Marco Silva na daf da zama kociyan Benfica, Fulham
Kocin Fulham, Marco Silva, na dab da cimma yarjejeniya domin zama sabon kocin Benfica.
Kwantiragin Silva a Craven Cottage zai ƙare a wannan watan, amma har yanzu ba a fitar da wata sanarwa a hukumance kan ficewarsa daga Fulham ba.
Fulham ta miƙa wa kocin nata ɗan ƙasar Portugal sabon tayin kwantiragi, amma har yanzu bai amince da shi ba.
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawa tsakanin Silva da Benfica ta samu ci gaba sosai a ƴan kwanakin nan, kuma suna gab da cimma yarjejeniya.
Benfica na neman wanda zai maye gurbin Jose Mourinho, wanda ya bar ƙunguyar tare da rattaba hannu kan kwantiragin shekara uku domin zama sabon kocin Real Madrid.
Mourinho mai shekaru 63 ya koma Benfica karo na biyu a watan Satumba, kuma ya jagoranci ƙungiyar zuwa matsayi na uku a gasar Primeira Liga.
Silva ya karɓi aikin horar da Fulham a watan Yulin 2021 bayan da ya bar Everton, kuma ya taimaka wa ƙungiyar komawa Premier League a kakarsa ta farko, bayan sun faɗi zuwa Championship shekara guda kafin hakan.
Fulham ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na 11 a Premier League, inda ta yi kunnen doki da Chelsea da maki 52.
Asalin hoton, Getty Images
, Daga Jaridu
Akwai rashin tabbass game da makomar Marc Cucurella a Chelsea bayan da kungiyoyi da dama suka tuntubi wakilan dan wasan kan barin Stamford Bridge. An ce Atletico Madrid da Barcelona da kuma Real Madrid na daga cikin wadanda ke zawarcin dan wasan na Sifaniya mai shekara 27.(The Athletic - subscription required), external
Liverpool na zawarcin dan wasan RB Leipzig Yan Diomande amma har yanzu ba su cimma matsaya ta baki ba kan cinikin dan wasan na Ivory Coast mai shekara 19. (Sky Sports), external
Newcastle ta bayyana dan wasan bayan Atalanta na Italiya Marco Palestra, mai shekara 21, a matsayin babban dan wasan da take son ta saya a bazara amma za ta iya fuskantar hamayya daga Manchester City da Arsenal da Inter Milan. (Mail), external
Daya daga cikin mutanen da suka mallaki Inter Miami, David Beckham na son ya dauki Pep Guardiola aiki a matsayin sabon kocin kungiyar ta Major League Soccer bayan ya bar Manchester City, sai dai dan kasar Sifaniya zai yi watsi da duk wani tayi na komawa filin wasa nan take.(Mirror), external
Asalin hoton, Getty Images
Bellingham ne zai sa riga mai lamba 10 a Ingila a gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya
An sanar da lambobin rigunan ƴan wasan Ingila a gasar Kofin Duniya ta wannan bazara, amma shin waɗannan zaɓuɓɓukan suna nuna yadda Thomas Tuchel ke tunani game da tawagarsa ta ƴan wasa 11 da za suke fara buga masa tamaula?
Ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham, wanda a ƴan watannin nan aka fara tambayar ko har yanzu yana cikin manyan tsare-tsaren Tuchel, an ba shi fitacciyar riga mai lamba 10. Shin hakan na nuna cewa shi ne zai ja ragamar gurbin mai kai hari daga tsakiya a gaban Morgan Rogers na Aston Villa, wanda aka ba lamba 17?
A wani bangaren kuma, Nico O’Reilly na Manchester City ya samu riga mai lamba 3, abin da zai ƙara ƙarfafa ra’ayin cewa zai shiga gasar a matsayin zaɓin farko na Ingila a matsayin ɗan baya daga hagu.
Ɗan wasan Newcastle, Dan Burn, wanda shi ma zai iya taka rawa a matsayin mai tsaron baya daga hagu, zai sanya riga mai lamba 15.
