Matatar Dangote ta ƙara yawan man fetur da take tacewa a rana

Asalin hoton, X/Dangote Refinery
Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan man fetur da take tacewa zuwa ganga 700,000 a rana, a wani tacewa ta gwaji da hukumomi suka yi, wanda hakan wani muhimmin mataki ne ga ayyukan matatar wadda ke ƙoƙarin tabbatar da kanta a matsayin mafi girma a duniya.
Wannan na nufin matatar ta ƙara man da take tacewa daga ganga 650,000 a rana.
Mataimakin shugaban sashen man fetur da gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin ya bayyana cewa ƙara yawan man da matatar ke tacewa na daga cikin shirin matatar na nunka yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin shekara biyu da rabi.
Matatar Dangote ta samu karɓuwa tun bayan fara aikinta, inda a yanzu take taka rawa wajen samar da man jiragen sama a ƙasashe da dama.
Sai dai matatar na ci gaba da fuskantar ƙalubale a cikin gida, inda take kokawa kan wasu matakan hukumomin Najeriya, musamman game da bai wa wasu kamfanonin damar shigar da tataccen man fetur daga waje.














