KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 15/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Fashi aka yi wa Barcelona - Raphinha

    A

    Asalin hoton, BBC SPORTS

    Dan wasan Barcelona na gaba Raphinya ya ce fitar da ƙungiyarsa da aka yi daga Champion Lig, "fashi aka yi wa Barcelona".

    A duka wasanni biyun da suka buga na gida da waje an korar mata ɗan wasa daya, waɗanda abokiyar hamayyarta Atletico Madrid ta ci ta 3-2 gida da waje.

    A wasan farko an ci Barceola har gida 2-0, yayin da a wasa na biyu Barcelonan ta ci 1-2, amma duk da haka an cire ta.

    A duka wasannin sai da aka fara katin gargaɗi sa'annan daga baya a bayar da jan kati, bayan duba na'urar da ke taimakawa alƙalin wasa.

    Raphina bai buga duka wasannin ba sakamakon raunin da ya ji: "a wajena fashi ne wannan wasan. Ba wai wannan ba har wanda aka fara".

    "Alƙalin wasan bai iya komai ba, hukuncin da ya yi ba wanda hankali zai ɗauka ba ne.

    "Ban san duka nawa Atletico suka yi wa 'yan Barcelona ba, amma alƙalin wasan bai basu ko katin gargaɗi ɗaya ba.

    "Ban san tsoron me suke ji ba idan Barcelona ta yi nasara."

  2. Matasa sun kai kaso 60 na 'yan kwayar da muka kama a shekara 5 - Marwa

    X

    Asalin hoton, Marwa X

    Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA Buba Marwa ya ce sama da kashi 60 na masu ta'ammali da miyagun kwayoyi da suka kama cikin shekaru biyar da suka ggabata matasa ne.

    Adadin mutanen da aka kama ya kai 77,859, wanda haka ke nuni da ta'azzarar ta'ammali miyagun kwayoyi tsakanin matasa.

    Marwa ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da maƙala kaso na 29 zuwa 30 a jami'ar Abuja, wadda ta zama Jami'ar Yakubu Gowon, kamar yadda sanarwar da Femi Babafemi daraktan yaɗa labaran hukumar ya fitar.

    Ya gargaɗi matasan Najeriya musamman waɗanda suke makarantun gaba da sakandire, saboda shaye-shayen yana kassara rayuwar matasan Najeriya da ya kamata su zama masu amfani ga ƙasar.

    Ya ce harkar shaye-shaye ta bar kan titunan Najeriya ta koma cikin makarantu.

  3. An buɗe mashigar Hormuz kuma jirage na wucewa - Trump

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamar yadda muka rawaito cewa, Sojojin Iran sun yi wa jiragen ruwan yankin Gulf da Bahar Maliya, da Tekun Oman idan Amurka ta ci gaba da toshe tashoshin ruwan Iran.

    A ranar Litinin ne Amurka ta ƙaddamar da shirinta na tsoshe tashoshin, a wani ƙarin haske da Amurka ta yi ta ce cikin awa 24 babu wani jirgi da ya wuce ta mashigar.

    A wata tattaunawa da gidan talabijin na Fox, wadda aka naɗa gabanin barazanar ta Iran, Shugaban Amurka Trump yace an buɗe mashigar ta Hormuz kuma jiragen ruwa na dawowa, amma bai yi ƙarin bayani ba.

    A Iran, Trump ya ce "ba mu kammala ba", amma ya ƙara da cewa yana ganin "yaƙi zai faru a kusa" kuma Amurka za ta so tattaunawa kan hakan da Iran.

  4. ADC ta kori Nafi'u Bala Gombe daga jam'iyyar

    W

    Asalin hoton, Nafi'u Bala Facebook

    Jam'iyyar adawa ta ADC ta kori tsohon maitaimakin jam'iyyar na ƙasa mai iƙirarin shugabancin Jam'iyyar Nafi'u Bala Gombe da wani mamba na jam'iyyar Leke Abejide. Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a yayin taronta na ƙasa da ta gudanar.

    An kori Nafi'u Gombe ne dalilin "yi wa jam'iyya zagon ƙasa", kamar yadda Faisal Kabiru ɗaya daga cikin masu magana da jam'iyyar ya shaida wa BBC Hausa, wanda hakan ya jefe jam'iyyar cikin mawuyacin hali.