Ga jerin rigunan da aka bai wa ƴan wasan Ingila:
Jordan Pickford
Ezri Konsa
Nico O'Reilly
Declan Rice
John Stones
Marc Guehi
Bukayo Saka
Elliot Anderson
Harry Kane
Jude Bellingham
Marcus Rashford
Tino Livramento
Dean Henderson
Jordan Henderson
Dan Burn
Kobbie Mainoo
Morgan Rogers
Anthony Gordon
Ollie Watkins
Noni Madueke
Eberechi Eze
Ivan Toney
James Trafford
Reece James
Djed Spence
Jarell Quansah
Asalin hoton, Getty Images
Baumgartner ba zai buga wa Austria kofin duniya ba, Gasar kofin duniya
Ɗan wasan tawagar Austria, Christoph Baumgartner, ba zai buga gasar Kofin Duniya ba, bayan da ya ji rauni, yayin ɗumama jiki kafin wasa, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta sanar a ranar Talata.
Ɗan wasan mai shekara 26 ya ji raunin ne yayin da yake shirye-shiryen wasan sada zumunci da Tunisia a ranar Litinin, inda gwajin MRI ya tabbatar da cewa ba zai iya halartar gasar ba.
Baumgartner ya yi kakar wasa mai kyau tare da RB Leipzig, inda ya zura kwallaye 17 tare da bayar da tara aka zura a raga.
Sai dai Austria ta samu labari mai daɗi bayan ƙyaftin ɗin tawagar, David Alaba, ya samu izinin tafiya tare da tawagar bayan an tabbatar da cewa raunin da ya sa aka cire shi a hutun rabin lokaci a wasan da suka ci 1-0 ba mai tsanani ba ne.
Tawagar Austria za ta tashi zuwa gasar a ranar 4 ga watan Yuni.
Za ta fara wasanta na rukuni da Jordan a ranar 16 ga watan Yuni, kafin daga bisani ta kara da masu riƙe da kofin duniya Argentina da kuma Algeria.
Asalin hoton, Getty Images
Uzbekistan ta sanar da ƴan ƙwallon da za su buga gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya
Kocin Uzbekistan, Fabio Cannavaro, ya sanar da tawagar ƴan wasan da za su wakilci kasar a gasar Kofin Duniya a karon farko a tarihinta.
Tawagar ta dogara ne da ɗan gaba Eldor Shomurodov da kuma mai tsaron baya, Abdukodir Khusanov. Kyaftin Shomurodov zai kasance babban mai tare hare-hare, tare da abokin wasansa na Istanbul Başakşehir, Abbosbek Fayzullaev.
Khusanov mai shekaru 22 na Manchester City ya sha fama da rauni a farkon kakar wasan bana, amma ya dawo yana buga wasa akai-akai a ƙarshen kakar, inda ya taimaka musu lashe FA Cup da League Cup a Ingila.
Uzbekistan za ta fara wasanta na Rukunin 11 da Colombia, sannan ta kara da Portugal da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo).
Jerin ƴan wasan tawagar Uzbekistan a gasar kofin duniya:
Masu cin ƙwallaye: Eldor Shomurodov (Istanbul Basaksehir), Igor Sergeev (Persepolis), Azizbek Amonov (Bukhara)
Asalin hoton, Getty Images
Turkiya ta bayyana ƴan wasan da za su buga gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya
Kocin Turkiyya, Vincenzo Montella, ya sanar da jerin ƴan wasan da za su buga gasar Kofin Duniya, inda ya zaɓi ƙwararrun ƴan wasa kamar Hakan Çalhanoğlu da Arda Güler da Kerem Aktürkoğlu da Barış Alper Yılmaz domin jagorantar tawagar.
An cire ɗan wasan tsakiya na Sporting Braga, Demir Ege Tıknaz, yayin da Montella ya mayar da hankali kan Kaan Ayhan na Galatasaray da Salih Özcan na Borussia Dortmund.
