Sirri 5 kan yadda za ku iya nasara a kasuwancinku

Tela

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Yasmin Rufo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Mai yiwuwa sunan Marcia Kilgore ba ya cikin wadanda ake saurin ganewa, amma kamfaninta na Beauty Pie ya shahara a sassan duniya daban-daban saboda yadda ya kawo sauyi a harkar masana'antar kayan kwalliya ta hanyar tsarin sayarwa da ya ta'allaka kacokan a intanet tare da tsarin biyan kuɗin rajista.

Kafin ta kafa kamfanin Beauty Pie a shekarar 2016, Kilgore ta riga ta kafa wasu fitattun kamfanoni da suka hada da cibiyar kula da lafiya da walwala ta Bliss, da kamfanin kayan shafe-shafe da kula da fata na Soap & Glory, sannan da kamfanin takalma na FitFlop.

A nan, fitacciyar 'yar kasuwa mai shekaru 57 wadda ta kafa kamfanoni masu yawa, ta bayar da labarin yadda ta kai ga nasara tare da bayyana muhimman darussa guda biyar da ta koya a tafiyarta ta kasuwanci.

Ba lallai ba ne ka kasance kana da cikakken tsari tun daga farko

Kilgore ba ta san za ta zama 'yar kasuwa ba, amma tun tana yarinya ta ga da idonta irin matsin lamba da damuwar da rashin tabbas na harkokin kuɗi kan haifar wa iyalai.

''Na tuna tun ina da shekara takwas na yanke shawarar cewa idan na kai shekarun iyayena, ba zan so in riƙa damuwa kan yadda zan biya kuɗin wutar lantarki ba," .

"Na san cewa yi wa wasu aiki ba lallai ne ya ba ni irin 'yancin da nake nema ba. Aƙalla idan kai ne ka mallaki kasuwancinka, kasadar da ake ɗauka taka ce, kuma kai ne ke da iko da yadda za ka tunkare ta," in ji ta.

Ba ta fara da wani babban ko cikakken shirin kasuwanci ba. Maimakon haka, ta bar Kanada zuwa birnin New York domin yin karatu a Jami'ar Columbia. Sai dai shirin da ta yi na biyan kuɗin karatun ya ci tura, lamarin da ya tilasta mata neman aiki domin ta riƙa ɗaukar nauyin kanta.

"Ba za ka iya zama kawai kana tunanin , 'Me zan yi ne?' . Dole ne ka nemi hanyar rayuwa. Na san dole ne in yi amfani da ƙwarewar da nake da ita domin ɗaukar nauyin kaina, sannan daga baya in gano matakin da zai biyo baya," in ji ta.

Ta fara aiki a matsayin mai horas da mutane kan motsa jiki da kula da lafiyar jiki, sannan da yamma tana daukar darussa kan harkar kwalliya da kula da fata.

"Abin da ya faru daga ƙarshe shi ne na gano cewa na ƙware sosai a aikin da ya shafi harkar kayan kwalliya," in ji ta. Daga bisani kuma ta yanke shawarar barin jami'a domin mayar da hankali kan gina sana'arta a wannan fanni.

Ka san aikin da kake yi dalla-dalla

Marcia Kilgore tana yi wa wata kwastoma kulawar fuska, a yayin da aka ajiye yankan kokwamba a gefenta.

Asalin hoton, Marcia Kilgore

Bayanan hoto, Marcia Kilgore a 1999
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kilgore daga cibiyarta ta kula da kwalliya da walwala, ta ce tana sa hannu a kusan kowane ɓangare na kasuwancinta, tun daga wanke kayayyaki da tufafi, zuwa gudanar da ayyukan kula da kwastomomi, har ma da horas da ma'aikata.

Ta ce wannan ƙwarewar da ta samu a aikace ta kasance mai matuƙar amfani gare ta lokacin da ta buɗe cibiyar kula da kwalliya da walwala ta Bliss Spa a birnin London a shekarun 1990.

"Na horas da mutane da dama kafin na buɗe cibiyata, amma da muka fara aiki sai ta cika da kwastomomi sosai. Wasu daga cikinsu suka tsorata da yawan aikin, har suka bar aikin," in ji ta.

"Abu mai kyau shi ne, na san yadda ake cire gashin jiki , sannan kuma na ƙware wajen kula da fuska. Saboda haka na sami damar kula da dukkan kwastomomin da kaina," in ji ta.

Shawarar Kilgore ita ce mutum ya fara kasuwanci a fannin da yake da cikakkiyar masaniya a kai.

"Ya kamata ka kasance kana da zurfin ƙwarewa da ilimi a abin da kake yi, ta yadda ba za ka shiga ruɗani ba idan mutane sun ba ka kunya ko kuma wasu abubuwa marasa zato suka taso suka girgiza shirinka," in ji ta.

Ka riƙa sake nazarin ra'ayoyinka da kanka

.

Asalin hoton, Marcia Kilgore

Bayanan hoto, Marcia Kilgore

Kilgore ta ba da shawarar cewa mutum ya riƙa tambayar kansa dalilin da zai sa mutane su damu ko su nuna sha'awa ga ra'ayinsa, sannan ya kasance yana iya bayyana amfanin wannan ra'ayi cikin jimla guda mai sauƙi kuma a sarari.

