Da gaske Buhari na neman wa'adi na uku – Buba Galadima

Bayanan bidiyo, Buba Galadima wanda tsohon makusancin Buhari ne na daya daga fitattun 'yan hamayyar gwamnati yanzu
An wallafa

Latsa hoton sama domin sauraren hirar.

Daya daga cikin jiga-jigai a cikin 'yan hamayya a Najeriya, Buba Galadima ya mayar da martani game da bukatar wasu kungiyoyi da ke kiraye-kirayen shugaban kasar ya nemi ci gaba da mulki karo na uku.