A ɓangaren kai hari, an cire Aral Şimşir, wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasa a gasar Denmark, amma an saka İrfan Can Kahveci cikin tawagar.
Turkiyya tana cikin Rukuni na huɗu a gasar Kofin Duniya, kuma za ta fara wasa da Australia, sannan ta kara da Paraguay da kuma Amurka, wadda ke ɗaya daga cikin masu karɓar bakuncin gasar.
Jerin ƴan wasan tawagar Turkiya da za ta buga kofin duniya:
Masu tsaron raga: Altay Bayindir (Manchester United), Mert Gunok (Fenerbahce), Ugurcan Cakir (Galatasaray)
Masu cin ƙwallaye: Arda Guler (Real Madrid), Baris Alper Yilmaz (Galatasaray), Can Uzun (Eintracht Frankfurt), Deniz Gul (Porto), Irfan Can Kahveci (Kasimpasa), Kenan Yildiz (Juventus), Kerem Akturkoglu (Fenerbahce), Oguz Aydin (Fenerbahce), Yunus Akgun (Galatasaray)
Asalin hoton, Getty Images
, Daga Jaridu
Dan wasan Portugal Bernardo Silva na shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da Barcelona bayan ya bar Manchester City kuma dan wasan mai shekara 31 yana son a kammala cinikin a hukumance kafin karshen mako.(AS - in Spanish), external
Watakila dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, ya koma Manchester United a shirye-shiryen kakar wasa ta bana, yayin da komawarsa Barcelona, inda ta kasance aro a kakar wasan da ta gabata, ta gamu da cikas.(Times - subscription required), external
Manchester United na son ta cefanar da Rashford domin taimaka wa sabon kocin kungiyar Michael Carrick' samun kudin musayar 'yan wasa kuma Arsenal da Chelsea da Newcastle da Tottenham na bibiyar halin da ake ciki . Kungiyar dai ba ta son ta sayar da dan wasan ga daya daga cikin manyan abokan hammayarta. (Mirror), external
Nottingham Forest za ta tattauna da dan wasan tsakiya Ibrahim Sangare, mai shekara 28, kan sabon kwantaragi yayin da Manchester United da Besiktas ke zawarcin dan kasar ta Ivory Coast.(Football Insider), external
Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin kocin Afirka ta Kudu ya samu bizar shiga Amurka ranar Talata, Gasar kofin duniya
Mataimakin kocin Afirka ta Kudu, Helman Mkhalele, ya samu bizar shiga Amurka ranar Talata, kuma zai tashi zuwa sansanin tawagar a Pachuca, Mexico, bayan da ƴan wasa da sauran ma’aikatan suka tafi gasar ba tare da shi ba a ranar Litinin.
Tafiyar Afirka ta Kudu zuwa gasar Kofin Duniya ta farko tun lokacin da suka karɓi bakunci a 2010 ta shiga rudani, bayan da aka gano cewa kuskuren gudanarwa ya sa yawancin ƴan wasa da ma’aikatan horarwa ba su samu bizar da ake buƙata ba a ranar da ya kamata su tashi da jirgin haya a ranar Lahadi.
Za su fara wasa da ƙasashen da ke karɓar bakunci, Mexico, a wasan buɗe gasar a Mexico City a ranar 11 ga watan Yuni, kuma sun rasa aƙalla rana guda na shiri da sabawa da yanayin Pachuca.
An fara ƙin amincewa da bukatar bizar Mkhalele da kuma Mdu Mbatha, daga Ofishin Jakadancin Amurka da ke Johannesburg saboda dalilan da ba a bayyana ba, amma yanzu an amince da su.
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu, Danny Jordaan, ya ce: “Zan tabbatar da cewa Helman da Mbatha sun samu bizar su, kuma za su tafi su haɗu da tawagar ranar Laraba duk za su kasance tare.”
Ya kuma ƙara da godiya ga ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka.
Afirka ta Kudu za ta buga wasan sada zumunci da Jamaica a ranar Juma’a.
