Ko Yari zai iya kawo wa Tinubu ƙuri'un ƴan Najeriya?

Asalin hoton, Senator Abdul'aziz Abubakar Yari/FB
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Sanata Abdulaziz Yari mai wakiltar Zamfara ta Yamma ne aka sanar a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen takarar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.
Sanarwar da kakakin shugaban Najeriyar, Bayo Onanuga ya fitar, ta lissafo wasu jiga-jigan ƴan siyasa daga arewaci da kudancin ƙasar da za su yi a kwamitoci daban-daban a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Tun bayan sanar da Sanata Yari, mutane da dama ke ta ala-sam barka, yayin da wasu ke ta kushe muƙamin da faɗin cewa ba wani tasiri da zai iya yi.
Gwamnatin APC mai mulki, za ta tunkari zaɓen ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke ta ƙorafi kan matsin rayuwa da rashin tsaro a sassan ƙasar, yayin da gwmanatin ke ta ƙoƙarin fahimtar da ƴan ƙasar matakan ci gaba da take ɗauka na tattalin azriki, da daƙile matsalar tsaron.
"Mun cika alƙawuran da muka ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, kuma mun sanya ƙasar nan a kan hanyar samun ci gaban tattalin arziki. Babu shakka mun fito daga cikin duhun da muke ciki, kuma yanzu muna gab da girbar amfanin tattalin arzikin da zai amfani dukkan ƴan Najeriya." in ji shugaba Tinubu, a sanarwar da Onanuga ya fitar ta kwamitin yaƙin neman zaɓen.
Me ya sa Sanata Abdulaziz Yari ya amshi muƙamin?
Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da naɗa shi Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a zaɓen 2027.
Yari, wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya ce ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da shugabancin jam'iyyar APC bisa amincewar da suka yi da shi.
Ya ce ya karɓi nauyin da aka ɗora masa da muhimmanci.
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da jam'iyyar bisa amincewar da suka yi da shi, injda ya ce ba zai ɗauki "wannan dama da wasa ba".
Yari ya yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓen cikin lumana, haɗin kai da mutunta dukkan ƴan Najeriya.
Ya kuma ce za a fara aikin nan take, tare da kira ga ƴan Najeriya da ke da bambancin ra'ayoyin siyasa da su zaɓi abin da zai kawo musu ci gaba maimakon rarrabuwar kai.
A tsarin kwamitin, Yari zai kasance Darakta Janar, yayin da aka naɗa Gwamnan Imo, Hope Uzodimma a matsayin sakatare.
Wane tasiri Yari zai yi a sake zaɓen Tinubu?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Jihar Kano (CAS), ya ce naɗin Sanata Yari a muƙamin bai rasa naasaba da gogewarsa a siyasa, musamman saboda ya taɓa takarar wannan kujerar a zaɓen fitar da gwanin da ya gabata.
Masanin na ganin Yari na ci gaba da jan zarensa ne saboda yadda ya nuna cewa har yanzu yana nan da ƙarfinsa.
"Akwai waɗada suka gwada takara da Bola Tinubu a baya, amma duk za a iya cewa jam'iyyar ta gagare su, amma shi har yanzu yana nan," in ji shi.
Wani abin da ya ƙara masa tasiri kuma a cewar Dr Sufi, kyakkyawar alaƙarsa da malaman addinin musulunci, musamman a arewacin Najeriya. Yana ganin su kansu za su yi tasiri wajen jan ra'ayin mabiyansu domin alaƙarsu da Sanata Yarin.
Haka kuma ana kallonsa a matsayin wanda ke yawan tallafa wa marasa ƙarfi a jiharsa, musamman a lokutan ibada da azumi.
Sai dai Dr Sufi ya ce ba lallai ƙimar mutanen da ke cikin kwamitin ya zama daga cikin dalilan da za su sa Tinubu ya yi nasara ba.
"Yawansu ko ƙimarsu ba lallai ne ya zama babban dalili, sai dai ƙila ana ganin kamar kowane ɓangaren al'umma an taɓa su, saboda haka waɗannan ne ake ganin ya rataya a kansu su je su bayyana nasarorin da aka sam," in ji Dr Sufi.
'APC ta yi dabara'
Masu sharhi kan harkokin siyasar Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027, musamman kan shigar wasu manyan ma'aikatan gwamnati cikin kwamitin.
Dr Sufi, ya ce jam'iyyar APC ta yi dabara da ba ta jira sai da ƴan adawa suka fitar da nasu ba, saboda hakan ma zai iya ɗauke hankalin jama'a kan wasu batutuwan.
