Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kisan masu laifi a Saudiyya: Waɗanda ke jiran hukunci sun kira BBC ta waya
- Marubuci, Aklilu Tsegay
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Tigrinya
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Akwai tsananin damuwa a muryar wani matashi dan kasar Habasha lokacin da ya samu damar tuntubar BBC ta wata wayar da ke cikin ɗakinsa a gidan yarin da ake tsare da masu jiran hukuncin kisa a Saudiyya.
Habtom, wanda aka sauya sunansa domin kare martabarsa kamar yadda aka yi wa ɗayan fursunan da aka ambata a wannan rahoto, ya shafe fiye da shekara uku ana tsare da shi a wani gidan yari da ke birnin Khamis Mushait da ke kudancin Saudiyya.
Duk da hayaniyar fursunonin da ke tare da shi suna ta ihun magana a bayansa, ya roƙi a taimaka masa, kuma ana iya jin ɓacin ransa ganin yadda gwamnatinsa ke nuna kamar ba ta ɗaukar wani mataki don sauya makomarsa ba.
Shi da wasu daga cikin takwarorinsa fursunoni sun tsere daga yaƙi da talauci a ƙasarsu, da fatan samun rayuwa mafi kyau.
Sai dai wannan tafiya ta neman ingantacciyar rayuwa, wadda ta sa suka bi ta Jibuti da Yemen, ta kai shi ga shiga gidan yari, inda ya haɗu da 'yan Habasha da ke tsare a gidajen yarin Saudiyya waɗanda ke fuskantar yiwuwar hukuncin kisa saboda laifukan safarar miyagun ƙwayoyi kuma wadanda ake tsare da su na ci gaba da karuwa.
Domin isar da labarinsu, wasu daga cikin fursunonin sun yi nasarar samun lambar wayar hannu ta Sashen Tigrinya na BBC. Gaba ɗaya, mun tattauna da mutum bakwai daga cikin ɗimbin 'yan Habasha da ke cikin gidan yarin, waɗanda yawansu zai iya kaiwa 200, kuma suna jiran a zartar musu da hukuncin kisa.
Sauran baƙi, ciki har da 'yan Pakistan, Sudan da Jordan, su ma na cikin irin wannan hali. Sai dai a cikin watanni bakwai na farkon wannan shekara, an zartar da hukuncin kisa kan 'yan Habasha 17, wanda shi ne mafi girman adadi a tsakanin waɗanda ba 'yan Saudiyawa ba. Biyar daga cikin waɗannan hukuncin kisan an aiwatar da su ne a ranar Litinin.
Bisa ga wani bincike da ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta gudanar, shekaru biyu da suka gabata an zartar da hukuncin kisa kan 'yan Habasha biyu . Amma a shekarar 2025, adadin ya haura zuwa mutum 35.
Ba a san takamaiman dalilin da ya sa aka samu karuwar wannan adadi ba, amma ana hasashen hakan na iya kasancewa yana da alaƙa da ƙaruwa a yawan mutanen da ke barin yankin Tigray da ke arewacin Habasha, inda wani mummunan yaƙin basasa da ya shafe shekaru biyu ya ƙare a ƙarshen shekarar 2022, bayan ya haddasa mummunar ɓarna da asara mai yawa.
''Hakan kuma na iya kasancewa yana da alaƙa da yadda Saudiyya ke ƙara yawan amfani da hukuncin kisa kan laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi a cikin 'yan shekarun nan," in ji mai bincike a ƙungiyar Amnesty International, Dana Ahmed, a wata tattaunawa da ta yi da BBC
Habtom, wanda kamar yawancin waɗanda BBC ta tattauna da su ya fito ne daga yankin Tigray, an same shi da laifin safarar hashish, wani nau'in hodar iblis da ake samu daga tabar wiwi. A Saudiyya, gwargwadon yadda alƙali ya ga ya dace, samunsa da laifi na iya kaiwa ga yanke masa hukuncin kisa.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama, ciki har da Reprieve da Human Rights Watch (HRW) da kuma Amnesty International, sun ce a irin waɗannan shari'o'i ba kasafai ake bin cikakken tsarin shari'a da ya dace ba.
A cewar Dana Ahmed na Amnesty International, ba a bai wa waɗanda ake tuhuma damar samun lauya ko kwafen takardun shari'arsu ba, yayin da fassarar harshe idan ma an samar da ita, sau da dama ba ta wadatar yadda ya kamata.
Ta ce, ko da yake a rubuce akwai damar ɗaukaka ƙara kan hukunci, rashin samun lauya na hana waɗannan mutane gabatar da ƙorafi ko ɗaukaka ƙara yadda ya kamata, "kuma daga nan sai a tabbatar da hukuncin kai-tsaye".