Suna cikin Rukunin A a gasar Kofin Duniya, inda bayan Mexico za su kara da Jamhuriyar Czech a Atlanta a ranar 18 ga watan Yuni, sannan su kara da Koriya ta Kudu a Monterrey kwanaki shida bayan nan.
Asalin hoton, Getty Images
Rodri zai yanke makomarsa a Man City bayan kofin duniya
Ɗan wasan tawagar Spain, Rodri, ya ce hankalinsa ya karkata ne kan Kofin Duniya, kuma zai yi magana kan makomarsa a Manchester City ne kawai bayan kammala gasar.
Wanda ya lashe ƙyautar Ballon d’Or ta 2024 ya shiga shekararsa ta ƙarshe a kwantiraginsa da Etihad mai buga gasar Premier League, kuma ana danganta shi da yiwuwar komawa Real Madrid.
Spain mai rike da kofin nahiyar Turai za ta kara da Cape Verde, Saudi Arabia da Uruguay a Rukunin takwas a gasar da za a fara daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli a Arewacin Amurka.
Rodri ya ce ya kuma bukaci abokan wasansa na Spain su yi koyi da jarumin wasan tennis Rafael Nadal bayan ya kalli shirin bidiyo (documentary) game da shi.
Asalin hoton, Getty Images
, Daga Jaridu
Dan wasan kasar Ivory Coast Evann Guessand, mai shekara 24, na nazari kan kungiyar da zai koma bayan karewar wa'adin aronsa daga Aston Villa zuwa Crystal Palace don mayar da cinikin na dindindin .(Evening Standard), external
Aston Villa na son ta bar dan wasan Sifaniya Andres Garcia, mai shekara 23, barin kungiyar a matsayin aro a lokacin bazara, inda Valencia da Elche na cikin cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa. (Tribuna Deportiva - in Spanish), external
Tottenham ta bayyana dan wasan Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya a matsayin dan wasan da take son ta saya, amma kungiyar ta Bundesliga ba za ta bar dan Faransa mai shekara 21 ya tafi a farashi mai rahusa ba.(Teamtalk), external
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta yi nisa kan tattaunawa da Iraola domin ba shi aikin koci, Liverpool
Liverpool ta yi nisa kan tattaunawa da Andoni Iraola yayin da suke neman sabon kocin ƙungiya, bayan korar Arne Slot.
Iraola ya bar Bournemouth a ƙarshen kakar wasan bana, kuma shi ne wanda ake ganin ya fi kusa da samun aikin horar da Liverpool a Anfield.
Liverpool na son yin nadin koci da wuri-wuri, kuma tana neman kocin da ya dace da salon wasansu da suka fi so—wato ƙwallon ƙafa mai kai hari da kuma matsa wa abokin hamayya lamba.
Har yanzu ba a fara tattaunawa kan ma’aikatan horarwa na Iraola ba, amma ɗan ƙasar Spain ɗin mai shekaru 43 yana sha’awar ɗaukar mataimakinsa a Bournemouth, Tommy Elphick, wanda kuma tsohon mai son Liverpool ne tun yana yaro, domin ya zo tare da shi.
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta yi watsi da tayin sayen Acheampong, Premier League
Chelsea ta ƙi karɓar tayin da ƙungiyoyi da dama da suka yi domin sayen mai tsaron baya, Josh Acheampong.
Ɗan wasan mai shekara 20, wanda ya fito daga makarantar horas da ƴan wasa ta Stamford Bridge, an ba shi matsayin “wanda ba za a taɓa sayarwa ba” dangane da makomarsa a ƙungiyar ɗin.
Wannan ya sanya shi a cikin rukuni ɗaya da ƴan wasa kamar João Pedro da Cole Palmer a gaba, da kuma Moisés Caicedo.
Hakan na zuwa ne duk da cewa ɗan wasan Ingila na ƴan kasa da shekara 21 ya buga wasa 17 a Premier League a kakar da ta gabata, inda tara daga cikinsu ya fara daga benci.
