Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 04 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman Minjibir

  1. Zaftarewar ƙasa ta hallaka mutum 14 a yankin Amhara na Habasha

    Ana ci gaba da aikin ceto a yankin Amhara da ke arewacin ƙasar Habasha bayan wata zaftarewar ƙasa da ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ta kashe mutane 14 tare da jikkata wasu bakwai.

    Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya a wani wurin ibada na sufi, inda ɗaruruwan masu ibada suka taru domin wani biki na addini.

    Rahotanni sun ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka maƙale ƙarƙashin ɓaraguzan ƙasa ba, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da lalube domin gano waɗanda abin ya rutsa da su.

    Irin waɗannan zaftarewar ƙasa na ƙara yawaita a Habasha, musamman a lokacin damina da kan fara daga watan Yuni zuwa Satumba.

  2. Gasar Commonwealth: Tinubu ya jinjina wa Najeriya bayan samun lambobin yabo 24

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar Najeriya murnar bajintar da ta nuna a Gasar Commonwealth da aka gudanar a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, bayan da ta lashe jimillar lambobin yabo 24.

    Tawagar ta samu lambobin zinariya 10, azurfa 7 da tagulla 7, lamarin da ya sanya Najeriya cikin ƙasashen da suka yi fice a gasar.

    A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yaba wa 'yan wasan kan jajircewa, ƙwazo da kuma nuna ruhin kishin ƙasa da ya dace da sunan Najeriya a idon duniya.

    Shugaban ya ce nasarorin da suka samu sun nuna irin wahalar da suka sha wajen horaswa da kuma ƙudirin da suke da shi na yin zarra.

    Tinubu ya kuma yabawa shugabannin Kwamitin Olympics na Najeriya da Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa saboda ci gaba da tallafa wa 'yan wasa da bunƙasa harkokin wasanni a ƙasar.

    Ya ce ƙwarewar da 'yan wasan suka samu a gasar za ta taimaka musu wajen cimma manyan nasarori a wasu gasa na duniya da za su zo nan gaba.

    Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin wasanni, da inganta cibiyoyin horaswa tare da samar da ƙarin damar da za su ba matasan Najeriya damar haskakawa a matakan nahiya da na duniya.

  3. Babu wani rashin jituwa tsakanina da Mojtaba Khamenei - Shugaban Iran

    Shugaban Iran, Massoud Pezeshkian, ya ce babu wani saɓani ko rashin jituwa tsakaninsa da jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, yana mai musanta jita-jitar da ke cewa dangantakarsu ta yi tsami.

    Ya kuma jaddada cewa ba shi da niyyar yin murabus daga muƙaminsa.

    Pezeshkian ya ce: "Ba zan yi murabus ba, zan tsaya daram."

    Ya kara da cewa wasu na ƙoƙarin haddasa rikici a tsakanin shugabannin ƙasar ta hanyar yaɗa labaran da ke nuna cewa jagoran addinin ƙasar na faɗin wani abu, yayin da gwamnati ke faɗin wani abu daban.

    Tun bayan da Mojtaba Khamenei ya karɓi shugabancin Iran bayan rasuwar mahaifinsa sakamakon yaƙi, an riƙa samun rahotanni marasa tabbaci da ke hasashen cewa Pezeshkian na iya yin murabus daga muƙaminsa.

    A gefe guda kuma, ana ci gaba da samun saɓanin bayanai tsakanin Iran da Amurka kan batun tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.

    Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da cewa Amurka na tattaunawa da Iran, hukumomin Tehran suna musanta hakan, suna cewa babu wata tattaunawa da ake yi a halin yanzu.

  4. Dangantakar Iran da Iraq na cikin mafi kyawun yanayi - Araqchi

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, wanda ke ziyarar aiki a Iraq, ya bayyana cewa dangantakar ƙasashen Iran da Iraq tana cikin mafi kyawun yanayi a halin yanzu.

    A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iraq ranar Litinin, Araqchi ya ce ziyarar da Firaministan Iraq ya kai Tehran kwanan nan ta gudana cikin yanayi mai kyau, inda ɓangarorin biyu suka yi tattaunawa mai amfani da ma'ana.

    Ya ƙara da cewa Iran da Iraq suna da haɗin gwiwa ta kusa a fannoni daban-daban da suka haɗa da siyasa, tattalin arziki, tsaro da harkokin sufuri.

    Ministan ya kuma bayyana cewa a yayin ziyararsa a birnin Najaf, ya shaida yadda aka yi shirye-shirye da tsare-tsare masu yawa domin kula waɗanda za su halarci tattakin Arba'een.

    A lokaci guda kuma Araqchi ya isa Karbala domin halartar bukukuwan Arba'een, firaministan Iraki Ali Zaidi ma ya kai ziyara birnin.

  5. An yi zanga-zangar adawa da atisayen sojin Amurka da Koriya ta Kudu a Seoul

    Wasu masu fafutukar kare muradun al’umma a birnin Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu, sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Amurka ranar Talata 4 ga Agusta.

    Masu zanga-zangar, waɗanda ke cikin ƙungiyar "Korean Solidarity for Peace, Sovereignty and Reunification", sun buƙaci a dakatar da babban atisayen soji na shekara-shekara mai suna Ulchi Freedom Shield, wanda Koriya ta Kudu da Amurka ke yi domin ƙara karfafa hadin gwiwa da shirin ko-ta-kwana tsakanin sojojin kasashen biyu.

