Iraola ya kama aikin horas da Liverpool a hukumance

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kocin Liverpool Andoni Iraola ya isa cibiyar horaswar ƙungiyar ta AXA , inda yawancin ƴan wasa da ma'aikatan ƙungiyar za su koma Merseyside a mako mai zuwa a ranar 14 ga Yuli.
Wannan zai bai wa ɗan ƙasar Spain ɗin fiye da wata guda tare da tawagarsa kafin wasan farko na Premier League da Liverpool za ta kara da Newcastle a ranar 23 ga watan Agusta.
To yaya zai kasance ga Iraola da Liverpool a wata mai zuwa?
Daya daga cikin abubuwan farko da za su faru shine nazarin ƴan wasan da suka dawo kafin fara aikin tukuru.
Babban abin da za a mayar da hankali a kai shi ne salon wasan ƙwallon ƙafa mai zafi da saurin gaske, kuma babu makawa za a sami sauye-sauye, a ɓangaren tawagar masu horaswa.
Iraola zai yi aiki tare da Tommy Elphick da Shaun Cooper - waɗanda suka kasance tare da shi a Bournemouth - a matsayin masu horar da ƙungiyar farko.