Har yanzu ba a tabbatar ba ko Acheampong, wanda kwantiraginsa da Chelsea zai kare a 2029, yana son barin ƙungiyar.
Sai dai Arsenal, Newcastle da Crystal Palace na sa ido kan halin da yake ciki, yayin da Bournemouth kuma ke ci gaba da nuna sha’awar sayensa tun a bara.
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan takarar shugabancin Fenerbahce na son sayen Greenwood, Kwallon kafa
Mason Greenwood shi ne babban ɗan wasan da dukkan ƴan takarar shugabancin Fenerbahce biyu ke son saye.
Tsohon ɗan wasan Manchester United da tawagar Ingila ya sha wahala a ƴan watannin nan a Marseille.
Sabon daraktan wasanni na ƙungiyar, Gregory Lorenzi, ya ce a makon da ya gabata cewa a shirye yake ya saurari tayin sayen Greenwood, wanda ya rage masa shekara uku a kwantiragin shekaru biyar da ya kulla lokacin da ya bar Manchester United a watan Yulin 2024.
Tsohon shugaba, Aziz Yildirim, na fafatawa da Hakan Safi kan kujerar shugabancin ƙungiyar ta Turkiyya, kuma ana sa ran za a sanar da sakamakon a ranar Lahadi.
An ce ba a ganin cewa samun yarjejeniya da Greenwood zai zama matsala.
Ɗan wasan ya koma gina rayuwarsa ne a wajen Manchester United duk da cewa an janye tuhumar da ake masa na yunƙurin fyade da cin zarafi a watan Fabrairu 2023.
Bincike na cikin gida ya kammala cewa Greenwood ba zai sake buga wa United wasa ba. A watan Afrilu, sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, ya nemi afuwa bayan ya kare Greenwood a lokacin da yake Marseille.
Ɗan wasan mai shekaru 24 ya zura kwallaye 48 a wasa 81 da ya buga wa Marseille. Ya gama kakar Ligue 1 da kwallaye 16, inda ya zo na biyu a jerin masu yawan cin kwallaye, bayan Esteban Lepaul na Rennes.
Fenerbahce ta kare a matsayi na biyu a gasar Super Lig ta Turkiyya har sau biyar a jere, kuma za ta shiga gasar Champions League daga zagayen share fage na biyu a watan Yuli.
Asalin hoton, Getty Images
An saka Partey cikin tawagar Ghana da za ta buga kofin duniya, Gasar kofin duniya
Tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey, yana cikin ƴan wasa tawagar Ghana Ghana da za ta halarci gasar Kofin Duniya a bana.
Partey ya musanta laifuka guda bakwai na yi wa mata fyade da kuma ɗaya na cin zarafi, da ake zarginsa da aikatawa tsakanin 2020 zuwa 2022, dangane da korafe-korafe daga mata huɗu daban-daban.
Ɗan wasan mai shekara 32, wanda yanzu ke buga wa Villarreal tamaula a La Liga, zai gurfana a gaban kotu a shekara mai zuwa.
Partey ya buga wa Arsenal wasa 167 a dukkan fafatawa tsakanin 2020 zuwa 2025, amma ya bar Emirates a bazarar da ta gabata bayan kwantiraginsa ya ƙare.
Kocin Ghana, Carlos Queiroz, ya saka Partey cikin jerin ƴan wasa 28 na wucin gadi domin atisaye kafin Kofin Duniya da kuma wasan sada zumunci da Wales a Cardiff a ranar 2 ga Yuni.
Partey ya ci gaba da kasancewa cikin tawagar yayin da Queiroz ya cire masu tsaron raga Solomon Agbasi da Paul Reverson domin rage adadin zuwa ƴan wasa 26 na ƙarshe.
An cire mai tsaron baya Alexander Djiku bayan da ya ji rauni a yayin da Spartak Moscow ta lashe kofin Russia, don haka aka maye gurbinsa da Derrick Luckassen, wanda aka haifa a Netherlands kuma ya fara buga wa Ghana tamaula a watan Maris.