    Ana sa ran fara atisayen na bana cikin makwanni biyu masu zuwa, inda zai ɗauki tsawon kwanaki 10 ana gudanar da shi.

    Hukumomin da za su halarci atisayen sun haɗa da Rundunar Hadin Gwiwar Sojojin Koriya ta Kudu da Amurka, Rundunar Sojojin Amurka da ke Koriya ta Kudu, Rundunar Majalisar Dinkin Duniya, Babban Hafsan Sojojin Koriya ta Kudu da kuma wasu hukumomin gwamnati.

    Masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna adawa da atisayen ne saboda sun yi imanin cewa yana iya ƙara dagula yanayin tsaro da tashin hankali a yankin Gabashin Asiya.

  6. Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙudirin hana makarantu ƙara kuɗin makaranta barkatai

    Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da zai ƙayyade wa makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da izini da sahalewar hukuma ba, domin kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe barkatai.

    Ƙudirin gyaran dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026 ya tanadi cewa duk makarantar da ke son ƙara kuɗin makaranta dole ne ta fara neman amincewar hukumar da abin ya shafa.

    Rahotanni sun ce karin kuɗin da ya wuce kashi 10 cikin 100 zai buƙaci ƙarin nazari da sahalewa.

    Shugaban Majalisar, Ismail Falgore, ya ce dokar za ta taimaka wajen inganta tsarin gudanar da makarantu da kuma tabbatar da cewa ana kare muradun iyaye da ɗalibai.

    Haka kuma, dokar ta tanadi ƙirƙirar muƙamin Sakataren Zartarwa domin ƙara inganta gudanar da ayyukan hukumar.

    Majalisar ta amince da ƙudirin ne bayan zaman sauraron ra'ayoyin jama'a da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kwamitin ilimi na majalisar ya gudanar kafin gabatar da rahotonsa.

  7. Mun fasa kai wa Ukraine hari saboda ta nemi afuwa - Iran

    Iran ta ce ta shirya kai hari kan wurare uku a Ukraine bayan wani hari da aka kai wa jirgin kasuwancinta, amma daga baya ta dakatar da shirin bayan Ukraine ta nemi afuwa inda ta ce harin ba a yi shi da nufin tayar da rikici da Tehran ba.

    Babban mai ba wa jagoran Iran shawara kan harkokin soji, Mohsen Rezaei, ya ce bayan tattaunawar da aka yi tsakanin ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu, Ukraine ta bayyana cewa harin wani ɓangare ne na yaƙinta da Rasha, ba da niyyar kai wa ƙasar hari ba.

    Rezaei ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da makamai masu linzami da Iran ta kai kan sansanonin Amurka sun taimaka wajen daƙile duk wani shirin farmakin da Amurka za ta iya kai wa.

    Game da mashigar Hormuz kuwa, ya ce Iran ba za ta amince da buɗe wata hanyar jiragen ruwa da ba ta ƙarƙashin ikonta ba, yana mai gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin da ya bijirewa umarninta."

  8. Sojojin Najeriya 86 sun tafi aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

    Rundunar sojin Najeriya ta tura jami'ai 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin aikin wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar ECOWAS

    Rundunar ta ce wannan matakin na nuna ci gaba da jajircewar da Najeriya ke yi wajen tallafa wa zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka ta Yamma.

    A wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce jami'an da aka tura sun tashi daga filin jirgin saman ƙasar da ke Abuja kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya domin fara aikinsu ƙarƙashin umarnin ECOWAS.

    Rundunar ta kuma ce Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen Afirka da suka fi bayar da gudunmawa wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya na ECOWAS da Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Rundunar sojin Najeriya dai ta ce wannan sabon aikin ya nuna muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa wajen hana rikice-rikice, gina zaman lafiya da kuma dawo da kwanciyar hankali a ƙasashen Afirka.

    An dai kafa wannan rundunar ne domin tallafa wa ɓangaren tsaro da kuma inganta yanayin siyasa a Guinea-Bissau, bayan shekaru ana fama da rikice-rikicen siyasa da juyin mulkin soja.

    Najeriya dai ta daɗe tana cikin ƙasashen da suka fi tura sojoji zuwa ayyukan ECOWAS, inda ta bayar da dakaru, kayan aiki da jagoranci a ƙasashe irin su Liberiya, Saliyo, Gambiya da kuma Guinea-Bissau.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar da suka haɗa da hare-haren 'yanbindiga, satar mutane domin neman kuɗin fansa da dai sauransu.

  9. Iran ta ƙaryata iƙirarin cewa shugaban ƙasar Pezeshkian ya yi murabus

    Wani babban jami'i a ofishin Shugaban Iran ya bayyana rahotannin da ke cewa shugaban ƙasar, Massoud Pezeshkian ya yi murabus a matsayin “karya tsagwaronta.”

    Mehdi Tabatabaei, mataimakin daraktan sadarwa da yaɗa bayanai na ofishin shugaban ƙasar, ya ce wasu masu tsattsauran ra'ayi ne ke yaɗa ƙarya domin kawo cikas ga haɗin kan ƙasa.

    Tun da farko, wasu kalamai da malamin addini Mohammad Bagher Kharrazi ya yi sun bazu sosai a kafafen yaɗa labarai da sada zumunta a Iran.

    Kharrazi ya yi iƙirarin cewa Mojtaba Khamenei ya ce idan Pezeshkian ya sake miƙa takardar murabus, za a amince da ita.

    Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da wannan iƙirari, tana mai cewa ba shi da tushe balle makama.

  10. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.