Gasar kofin duniya 2026: Argentina za ta kara da Masar a zagayen ƴan 16

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen ƙasashe 32
Argentina 3 , Cape Verde 2 After extra time
Argentina
Cape Verde
After extra time
Gama Wasa Argentina 1 , Cape Verde 1,Hutun rabin lokaci Argentina 1 , Cape Verde 0

Key Events

Argentina

  • L. MessiGoal 29 minutes
  • Lisandro MartínezGoal 92 minutes extra time
  • Diney BorgesOwn Goal 111 minutes extra time

Cape Verde

  • Deroy DuarteGoal 59 minutes
  • Sidny CabralGoal 103 minutes extra time
Ba da ƙwallo a ci
Argentina,Lisandro Martínez (29 minutes), A. Mac Allister (92 minutes extra time)
Cape Verde,Ryan Mendes (59 minutes), Yannick Semedo (103 minutes extra time)

Taƙaitattu

  • Ko Argentina za ta fitar da Cape Verde cikin ruwan sanyi kuwa?
  • Masar ta kai zagayen ƴan 16 a gasar kofin duniya, bayan doke Australia a bugun fenariti
  • Masar za ta kara da wadda ta kai zagayen gaba tsakanin Argentina ko Cape Verde a wasan yan 16 nan gaba
  • Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
  • Nagelsmann ya ajiye aikin kociyan Jamus, bayan kasa yin abin kirki a gasar kofin duniya ta 2026
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon A1

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin.

    Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.

  2. Wasan da za a buga ranar Asabar

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Yadda aka kara a wasan, Argentina 3-2 Cape Verde

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  4. An tashi wasan, Argentina 3-2 Cape Verde

    Argentina ta kai zagayen yan 16 a gasar cin kofin duniya, bayan da ta doke Cape Verde 3-2.

    Kenan za ta fuskanci Masar a karawar yan 16.

    Argentina ce mai rike da kofin duniya da ta dauka a Qatar a 2022.

    Cape Verde ta yi kokari, wadda ta hana Kamaru zuwa gasar nan, amma ta yi kokari, sai a wasa na hudu ne ta yi rashin nasara, shi ne a hannun Argentina.

    Koma dai yaya Argentina ta ji a jikinta, ba za ta taba manta Cape Verde ba, wadda sai da kai ruwa rana.

  5. , Argentina 3-2 Cape Verde

    Cape Verde na kara sa matsi ta farke na ukun, amma kamar lokacin ya kure mata.

  6. Kadan ya rage Cape Verde ta farke, Argentina 3-2 Cape Verde

    Sidny Cabral ya i bugun tazara kamar yadda ya zare na biyu, amma Emi Martinez ya gane mai yake son yi ya sawa kwallon hannu da bi saman raga.

  7. , Argentina 3-2 Cape Verde

    An ce Cape Verde ce ta ci gida ta hannun Diney Borges.

  8. GOAL Argentina 3-2 Cape Verde, Cristian Romero

    Kwana ce aka kwaso daga wajen Messi, inda Romero ya yi tsalle ya saka kai ta fada raga.

    Argentina 3-2 Cape Verde

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Argentina ta yi sauyin dan wasa, Argentina 2-2 Cape Verde

    Argentina ta yi canji nan da nan..

    Gonzalo Montiel, wanda ya zura kwallo a wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022 a bugun fenariti, ya maye gurbin Nahuel Molina.

  10. , Argentina 2-2 Cape Verde

    Sidny Lopes Cabral

    Asalin hoton, Getty Images

  11. An je hutu za a koma zango na biyu, Argentina 2-2 Cape Verde

    Za su karasa minti 15, idan wata tawaga ta ci kwallo shike nan idan ba haka ba sai dai bugun fenariti ya fitar da wadda za ta je zagayen gaba na yan 16 da za ta fuskanci Masar.

  12. GOAL Argentina 2-2 Cape Verde, Sidny Lopes Cabral

    Kwallo ce daga bangaren hagu ya dan yi yanka daga nan ya fereta ta kuma yi kwana ta fada ragar Argentina tun daga wajen da'ira ta 18.

    Kwallon ta yi kyau matuka. Cape Verde ba tab hakura ba, ana ci tana farkewa.

    Sidny Lopes Cabral

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Cape Verde ta yi canji biyu, Argentina 2-1 Cape Verde

    Kevin Pina da Deroy Duarte sun fita an kuma sa Yannick Semedo da Gilson Benchimol madadinsu.

  14. Argentina 2-1 Cape Verde

    Asalin hoton, Getty Images

  15. GOAL - Argentina 2-1 Cape Verde, Lisandro Martinez

    An komawa wasan ne Argentina ta kwaso kwana daga hagu cikin gidan Cape Verde aka tashi cin kasuwar sama sai kwallon ta yi gefen dama, inda Martinez ya je a guje ya tara ya kuma sa kafar hagu ya buga da karfi ta fada raga.

    Argentina 2-1 Cape Verde

    Asalin hoton, Getty Images

  16. an ci gaba da wasan, Argentina 1-1 Cape Verde

    Ko Cape Verde za ta ci gaba sa kwazon da zai kai bugun fenariti kuwa?

  17. An kammala minti 90, Argentina 1-1 Cape Verde

    Za su dan huta su koma fili mu ci gaba da wasa na minti 30, kowanne zango minti 15, idan sakamakon ya canja mu tashi idan ba haka ba ta kaimu ga bugun daga kai sai mai tsaron raga.

    Argentina ce ke rike da kofin da ta dauka a Qatar a 2022.

  18. , Argentina 1-1 Cape Verde

    Argentina 1-1 Cape Verde

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Argentina ta samu bugun tazara mai kyau, Argentina 1-1 Cape Verde

    Messi ya buga, amma mai tsaron gidan Cape Verde ya yi kokawa da kwallon da ta kai Argentina ta samu sa mata kai, amma dai ya kama.

  20. An yi karin lokaci, Argentina 1-1 Cape Verde

    An kara minti takwas da zai iya bayar da kara kwallo na biyu ko kuma mu ci gaba da wasan minti 30 nan gaba.

    Idan fa aka ci gaba da haka sai dai fenariti ta raba karawar, kenan an shiga ta mai rabo kenan.