Matuƙin jirgin Amurka da aka harbo a Iran ya faɗi yadda ya tsira

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wani matuƙin jirgin saman rundunar sojin saman Amurka ya bayyana yadda ya yi ta faɗowa daga sama bayan laimarsa ta samu matsala, lokacin da aka harbo jirginsa a sararin samaniyar Iran, lamarin da ya haifar da wata hatsaniyar aikin ceto.

"Lokaci guda da na ɗaga kai sama na ga babu laimar da za ta taimaka mini sauka lafiya, wannan shi ne abin da ya fi ba ni tsoro a rayuwata," in ji matukin, wanda ba a bayyana sunansa ba a hirar da ya yi da shirin 60 Minutes na tashar CBS News.

Wannan shiri da aka watsa ranar Lahadi shi ne karo na farko da ɗaya daga cikin matuƙan jirgin da abin ya shafa a watan Afrilu ya yi magana a bainar jama'a game da abin da ya faru da shi.

Sojojin Amurka biyu da ke cikin jirgin sun yi tsalle daga jirgin bayan ya samu matsala. Sun rabu da juna a yayin saukar gaggawar kuma dole suka ɓuya daga jami'an tsaron Iran har sai da dakarun musamman na Amurka suka zo suka ceto su.

"Mu'ujiza ce ta sa na tsira"

"Kalmar faɗowa daga sama ba tare da iko ba ta dace da abin da ya faru," in ji matukin, wanda aka bayyana da sunan Bravo a cikin shirin.

"Ban fi mayar da hankali kan irin saurin da nake faɗowa ba. Abin da na fi damuwa da shi shi ne yadda zan shawo kan matsalolin da ke gabana, tare da ƙoƙarin buɗe laimar ko cire sassan da suka maƙale domin ta yi aiki yadda ya kamata," in ji shi.

Ya bayyana tsira da rayuwa a matsayin "mu'ujiza", duk da cewa ya samu karaya a bayansa, kafaɗarsa da kuma hannunsa.

Ya ce saurin tafiyar da ya kai shi ƙasa ya kai tsakanin mil 70 zuwa 100 a awa guda, wato kusan kilomita 113 zuwa 161 cikin awa guda.

Ɗaya matukin da aka harbo tare da shi, wanda aka bayyana da sunan Alpha, ya ƙi amincewa a yi hira da shi.

Yadda Iran ta harbo jirgin

Jirgin yaƙin F-15E mai kujeru biyu, wanda darajarsa ta kai dala miliyan 30 (fam miliyan 22), ya faɗi ne bayan makami mai linzami da ake harbawa daga kafaɗa, wanda farashinsa kusan dala 100,000, ya same shi. A cewar tashar CBS, abokiyar hulɗar BBC a Amurka.

Bravo ya ce duk da munanan raunukan da ya samu, ya yi tafiya da hawa tsauni har ya kai saman wani dogon tudu, yayin da yake tsoron ka da sojojin Iran su gano shi.

"Kar ka taɓa bari rashin ƙwarin gwiwa ya sa ka ƙare a talabijin ɗin Iran," in ji shi cikin barkwanci.

An ceto Alpha cikin sa'o'i shida kacal a wani samame da ya haɗa da gumurzu mai tsanani, a cewar Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth.

"An yi musayar wuta tun daga lokacin da aka shiga har zuwa lokacin da aka fita," in ji Hegseth. "Amma sun samu nasarar dawo da Alpha."

Shi kuwa Bravo an ceto shi ne bayan ya shafe sa'o'i 48 a bayan layin abokan gaba.

A wani lokaci, sama da sojojin Amurka 90 ne suke cikin ƙasar Iran suna gudanar da aikin ceton, in ji Admiral Brad Cooper na Rundunar CENTCOM ta Amurka. Ya ƙara da cewa wannan ne karo na farko cikin shekaru 46 da sojojin Amurka suka gudanar da aiki a cikin Iran.

Sai dai jiragen sama da jirage masu saukar ungulu da aka shirya domin fitar da sojojin sun makale a cikin yashin hamada. Hakan ya sa dole aka lalata su yayin da dakarun musamman ke jiran ƙarin tawagar ceto.

CBS ta rawaito cewa biyu daga cikin jiragen da aka lalata kowannensu ya kai kusan dala miliyan 100. Haka kuma an lalata wasu ƙananan jirage masu saukar ungulu na Little Bird domin ka da fasahohin da ke cikinsu su faɗa hannun Iran.

Yaushe za a gama yaƙin Iran da Amurka?

Wannan aiki ya gudana ne kusan makonni biyar bayan fara yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran.

Yanzu yaƙin ya shiga wata na bakwai, kuma yana ƙara zama abin da jama'ar Amurka ba sa goyon baya, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar lokacin yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓukan rabin wa'adin majalisa da za a yi a watan Nuwamba.

Yawancin rashin jin daɗin jama'a ya samo asali ne daga tashin farashin makamashi a duniya da kuma yadda hakan ya jawo hauhawar farashin sauran kayayyaki.

A makon da ya gabata, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen cewa yaƙin zai ci gaba aƙalla har zuwa ranar zaɓe, wato 3 ga Nuwamba.