Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni game da jana’izar Khamenei da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/07/2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed, Abdullahi Bello da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Amurka ta sake ƙaƙaba sabbin takunkumai kan Iran

    Amurka da Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ƙaƙaba sabbin takunkumai kan wasu mutane da kamfanoni masu alaƙa da Iran, bayan sabbin hare-haren da Tehran ta kai kan jiragen ruwa na kasuwanci a mashigin Hormuz.

    Kamar yadda Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar, daga cikin waɗanda takunkuman suka shafa har da Ali Ansari, wani ɗan kasuwa kuma ma'aikacin banki ɗan Iran da ke zaune a Dubai, wanda Birtaniya ta taɓa sanya wa takunkumi bisa zargin tallafa wa ayyukan dakarun juyin juya hali.

    Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ta bayyana Ansari a matsayin "babban mai samar da kuɗaɗe" ga sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, tana zarginsa da karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa manyan kadarori da kasuwanci a ƙasashen waje domin amfanar kansa da wasu jami'an gwamnati da kuma dakarun.

    Ofishin Kula da Kadarorin Ƙetare na Ma'aikatar a Amurka ya kuma sanya takunkumi kan wasu manyan cibiyoyin musayar kuɗi na Iran, inda ya zarge su da gudanar da mu'amalar biliyoyin daloli a madadin bankunan Iran da aka sanya wa takunkumi tare da amfani da kamfanonin bogi domin ɓoye haramtattun harkokin kuɗi na gwamnatin Iran.

    Waɗannan sabbin takunkuman na zuwa ne bayan da faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan tsagaita wuta na wani ɗan lokaci.

  2. Masar da Qatar sun roƙi Amurka da Iran su koma teburin sulhu

    Ministocin harkokin wajen Masar da Qatar sun buƙaci Amurka da Iran da su koma kan teburin tattaunawa domin daidaita rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Kiran nasu na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasarsa ta amince a ci gaba da tattaunawa da Tehran, duk da cewa ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin ta ƙare.

    A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, ta ce ministan harkokin wajen ƙasar, Badr Abdel Ati, da Firaminista kuma ministan harkokin wajen Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, sun tattauna ta wayar tarho, inda suka buƙaci dukkan ɓangarorin su fifita diflomasiyya da tattaunawa tare da komawa kan teburin sasanci.

    Sanarwar ta kuma ce ministan harkokin wajen Masar ya tattauna kan halin da yankin ke ciki da takwarorinsa na Kuwait, Bahrain da Jordan.

    A nata sanarwar, ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta ce Sheikh Mohammed ya jaddada muhimmancin dukkan ɓangarorin su ci gaba da bin hanyar lalama da diflomasiyya.

  3. Binciken BBC ya gano an kashe mutane daga ƙasashe sama da 40 yayin taya Rasha yaƙi da Ukraine

    Sojojin Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Wani bincike da Sashen Rashanci na BBC ya gudanar ya tabbatar da cewa mutane daga ƙasashe sama da 40 ne suka mutu yayin da suke taya Rasha a yaƙinta da Ukraine.

    Binciken ya nuna cewa waɗanda suka mutu sun haɗa da mutanen da aka ɗauko daga gidajen yarin Rasha, da waɗanda suka shiga aikin soja da son ransu, da kuma wasu da aka yaudara ko aka tilasta musu shiga yaƙin.

    Binciken ya tabbatar da mutuwar fiye da ƴan ƙasashen waje 3,500, sai dai BBC ta ce akwai yiwuwar adadin ya fi haka sosai.

    Rahoton ya ƙara da cewa kusan kashi biyu bisa uku na waɗanda aka tabbatar sun mutu ƴan Koriya ta Arewa ne.

    Sauran kuwa sun fito ne daga ƙasashe daban-daban a nahiyoyin Afirka, Latin Amurka, Asiya da kuma Amurka.

  4. Tinubu ya sake ɗaukar Shettima a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2027

    Tinubu ya sake zaɓen Kashin Shettima

    Asalin hoton, APC/X

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake zaɓen mataimakinsa na yanzu, Kashim Shettima, domin su sake tsayawa takara tare a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

    Jam’iyyar APC ce ta tabbatar da hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafin X, inda ta karɓi fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasar a zaɓen mai zuwa.

    Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya karɓi takardun da aka cike wa shugabannin a wani taro da aka gudanar a Abuja.

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Masari ne ya miƙa takardun a madadin Shugaba Tinubu.

    APC ta bayyana cewa a yanzu za a miƙa takardun takarar zuwa hukumar zaɓe ta INEC domin kammala sauran matakan rajistar takara.

    A baya dai an yi ta yaɗa raɗe-raɗin cewa wataƙila Tinubu ya ajiye Shettima ya ɗauki wani mutum daban daga arewacin ƙasar saboda cece-ku-cen da ake yi game da tikitin takarar Musulmi da Musulmi.

  5. An saki ɗalibai da malaman makaranta da aka sace a Oyo

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/X

    Fadar shugaban Najeriya ta sanar da cewa an saki duka ɗalibai da malaman makaranta da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Orire ta jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin ƙasar.

    Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a yau Juma'a.

    A wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya ce an saki duka mutanen daga daga hannun masu garkuwa da su, tare da wallafa hotunansu.

    “Daga ƙarshe, jami'an tsaron mu sun ceto duka ɗalibai da malaman makaranta da aka yi garkuwa da su a Orire, jihar Oyo," in ji Onanuga.

    Ya kuma wallafa wani gajeren bidiyon malamar da ke tare da su tana jawabi da jin daɗi. Sai dai ba a yi cikakken bayani kan yadda aka kuɓutar da su ba.