Wani abu da ya ɗauki hankali a kwamitin in ji D Sufi shi ne yawan mutanen da aka gani a cikin kwamitin, inda ake ganin hakan na nuna akwai wani shiri na musamman da aka yi.
Akwai dai ƙorafe-ƙorafe kan rashin ganin wasu fuskoki da rashin ganin wasu a cikin kwamitin.
Masanin na ganin akwai yiwuwar an kalli alaƙarsa da mutanen da ke yankinsa ya sa aka damƙa mishi wannan aiki.
Sauran mutanen da aka naɗa a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu
Bayan naɗa Sanata Abdulaziz Yari a matsayin Darakta Janar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima su ne za su kasance a matsayin ciyaman da mataimaki a kwamitin yaƙin neman zaɓen.
Shi ma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, zai kasance mataimakin ciyaman na kwamitin.
Sanata Ajibola Bashiru, sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, da Hadiza Bala-Usman za su riƙe muƙaman mataimakan sakatare.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, an naɗa su a matsain mataimakan darakta-janar na yaƙin neman zaɓen a kudanci da arewacin ƙasar.
Za su yi aiki tare da Sanata Bamidele Opeyemi da Sanata Jibril Barau a shiyyoyin biyu.
Haka kuma, an naɗa Sanata Adams Oshiomhole a matsayin mataimakin darakta-janar mai kula da yaɗa manufofin kamfe da haɗa magoya baya.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa kuma zai riƙa mataimakin darakta-janar mai kula da harkokin gudanarwa.
Kwamitin ya kuma naɗa masu magana da yawun kamfen guda biyar, ƙarƙashin jagorancin Dele Alake. Sauran su ne Alwan Hassan, Ayobami Oyalowo, Kemi Asekun-Shittu da Adamu Fanda.
Akwai kuma wasu mukamai da aka ware a kwamitocin daban-daban, waɗanda wasu gwamnoni da ministoci da sauran masu muƙaman gwamnati za su riƙe.
APC na sake nazarin jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu
Sai dai shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sake nazarin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan fitar da jerin sunayen.
Wata majiya daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da ke cikin kwamitin ta tabbatar wa BBC cewa an umurci shugabannin jam'iyyar da fadar shugaban ƙasa da su sake duba jerin sunayen ne saboda kura-kuran da aka samu, ciki har da sanya sunayen wasu jami'an gwamnati da ake ganin bai dace su kasance cikin tsarin yaƙin neman zaɓen jam'iyya ba.
Akwai kuma wasu manyan ƴan jam'iyyar da ake ganin ya kamata su kasance cikin kwamitin ba a samu sunayensu ba ciki har da gwamnoni.
Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, wanda ya jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Haka kuma babu sunan Festus Keyamo, wanda yana ɗaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a 2023.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya jagoranci ɓangaren hulɗa da masu ruwa da tsaki a kwamitin 2023, shi ma ba ya cikin jerin farko.
Sai dai majiyar ta shaida wa BBC cewa, duk da wannan umarnin, ba a janye naɗin Sanata Abdul'aziz Yari a matsayin Darakta-Janar ba, amma za a sake nazari domin yin gyare-gyare da sake fitar da sabon jerin sunayen.
Wane ne Sanata Abdulaziz Yari?
Sanator Abdul'aziz Yari jigo ne kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya, wanda a halin yanzu yake matsayin Sanata mai wakiltar shiyyar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.
Shi tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne na tsawon wa'adi biyu (daga 2011 zuwa 2019) kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF).
An haife shi a 1968 a ƙaramar hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara
Ya fara shiga harkokin siyasa ne gadan-gadan tun farkon Jamhuriya ta Huɗu a shekarar 1999.
Ya yi aiki a matsayin Sakataren jam'iyyar ANPP na Jihar Zamfara, sannan daga baya ya zama Shugaban Jam'iyyar ANPP na Jiha.
A shekarar 2007, an zaɓe shi a matsayin Ɗan Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Anka/Talata Mafara, inda har ya riƙe shugabancin Kwamitin Kashe Kuɗi na majalisar.
A zaɓen shekarar 2011, ya doke tsohon gwamna Mahmud Shinkafi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ANPP.
Ya sake lashe zaɓe a shekarar 2015 a ƙarƙashin sabuwar jam'iyyar APC.











