifi game da tuhume-tuhumen da aka yi mata a kotu, sai ta ce “kowa na da masa laifin.”

“Ya kamata gwamnatin Najeriya ta rika yin kyakkyawar lura kan matakan da take bi da kuma tsare-tsaren da take bi wajen tunkarar irin wadannan shari’u.

BBC ta nemi martani daga gwamnatin Najeriya.

A nata bangaren, Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Birtaniya (NCA) ta ce: “Akwai sarkakiya sosai a dik lokacin da shari’a ta hada da wasu kasashe, musamman idan akwai siyasa a ciki.”

'

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya ce kasar da ta fi kowace fitar da man fetur a Afirka

Ta yi amannar cewa hukumar NCA ta tuhume ta ne saboda ta ga cewa “ita ce karkatacciyar kuka”, ba tare da kallon irin aikin da ta yi na kawar da rashawa a bangaren man fetur ba, lamarin da ya sa ta tara makiya a Najeriya, kasar da ta fi kowacce fitar da danyen man fetur a nahiyar Afirka.

”Ni ce mace ta farko da ta rike irin wannan mukami ta ministar man fetur kuma na shugabanci kungiyar Opec, daga kasa wadda ale nuna wa mata kiyayya,” in ki Diezani.

Ya ci a ce hukumar NCA “ta yi waiwaye tare da yin duba na tsanaki gane da hujjojin da ke kasa tun da farko,” in ji ta.

Wani mai magana da yawun hukumar NCA ya shaida wa BBC cewa hukumar ta gudanar da “dogon bincike mai zurfi da sarkakiya, wanda kuma aka rika nazari a kansa lokaci zuwa lokaci a tsawon shari’ar”.

Mai magana da yawun hukumar ya kara da cewa NCA “ta yi aiki tare da wasu hukumomi irin ta a kasashen waje, kamar yadda takan yi a duk sauran ayyukanta, an yi wannan bincike ba tare da nuna son kai ba”.

“An gabatar da takardu kunshe da shaidu ga hukumar CPS wadda ita ce ta bayar da umarnin shigar da karar tare kuma da martaba duk wani hukunci da masu yanke hukunci suka zartar.”

Haka nan an wanke yayan Diezani, wato Doye Agamas mai shekara 69, wanda babban malamin coci ne a birnin Manchester, inda aka wanke shi daga zargin hada baki wajen yin rashawa.

Ita ma wata shugaban kamfanin man fetur Olatimbo Ayinde mai shakara 54, ba a same ta da laifin cin hanci ba, ko kuma bayar da cin hanci ga jami’in wata kasa ba.

An tuhume ta a kotu duk kuwa da cewa ta taba zama mai kwarmata bayanai a wata shari’a kan rashawa da hukumomi Najeriya suka assasa.

A shekarar 2023, ma’iakatar shari’a ta Amurka ta kwace kadarori da suka kai darajar dala mikiyan 53 daga manyan masu hada-hadar man fetur da ke cikin wannan shari’a.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar ya fitar a wancan lokacin, ta ce “Alison-Madueke ta yi amfani da mukaminta wajen bai wa mutanen kwagilolin man fetur mai tsoka”.

A game da wannan, Diezani ta shaida wa BBC cewa: Ba a ba ni damar kalubalantar wannan ba saboda ba a gurfanar da ni a kotu kan shi ba, sannan kuma ta ce “an bayar da kwangilolin ne bisa doka da ka’ida.”

Hukumar yaki da rashawa ta Najeriya EFCC, ita ma ta ce ta kwato kudi da suka kai kudi sama da dala miliyan 153 da kadarori sama da 80 daga ‘yar siyasar a shekarar 2022.

Lokacin da aka yi mata tambaya game da haka, sai ta ce: “Kadarorin da aka kwace ba an karbe su ba ne kai-tsaye daga gare ni…Ban san abin da ya faru ba game da wannan. Yanzu ne zan samu ‘yancin sanin mece ce gaskiyar abin da ya faru a can.”