"Akwai rashin rashin adalci a kusan dukkan matakan shari'ar, tun daga yanke hukunci har zuwa duba shari'ar da Kotun Ƙoli ke yi da kuma amincewar Sarki da hukuncin. Mutanen da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa da iyalansu na rayuwa cikin duhu, ba tare da sanin makomarsu ba."
Habtom ya yi zargin cewa ba a ba shi damar tattaunawa da lauya ko kuma kare kansa a gaban kotu ba. Haka kuma ya ce an tilasta masa sanya hannu a kan wata takarda da aka rubuta da harshen Larabci, wadda ke nuna cewa ya amince da hukuncin da aka yanke masa, alhali bai fahimci abin da ke kunshe a cikin takardar da ya sanya wa hannu ba.
Sauran fursunonin da BBC ta tattauna da su, sun bayar da irin waɗannan korafe-korafe game da tsarin shari'ar.
Kungiyar kare hakkin biladama ta Human Rights Watch (HRW) ta ce ita ma ta yi magana da wasu mutane da ke da kusanci da waɗannan shari'o'i, inda ta samu bayanai kan "hukunce-hukuncen taro da shari'o'in taro da ba su cika ka'idojin shari'a da suka dace ba, da kuma mutanen da aka tsare sannan aka bari suna jira ba tare da sanin lokacin da za a aiwatar da hukuncin a kansu ba."
Mahukuntan Saudiyya ba su mayar da martani ga buƙatar BBC ta neman bayani kan zarge-zargen da ke cewa ba a gudanar da shari'o'in cikin adalci ba. Sai dai duk lokacin da aka aiwatar da hukuncin kisa, hukumomin ƙasar kan fitar da sanarwa ta hannun kamfanin dillancin labarai na gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukuncin ya nuna aniyar mahukuntan ƙasar na kare al'umma daga "annobar miyagun ƙwayoyi" da kuma illolin da suke haddasawa.
Habtom ya ce duk da cewa lokaci zuwa lokaci yana samun damar tuntuɓar iyalansa ta wayar da ke makale a bangon ɗakin da ake tsare da shi, ya ƙi gaya musu cewa yana cikin waɗanda ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa.
"Na gwammace a sanar da su ne bayan mutuwata maimakon a yanzu," in ji shi.
Fatansa shi ne kammala makarantar sakandare, ya shiga jami'a ya kammala karatunsa, sannan ya samu aikin da zai riƙa tallafa wa iyayensa. Sai dai yaƙin Tigray ya rusa wannan buri nasa.
"An rusa burina, don haka na yanke shawarar yin hijira," in ji shi.
Bayan ya tsallake wannan tafiya mai haɗari zuwa Saudiyya a shekarar 2021, Habtom ya samu aiki mai ƙarancin albashi a matsayin makiyayi mai kula da awaki. Sai dai daga baya masu aikin nasa sun ba shi da wasu mutane damar samun ƙarin kuɗaɗen shiga.
Sun ce an bukace su da su kai wani kunshi zuwa wani wuri, amma jami'an 'yan sanda suka tare su a hanya. Bayan bincike, an same su da ganyen da ake kira khat, wani sinadari mai kara kuzari da ake yawan amfani da shi a yankin gabashin Afirka.
Sai dai sanarwar da Saudiyya ta fitar a hukumance duk su bayyana laifin a matsayin safarar hashish. Amma mutanen da BBC ta tattauna da su sun ce abin da ake zargin sun yi safara sa shi ne khat.
"Ban san abin da muke ɗauke da shi ba. Amma daga baya aka gaya mini cewa khat ne. Har yanzu ma ban san mene ne khat ɗin ba," in ji Habtom, yayin da ya amince cewa kuɗin da aka yi masa alƙawarin biya ne ya ja hankalinsa ya shiga aikin.
Habtom ya amince cewa ya "yi kuskure ba tare da ya sani ba", kuma ya bayyana fatan cewa za a sassauta hukuncin da aka yanke masa daga kisa zuwa ɗaurin kurkuku.
An zartar da hukuncin kisa kan uku daga cikin abokan zamansa 'yan Habasha da ake tsare da su a watan Afrilu, sannan aka sake aiwatar da hukuncin kan wasu tara a watan Yuni.
Hukuncin kisan da aiwatar a watan Afrilu ya tayar da hankalin ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da kuma wasu fitattun mutane a Habasha, ciki har da shugaban Cocin 'yan gargajiya ta Orthodox a Habasha, wadda ke tasiri a ƙasar.
BBC ta tuntubi jami'an gwamnatin Habasha da ke Saudiyya da kuma gwamnatin ƙasar a Addis Ababa domin neman martani kan lamarin, amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto ba ta samu wani amsa daga gare su ba.
