EU ta zargi TikTok da gaza kare ƙananan yara

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Tarayyar Turai ta zargi masu manhajar TikTok da gazawa wajen kare yara daga cutarwa, inda ta ce akasarin yara da ke amfani da dandalin na fuskantar hantara da kuma cin karo da miyagun mutane masu cutar da su.
Hukumar ta ce ya kamata a tabbatar da cewa babu wanda zai iya alaƙa da yara a shafin sai wanda aka bai wa izini.
Babbar mai kula da ɓangaren ci gaban zamani ta hukumar Henna Virkkunen ta ce bai kamata a ce sai yaro ya ga dama ne za a kare shi ba, a maimakon haka ya kamata a kare su da zarar suna kan mahajar.
TikTok ya ce zai yi nazari kan bayanin na Tarayyar Turai domin ganin yadda za su haɗa hannu wajen gyara lamarin.
Idan rahoton na EU ya zama gaskiya, hukumar za ta iya cin tarar TikTok na kuɗi masu yawa da za su kai kashi 6 cikin 100 na jimillar kuɗin da yake samu a shekara.