    An kori nafi'u Gombe tare da wasu da suka haɗa da Kenneth Ehiator daga Abia wanda shi ma yake iƙirarin shugabancin jam'iyya a jihar, da Stella Chukwu da kuma Elias Adiukwu.

    Nafi'u da ya dage kan zama shugaban jam'iyyar ya fitar da sanarwar waɗanda suka shiga jam'iyyar su Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ba halastattun 'yan jam'iyya ba ne, saboda sun shiga ba ta hannunsa ba, kazalika katin 'yan jam'iyyarsu a shi da wani amfani.

    Ya kuma jagoranci zanga-zangar da aka yi a Abuja, wadda ta mayar da hankali wajen neman hukumar zaɓe INEC ta yarda da shi a matsayin halastaccen shugaban ADC.

    A babban taron da jam'iyyar ta gudanar na ƙasa, an amince da David Mark a matsayin shugaban ADC na ƙasa da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare da dai sauransu.

    Idan ba a manta ba, a wani taron manema labarai da ADC ta yi ta nemi Shugaban INEC ya sauka da muƙaminsa saboda cire sunan Sanata David Mark daga shugaban jam'iyyar da sauran muƙarrabansa.

  5. Isra'ila tace tana kai hari da iyaka ƙarfinta a kudancin Lebanon

    t

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar Dakarun tsaron Isra'ila ta ba ba da sanarwar mutane sun ƙauracewa yankin kudancin Lebanon inda tace "tana kai hare-harenta na sama a yanzu".

    Hukumar tace ana kai harin ne da ƙurewar ƙarfi a yankin kudancin tekun Zahrani, kuma akwai buƙatar mutane su fice daga wajen cikin gaggawa su nufi yankin arewaci.

    "Dun wani wanda a yanzu yake zaune a yankin da yake kusa da abubuwan Hezoullah, yana sanya rayuwarsa ne cikin haɗari," kamar yadda sanarwar ta ambato.

  6. Ba a gane unguwannin Tehran, in ji wata mai aikin agani

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Martje van Raamsdonk ya daɗe a Iran tare da hukumar ba da agaji ta Norwegian Refugee Council (NRC) - tun watan November.

    NRC na daga cikin ƙungiyoyin agajin da ba su da yawa a cikin Iran kuma Martje ta shaida wa BBC yadda ta shaida ɓarnar da wannan rikici a ya yi a Tehran babban birnin Iran.

    "Kusan kullum sai sun wurga bam cikin yankin da ke da cunkoson fararen hula a nan Tehran, wanda babban birni ne mai ɗauke da mutane sama da miliyan 10, an lalata gine-gine da yawa sannan ba ma a gane gine-ginen da ke makwabtaka," in ji ta.

    "Abokiyar aikina ta bayyana wani labarin da ta gani mai taɓa zuciya. Suna zaune ne a yankin Tehran a garin Isfahan suna kusa da inda ake kai hare-haren, inda makami mai linzami ke faɗawa.

    "Ƙarar fashewar kullum na girgiza tagoginsu da ƙofofinsu da gine-ginesu kuma hakan na tasiri kan rayuwarsu."

    A

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Sabon shugaban ƙasar Vietnam, To Lam, ya tattauna da takwaransa na China

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon shugaban ƙasar Vietnam, To Lam, ya tattauna da takwaransa na China a yayin ziyarar da ya kai Beijing.

    Kafar yada labarai ta China ta ce Shugaban Xi Jinping, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da Tom Lam, domin ci gaba karfafa akidarsu ta gurguzu.

    Kasashen biyu sun nemi karfafa alakar da suke da ita daman a tsakaninsu ta tattalin arziki, yayin da duniya ke fama da matsaloli na tattalin arziki na daga harajin Shugaba Trump na Amurka.

    A makon da ya gabata ne Tom Lam ya zama shugaban Vietnam mafi karfin iko a cikin gomman shekaru a lokacin da babban taron kasar ya zabe shi a matsayin shugaban kasa, kari a kan matsayinsa na jagoran jam'yyar Gurguzu.

  8. Fafaroma na ziyara a ƙasar Kamaru

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Laraba ne Fafaroma Leo zai isa Kamaru, a bangare na biyu na ziyarar da yake yi a nahiyar Afirka.

    A yayin ziyarar zai gana da Paul Biya, shugaban kasar da ya fi tsufa a duniya, wanda ke jagorantar kasar sama da shekara 40.