Haka kuma akwai Antoine Semenyo na Manchester City da Brandon Thomas-Asante na Coventry, tare da ƴan wasan Leicester Jordan Ayew da Abdul Fatawu.
Joseph Anang, wanda ke buga wa St Patrick Athletic a League of Ireland, yana ɗaya daga cikin masu tsaron raga uku a tawagar.
Mai taka leda a Tottenham, Mohammed Kudus bai samu goron gayyata ba, saboda raunin ƙafa da ya hana shi buga wasa tun watan Janairu.
Jerin ƴan wasa 28 da Ghana ta bayyana:
Masu tsaron raga: Benjamin Asare (Accra Hearts of Oak SC), Lawrence Ati-Zigi (St Gallen), Joseph Anang (St Patrick's Athletic).
Masu tsaron baya: Baba Abdul Rahman (PAOK), Gideon Mensah (Auxerre), Marvin Senaya (Auxerre), Alidu Seidu (Rennes), Abdul Mumin (Rayo Vallecano), Jerome Opoku (Istanbul Basaksehir), Jonas Adjetey (Wolfsburg), Kojo Oppong Peprah (Nice), Elisha Owusu (Auxerre), Derrick Luckassen (Pafos).
Masu buga tsakiya: Thomas Partey (Villarreal), Kwasi Sibo (Real Oviedo), Augustine Boakye (Saint-Etienne), Caleb Yirenkyi (Nordsjaelland), Abdul Fatawu Issahaku (Leicester City).
Masu cin ƙwallaye: Kamaldeen Sulemana (Atalanta), Christopher Bonsu Baah (Al Qadsiah), Ernest Nuamah (Lyon), Antoine Semenyo (Manchester City), Brandon Thomas-Asante (Coventry City), Prince Kwabena Adu (Viktoria Plzen), Inaki Williams (Athletic Bilbao), Jordan Ayew (Leicester City).
Asalin hoton, Getty Images
‘Yansanda sun kama mutum 24 bayan soka wa mutum 6 wuka wajen bikin murnar lashe kofin Arsenal
Yansanda sun kama mutum 24 a Landan bayan soka wa mutum 6 wuka a gangamin murnar lashe kofin da kungiyar Arsenal ta yi a birnin.
Hukumar ‘yansanda birnin Landan ta ce wadanda aka soka wa wukar ba su samu munanan raunuka ba, sai dai an garzaya da wani matashi dan shekara 20 asibiti saboda yana cikin mawuyacin hali.
‘Yansandan sun ce an soki matashin ne a titin Hornsey, jim kadan kafin karfe 8:30 na daren ranar Lahadi.
Fiye da ‘yansanda 500 ne aka baza a birnin Landan domin tabbatar da doka a bikin, wanda ya tara dubun dubatar magoya bayan kungiyar Arsenal domin murnar lashe kofin gasar Premier karon farko a cikin shekara 22.
Ana sa ran Iraola ne zai maye gurbin Slot a Liverpool, Liverpool
Andoni Iraola shi ne kan gaba da ake ganin za a bai wa akin kociyan Liverpool, bayan da ta kori, Arne Slot a ranar Asabar.
An fahimci cewa Iraola ya riga ya tattaunawa da Crystal Palace da Bayer Leverkusen da kuma AC Milan tun bayan da ya sanar da zai bar Bournemouth da zarar an kammala kakar nan, amma yanzu da alama shi ne babban zaɓin Liverpool, inda daraktan wasanni Richard Hughes—wanda ya taɓa nada shi a Bournemouth—ke da tasiri a yanke shawarar.
Ga bayan aikin kociyansa da lambobin girmamawa:
– Iraola ya bar Bournemouth bayan ta shafe wasa 19 ba tare da rashin nasara ba, kuma ya kai zuwa gasar Europa League, wanda shi ne karo na farko da suka taɓa samun tikitin Turai a tarihinsu.