"Idan ba za ka iya amsa tambayar, 'To meye amfanin hakan?' cikin jimla guda ba, to hakan na nufin ra'ayinka bai kai matsayin da zai gamsar da mutane ba tukuna," in ji ta.

Ta ce hakan ba lallai yana nufin a yi watsi da ra'ayin ba, amma akwai bukatar a ƙara tace shi da inganta shi domin manufarsa ta kasance mai sauƙin fahimta nan take ga duk wanda ya ji bayani a kansa.

Kilgore ta kuma yi gargaɗi game da abin da ta kira "son zuciya ga ra'ayin mutum", wato lokacin da mutum yake ganin ra'ayinsa yana da matuƙar kyau kawai saboda shi ne ya ƙirƙire shi ko ya mallake shi.

"Kana iya ganin ra'ayinka a matsayin abin burgewa ƙwarai, amma a zahiri kana rayuwa ne a cikin duniyar tunaninka kawai," in ji ta.

Ta ba da shawarar cewa mutum ya riƙa gwada ra'ayinsa a wajen mutanen da yake sa ran za su kasance kwastomominsa kafin ya zurfafa wajen zuba jari a wani abu da watakila babu wanda ya damu da shi face shi kaɗai.

Ta kuma ƙara da cewa ƙirƙirarriyar basira ta (AI) a yanzu ta buɗe manyan damammaki ga masu son fara kasuwancinsu, domin a cewarta, "ba sai kana da babban kasafin kuɗi domin ɗaukar masu ba da shawara ba."

"AI na iya taimaka maka wajen nazari kan ra'ayinka ta fannoni daban-daban, ya ƙalubalanci wasu daga cikin zato da ka yi, sannan ya ba ka shawara kan abubuwan da ya kamata ka yi la'akari da su waɗanda watakila ba su fito maka fili ba," in ji ta.

4. Ka shirya fuskantar ƙalubale da sadaukarwa, kuma ka kasance mai kirki

A lokacin da take fara sana'arta, Kilgore ta fahimci cewa dole ne ta kasance mutum mai kyakkyawar mu'amala da mutane, wanda mutane za su riƙa jin daɗin kasancewa tare da ita.

"Na fahimci cewa dole ne in kasance irin mutumin da mutane ke fatan yin aiki tare da shi ko kuma kasancewa a kusa da shi," in ji ta.

"Na yi iya ƙoƙarina wajen kasancewa mutum mai fara'a, mai matuƙar aiki tuƙuru, kuma mai nuna ƙwarewa da ƙoƙari fiye da kowa a aikin da nake yi," in ji ta.

"Idan ka yi aikinka yadda ya kamata kuma cikin kwarewa, mutane za su ba ka shawara ga wasu," in ji ta.

Ta ce ba a dauki lokaci mai tsawo ba kafin ta bude wata ƙaramar cibiyar kwalliya, wadda daga baya ta yi suna har ta kasance ana yin rajistar kwastomomi watanni da dama kafin lokacin da za a samu damar yi musu hidima.

Ta kuma bayyana cewa, domin kasuwanci ya yi nasara, dole ne mutum ya kasance a shirye ya yi wasu manyan sadaukarwa.

"Idan kana son kasuwancinka ya yi nasara, dole ne ka kasance a shirye ka sadaukar da lokaci, ƙoƙari da wasu abubuwa da ka saba da su," in ji ta.​

"Ba za ka samu lokaci mai yawa na hutu ba," in ji ta, inda ta bayyana cewa tafiyar da kasuwanci na buƙatar mutum ya kasance yana sa ido kan yadda halayen kwastomomi ke sauyawa, da fitowar sababbin masu fafatawa a kasuwa, da kuma sauye-sauyen da ke faruwa a kasuwar gaba ɗaya.

Wannan sau da yawa na nufin mutum zai riƙa ba da lokacinsa wajen karatu, gudanar da bincike da kuma nazarin sabbin ra'ayoyi, har ma bayan lokutan aikin yau da kullum sun ƙare.

Ka tambayi kanka abin da za ka yi nadama a kai a ƙarshen rayuwa

Wata dabara da Kilgore ta ce ta dade tana amfani da ita a tsawon rayuwarta ta sana'a ita ce abin da ta kira "gwajin nadama na ƙarshe", inda take tambayar kanta ko aikin ko shirin da take son aiwatarwa zai ci gaba da kasancewa mai muhimmanci a gare ta idan ta waiwayi rayuwarta a ƙarshenta.

Ka yi tunanin kana a ƙarshen rayuwarka, sannan ka yi tunani kan abubuwan da za ka yi nadamar rashin aikatawa. Idan akwai wani abu da za ka so ka yi daban, to ka fara yin sa tun yanzu," in ji ta.

"Idan abin da ka aikata bai kasance mai ma'ana ba, ko kuma ba ka taimaka wa mutane ta wata hanya ba, shin za ka gamsu cewa ka tafiyar da rayuwarka yadda ya dace?" in ji ta.

Ta ce a gare ta, nasara ba wai kawai gina wani kamfani ne ba, har ila yau tana da alaƙa da zaɓar ra'ayoyin da suka cancanci a kashe lokaci da ƙoƙari wajen aiwatar da su.