    A ranar Alhamis Fafaroman zai je Bamenda, birnin da ke zaman cibiyar, fadan 'yan a-ware, masu neman 'yancin yankin renon Ingilishi na kasar biyu.

    Jagoran na darikar Katolika na duniya zai jagoranci gangami na addu'a, kuma ana sa ran zai gabatar da muhimmin jawabi na sakon zaman lafiya da sasanto.

    Tun bayan da fada ya barke na a-ware a 2017 kasar ta Kamaru, Cocin na Katolika, ke ci gaba da kiran neman tattaunawa da sasanta rikicin cikin ruwan sanyi.

  9. JD Vance ya ce akwai rashin yarda tsakanin masu Iran da Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce ya yi amanna masu shiga tsakani na Iran, suna son a cimma matsaya, amma kuma ya ce rashin yarda tsakanin gwamnatin Amurka da Iran, abu ne da ba za a iya magance shi ba nan take.

    Wakilin BBC ya ce JD Vance ya ji dadi sosai inda Amurka ta tsaya da Iran.

    Ya bayyana hakan ne bayan da Shugaba Trump ya nuna cewa tattaunawa zagaye na biyu a Pakistan ka iya kasancewa nan gaba a makon nan.

    A karshen makon da ya gabata ne tattaunawar da aka yi a Pakistan a kan batun sake bude Mashigar Hormuz, da kuma makomar shirin nukiliya na Iran ta wargaje, abin da ya kai ga Amurka ta datse tashoshin jiragen ruwa na Iran.

    Kwarya-kwaryar yarjejeniyar dakatar da bude wuta a yakin na Amurka da Iran, za ta zo karshe cikin mako daya, kuma Shugaba Trump ya gaya wa kafar yada labarai ta ABC cewa ba ya tunanin tsawaita ta.

  10. A karon farko cikin shekaru an tattauna Isra'ila da Lebanon gaba da gaba

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila da Lebanon sun amince su ci gaba tattaunawarsu ta kai tsaye, bayan ganawarsu ta farko ta gaba da gaba da suka yi cikin gomman shekaru, yayin yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

    Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, wanda ya bayyana haka, ya ce zuwa yanzu ba a kai ga yanke shawarar lokaci da kuma inda za a yi zaman ba.

    Wakiliyar Lebanon a tattaunawar ta Washington - wadda ita ce jakadiyar Lebanon din a Amurka, Nada Hamadeh Moawad, ta bayyana tattaunawar a matsayin mai amfani, yayin da takwaranta na Isra'ila, Yechiel Leiter, ya ce sun yi tattaunawa mai armashin gaske.

    Sai dai babu wani ci gaba da aka samu kan batun dakatar da buɗe wuta da Lebanon ke neman a yi, inda Isra'ila ta kafe cewa lalle ilalla sai ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ɗin wadda Iran ke marawa baya, ta zubar da makamanta.

    Hezbollah dai ta yi watsi da tattaunawar.

  11. An cika shekara uku da fara yaƙin Sudan, wane hali ƙasar ke ciki yanzu?

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da yakin basasar Sudan ya shiga shekararsa ta uku, masu bayar da agaji na taro a birnin Berlin na Jamus, domin tattauna yadda za a ci gaba da samar da taimako dafarfado da tattaunawar zaman lafiya, a kan halin tabarbarewar rayuwa mafi girma a duniya.

    Shekara 3 da ta gabata fada ya barke a Khartoum, babban birnin shi ne cibiyar wannan mummunan yakin basasa, kafin sojojin kasar su sake kwato shi daga mayakan RSF.

    Sama da mutum miliyan 12 ne rikicin, neman ikon tsakanin rundunar sojin Sudan da kuma kungiyar RSF ya raba da muhallinsu.

    fadan ya fara ne a babban birnin kasar Kahartoum, amma ya fantsama har zuwa yammaci da kudancin kasar.

    Duk wani kokari na cimma zaman lafiya ya dakata kuma tattalin arzikin kasar ta Sudan ya durkushe.

    Kashi 65 cikin dari na al'ummar kasar na bukatar abinci da ruwa da matsuguni da kuma magani.

  12. Masu bibiyarmu a wannan shafi Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan an wayi gari lafiya, da fatan nasara a wannan rana ta Laraba.

    Ku kasance da mu kamar kullum domin kawo muka labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran.

    Kazalika da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya na abubuwan nishaɗi, takaici, al'ajabi da kuma ban tausayi.

    Ku kasance da mu.