– Bournemouth ta sha kashi sau bakwai kacal a gasar Premier League a kakar nan, inda ta kare a matsayi na shida. Arsenal da Manchester City ne kaɗai suke da ƙarancin rashin nasara a kansu, yayin da Liverpool ta sha kashi sau 12 duk da cewa ta kare a matsayi ɗaya sama da Bournemouth.
– A cikin shekara uku da ya jagoranta, ƙungiyar ta yi nasara a wasa 47 cikin 127 (kashi 37%), ta yi canjaras 40, ta kuma sha kashi 40. Ta zura ƙwallaye 196.
– Nasarar Bournemouth ta zo ne duk da yawan sayar da manyan ƴan wasa. A kakar da ta gabata, uku daga cikin ƴan baya huɗu sun tafi kafin fara kakar, inda ƙungiyar ta samu kusan £144.5m daga sayar da Milos Kerkez da Dean Huijsen da kuma Illia Zabarnyi.
– Antoine Semenyo shi ne wanda ya fi zura ƙwallaye a zamanin Iraola da 31 a raga a dukkan fafatawa.
– A baya, Iraola ya horar da AEK Larnaca inda ya lashe Cypriot Super Cup a 2018, Mirandés a Spain, da Rayo Vallecano inda ya taimaka musu zuwa LaLiga sannan suka kare a matsayi na 12 da na 11. A dukkan ƙungiyoyin da ya horar, yana da kashi 38.4% na nasara.
Asalin hoton, Getty Images
Iraq ta sanar da ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya, Gasar kofin duniya
Kocin Iraq, Graham Arnold, ya sanar ranar Litinin jerin ƴan wasa 26 da za su buga Kofin Duniya, inda ya dogara sosai da babban rukuni na ƴan wasan da suka taimaka wajen samun tikitin shiga gasar ta hanyar wasannin share fage a tsakanin nahiyoyi.
Ɗan wasan da ke buga gaba, Aymen Hussein ana sa ran zai jagoranci gurbin kai hare-hare a tawagar Iraq a wasannin da za ta buga a Arewacin Amurka. Wannan tsohon ɗan wasan, wanda ake kallonsa a matsayin gwarzo, shi ne zai jagoranci sahun gaba tare da Ali Al-Hamadi na Ipswich Town da kuma matasan ƴan wasa masu basira da ya haɗa da Ali Jassim da kuma Youssef Amyn.
Wani abin lura shi ne rashin sunan Dario Naamo daga cikin tawagar. An cire ɗan wasan Dundee, bayan da ya canza ƙasar da yake wakilta a wasannin ƙasa da ƙasa, bayan da ya taɓa bugawa Finland a matakin matasa.
Zaɓin ƴan wasan tsakiya na Arnold ya ƙunshi ƙwararru da suka saba da ƙwallon ƙafa a Turai, inda Zidane Iqbal na Utrecht da Aimar Sher na Heerenveen ke kan gaba a jerin.
Haka kuma, Arnold ya yanke shawarar barin mai tsaron raga, Kamil Saadi cikin tawagar atisaye a matsayin kariya idan aka samu rauni.
Iraq na komawa gasar Kofin Duniya a karon farko cikin shekaru 40, bayan ta doke Bolivia da ci 2-1 a watan Afrilu domin samun tikitin ƙarshe.
An saka su a Rukunin I tare da Faransa da Senegal da kuma Norway.
