Sabuwar cukumurɗar siyasa ta taso a jihar Ribas

Asalin hoton, Sir Siminalayi Fubara/FACEBOOK
Shugabancin jam'iyyar APC da kotu ta mayar kan iko a jihar Ribas ya ayyana duk zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar a jihar ta kudu maso kudancin Najeriya, a matsayin haramtacce da ya saɓa wa doka.
Zaɓukan su ne dai suka fito da Kingsley Chinda - wani na-hannun daman Nyesom Wike, ministan Abuja, babban birnin Najeriya - a matsayin ɗan takarar gwamna na APC bayan Siminalayi Fubara, gwamna mai ci ya janye.
Sauran abokan tafiyar Wike ne suka zama 'yan takarar APC na zaɓuka masu zuwa a guraben majalisar tarayya da majalisar dokokin jihar Ribas.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Mai shari'a Elfreida Oluwayemisi Williams-Dawodu ta Kotun Ɗaukaka Ƙara a ranar Juma'a, ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Jihar RIbas wanda ya soke tarukan jam'iyyar APC da suka samar da shugabancin Cif Tony Okocha.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Darlinton Nwauju mai magana da yawun shugabancin APC da kotu ta mayar kan iko a ƙarƙashin jagorancin Emeka Beke, ya ce dogaro da hukuncin kotun, dukkan masu neman takara da wakilai da harkokin sadarwa da takardu ciki har da shawarwarin da aka cimma a madadin jam'iyyar APC reshen Jihar Ribas daga ranar 20 ga watan Disamban 2024 zuwa 29 ga watan Mayun 2026, ba su da wani tasiri a jam'iyyance.





