Ba tare da ta ambaci hukuncin kisa kai tsaye ba, Ma'aikatar Harkokin Wajen Habasha ta fitar da wata sanarwa a ranar 13 ga Yuli inda ta ce tana ci gaba da mu'amala da hukumomin Saudiyya akai-akai, domin "nemo hanyoyin da suka dace na taimaka wa 'yan ƙasar Habasha da ke cikin mawuyacin hali."
Yayin da suke jiran sakamakon ƙoƙarin diflomasiyya da ake yi, fursunonin da suka tattauna da BBC sun ce suna ci gaba da fuskantar matsanancin ƙalubale a gidajen yarin da suka cika da mutane fiye da ƙarfin da aka tanada musu.
Desta, wanda ke tsare a wani sashe daban na gidan yarin, ya ce akwai mutane 200 a cikin ɗakin da yake ciki, duk da cewa an gina shi ne domin ɗaukar mutum 90 kacal. Ya ce akwai gadajen bene 45 da aka jera a gefunan bangon ɗakin.
Ya ce da rana fursunonin kan zauna a ƙasa cikin matsanancin zafi da cunkoso, suna manne da juna saboda ƙarancin wuri. Da daddare kuma, idan yanayi ya yi sanyi, sukan lulluɓe jikinsu da buhunan shara maimakon zanin gado, domin samun ɗan kariya daga sanyi.
"Fargabar fuskantar hukuncin kisa, haɗe da yanayin cunkoso da muke ciki, na jefa mu cikin haɗarin kamuwa da cututtuka da shiga cikin matsanancin damuwa," in ji Desta.
"Jami'in gadin kan buɗe ƙofar ne kawai domin kawo mana abinci, inda yake rufe baki da hancinsa da abin rufe fuska. Wannan ne kaɗai lokacin da ake buɗe ƙofar. Bayan ya ba mu abincin, sai ya gaggauta kulle ƙofar ya tafi," in ji Desta.
"Ba za mu iya yi musu wata tambaya ko mu yi magana da su ba. Ko da ka yi ƙoƙarin tambaya, ana iya yi maka mummunan duka," in ji Desta.
An kama shi ne fiye da shekara uku da suka gabata yayin da yake ƙoƙarin tsallaka kan iyaka daga Yemen zuwa Saudiyya, inda aka zarge shi da safarar miyagun ƙwayoyi.
"Mun kasance 'yan Habasha huɗu, kuma akwai wani ɗan Yemen tare da mu. Ya gaya mana cewa zai iya taimaka mana mu tsallaka kan iyaka cikin aminci domin ya san hanyar da ta fi aminci. A madadin haka, ya nemi mu ɗauki wasu kunshe-kunshe da ke ɗauke da khat, har ma ya yi mana alƙawarin zai ba mu wasu kuɗaɗe," in ji shi.
"Abin takaici, jim kaɗan bayan mun tsallaka kan iyakar, jami'an 'yan sanda suka kama mu. Sun bude mana wuta, kuma mutumin ɗan Yemen ɗin ya tsere, amma mu ba mu samu damar guduwa ba. Mun shiga firgici kuma ba mu san inda za mu dosa ba," in ji shi.
Kamar sauran waɗanda BBC ta tattauna da su, Desta ya ce bai taɓa tsammanin za a yanke masa hukuncin kisa ba, domin ya yi imanin cewa daga ƙarshe za a sake shi ya koma ƙasarsa bayan ya kammala zaman gidan yari.
A maimakon haka, ya yi zargin cewa shi ma an tilasta masa sanya hannu a kan wata takarda da aka rubuta da harshen Larabci, wadda ta ƙunshi tuhume-tuhumen da hukuncinsu zai iya kaiwa ga kisa. Daga baya, lokacin da ya bayyana a gaban kotu, ya ce ba a ba shi damar ƙalubalantar tuhume-tuhumen da ake masa ba, kuma ba shi da wakilcin lauya.
"Lokacin da ka bayyana a gaban alƙali a karon farko, tambayar da zai yi maka ita ce: 'Ka amince da tuhume-tuhumen da ake maka?' Idan kuma ka sake bayyana a gabansa a karo na biyu, sai ya yanke maka hukuncin kisa," in ji Desta.
A matsayinsa na mai sana'ar yin tubali da ke fama wajen tallafa wa iyalansa, ya bar yankin Tigray ne a lokacin yaƙin, yayin da rikicin ke ƙara matsowa kusa da yankin da yake zaune.
Yanzu kuma, yana sake fargabar rayuwarsa. Shi da Habtom, tare da wasu da dama daga cikin waɗanda ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa, na ci gaba da roƙon a kawo musu ɗauki daga wajen gidan yarin.