Masu tsare raga: Fahad Talib, Jalal Hassan, Ahmed Basil
Masu tsaren baya: Hussein Ali, Manaf Younis, Zaid Tahseen, Rebin Sulaka, Akam Hashem, Merchas Doski, Ahmed Yahya, Zaid Ismail, Frans Putros, Mustafa Saadoon
Masu buga tsakiya: Amir Al Ammari, Kevin Yakob, Zidane Iqbal, Aimar Sher, Ibrahim Bayesh, Ahmed Qasim, Youssef Amyn, Marko Farji Masu cin ƙwallaye: Ali Jassim, Ali Al Hamadi, Ali Yousef, Aymen Hussein, Mohanad Ali
Asalin hoton, Getty Images
, Daga Jaridu
Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya nuna aniyar dauko dan wasan Aston Villa da Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, a kokarinsa na ci gaba da samun nasarar lashe gasar Premier, duk da cewa Paris St-Germain da ta lashe gasar zakarun Turai ita ma na zawarcinsa. (Mirror), external
Manyan masu daukar ma'aikata a Real Madrid sun bukaci kungiyar ta nemi dan wasan Arsenal Declan Rice, sakamakon yadda dan wasan na Ingila mai shekaru 27 ya burge su kan jagoranci da kuma kwarewa.(Teamtalk), external
Golan Liverpool Alisson, mai shekara 33, yana shirin fada wa sabon kocin kungiyar cewa yana son ya bar Anfield ya koma Juventus. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external
Manchester United na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Brazil Ederson, mai shekara 26, daga Atalanta kan kudi kusan fan miliyan 35. (Talksport), external
Asalin hoton, Getty Images
Za a hana ƴan wasa zuwa wajen koci idan gola ya ji rauni a gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya
Za a hana ƴan wasa a gasar Kofin Duniya ta 2026 zuwa yankin masu horarwa, domin tattaunawa da koci a lokacin da mai tsaron raga ya ji rauni, kamar yadda shugaban alkalan FIFA, Pierluigi Collina, ya bayyana.
Haka kuma, Hukumar Dokokin Kwallon Kafa ta Duniya (IFAB) ta amince da bukatar sauya tsarin VAR, domin a ba da damar duba kura-kuran da suka shafi ketar da aka yi wa ƴan wasa.
Wannan tsarin da ake kira “goalkeeper tactical timeout” ya zama abin tattaunawa sosai a ƴan shekarun nan. Ana amfani da shi a wasu lokuta ne ta hanyar kociyoyi domin ba ƴan wasa sabbin umarni ko dabaru ko kuma rage karfin gwiwar abokan hamayya.
A watan Nuwamba, kocin Leeds United, Daniel Farke, ya zargi mai tsaron ragar Manchester City, Gianluigi Donnarumma, da yin kamar ya ji rauni domin “karkatar da dokoki” da kuma dakatar da wasa na ɗan lokaci.
A irin wannan yanayi, mai tsaron raga kan zauna a kasa ya nuna alamar neman a duba lafiyarsa, sauran ƴan wasa su tafi wajen koci domin samun sabon umarni, sannan da zarar an gama bayanin, mai tsaron ragar zai tashi ya ci gaba da wasa kamar yadda aka saba.
Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Wiliiams na jin raɗaɗin da kasarsa ba za ta buga gasar kofin duniya ba, Gasar kofin duniya
Neco Williams ya amince cewa rashin zuwa buga gasar cin Kofin Duniya ta bana har yanzu yana ci masa rai, domin ya yi imanin Wales za ta iya yin tasiri a gasar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Wales ta rasa damar zuwa gasar karo na biyu a jere bayan ta sha kashi a wasan neman cike gurbi a hannun Bosnia-Herzegovina.
Wannan rashin nasara ta fi taɓa zuciyar ɗan wasan baya na Nottingham Forest, Neco Williams, musamman ganin cewa shi ne ya kasa cin fenariti mai muhimmanci a karawar.
Sai dai duk da wannan ci gaba da takaici, ɗan wasan mai shekara 25 ɗin ya ce wasannin sada zumunta da Ghana da Romania a wannan mako su ne matakin farko na ci gaba da huce wannan raɗaɗi, yayin da tawagar ke mai da hankali kan gasar Euro 2028 da za a yi a gida.
Wasan da za su buga da Ghana a Cardiff ranar Talata zai zama abin tunawa da abin da suka rasa, domin Ghana na shirin shiga rukunin gasar World Cup ɗin da Ingila za ta kasance a ciki.