    A wani hari da ƴan bindiga suka kai kan makarantu a Jihar Oyo ranar 15 ga Mayu, 2026, aka sace mutum 46 da suka haɗa da dalibai 39 da malamai 7.

    A jihar Borno ma an kai makamancin wannan hari, inda aka yi awon gaba da ɗalibai sama da 40 su ma, amma har yanzu babu labarin sakinsu.

  6. Wata tawaga ta tafi Iran don neman mafita kan yaƙin da ya barke

    Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, TASNIM

    Bayanan hoto, Jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei

    Wata tawaga daga Qatar ta tafi Iran a yunƙuri na baya-bayan nan wajen ceto yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Iran ɗin da Amurka, wadda ke barazanar wargajewa bayan sake rincaɓewar yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.

    Wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Fox News cewa har yanzu Amurka a shirye take a samu mafita game da rikicin kuma ana tattaunawa ta wasu fannonin.

    A tsokacin da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta amince da wata buƙata daga Iran ta ci gaba da tattaunawa, sai dai ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe.

    Yaƙin da ya sake ɓarkewa tsakanin ƙasashen biyu na faruwa ne a Mashigar Hormuz, hanyar ruwa da ake taƙaddama a kanta.

  7. Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin naira triliyan 1.854

    Fubara

    Asalin hoton, X/@SimFubara

    Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1.854 ga majalisar dokokin jihar, wanda shi ne karo na farko da ya bayyana a gaban majalisar a ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule tun bayan rikicin siyasa da ya raba majalisar a shekarar 2023.

    Da yake gabatar da kasafin, Gwamna Fubara ya ce an tsara shi ne domin ci gaba da bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa ayyukan more rayuwa da inganta zuba jari a jihar.

    Kasafin kuɗin na bana ya kai naira tiriliyan 1.854, wanda ke nuna ƙarin kashi 24.49 cikin ɗari idan aka kwatanta da kasafin kuɗin shekarar 2025, wanda aka yi wa gyara kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

  8. Wanda zai zama Firaministan Birtaniya ya nemi afuwa kan martanin jam'iyyarsa game da Gaza

    Birtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutumin da ake ganin zai iya zama Firaministan Birtaniya na gaba, Andy burnham, ya nemi afuwa kan martanin farko da jam'iyyarsa ta Labour mai mulki ta mayar kan matakan da Isra'ila ta ɗauka a zirin Gaza.

    A wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Burnam din ya ce jam'iyyarsa ta yi kuskure a yadda ta fara tunkarar lamarin.

    A farkon makonnin rikicin, Firaminista Keir Starmer ya fuskanci suka, bayan ya bayyana cewa Isra'ila na da ‘haƙƙin’ katse samar da ruwa da makamashi ga Gaza.

    Kodayake daga baya ya ce abin da yake nufi shi ne Isra'ila na da haƙƙin kare kanta.

    Andy Burnam ya ce idan ya zama shugaban gwamnati, matakin Birtaniya game da rikicin zai kasance mai tsauri fiye da na yanzu.

  9. Tarukan addini 5 mafiya girma a duniya

    Hindu

    Asalin hoton, Getty Images

    Addinai da al'adu a faɗin duniya na gudanar da taruka daban-daban, inda miliyoyin mabiya addini ko wata mazhaba ko kuma wata al'ada ke haɗuwa a wuri guda domin bikin.

    Mafiya lokuta ana irin waɗannan tarukan ne shekara-shekara wani abu da ke bai wa masu son halartar taron yin tanadi walau dai na kuɗin tafiya ko guzuri.

    A yanzu haka akwai taruka manya guda biyar da suka fi kowanne samun taron jama'a a duniya inda kuma uku daga cikinsu na mabiya addinin Musulunci ne sai kuma guda biyu na mabiya addinin Hindu da Yahudanci.

  10. Muhammad ya sake zama sunan da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales

    Jarirai

    Asalin hoton, Getty Images

    Sunan Muhammad ya sake zama sunan da mahaifa suka fi saka wa ƴaƴansu maza a Ingila da Wales a shekarar 2025.

    Hukumar ƙididdiga ta Ingila ce ta sanar da hakan a wani rahoto da ta fitar ranar Alhamis dangane da sunayen da aka fi sanya wa yara a shekarar da ta gabata.

    Wannan dai shi ne karo na uku a jere da sunan na Muhamamd ke zama wanda aka fi sanya wa yara a Ingila da Wales - sunan ne ja-gaba a shekarun 2023 da 2024 da kuma 2025.

  11. Nicaragua ta soke lasisin lauyoyi 2,000

    Lauya

    Asalin hoton, Bloomberg Creative/ Getty Images

    Hukumomi a Nicaragua sun soke lasisin lauyoyi 2,000 ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba.

    Kafafen yaɗa labarai na Nicaragua sun ruwaito cewa an cire sunayen lauyoyin daga rajistar Kotun Koli, matakin da ya hana su ci gaba da gudanar da aikinsu na lauya.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wannan mataki zai rufe hanya ta ƙarshe da ta rage ga mutanen da ke neman kariyar shari'a daga gwamnatin da ake zargi da mulkin kama-karya ƙarƙashin Daniel Ortega da matarsa, Rosario Murillo.

    Ma'auratan sun shafe kusan shekara 20 suna mulkin Nicaragua da cikakken iko, tare da riƙe madafun iko

  12. Gobarar daji ta yi ajalin aƙalla mutum 12 a Spain

    Spain

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a kudancin Sifaniya sun ce aƙalla mutum 12 ne suka mutu sakamakon wata gobarar daji a lardin Almería.

    An samu gawar wasu daga cikin waɗanda suka mutu ne a cikin motoci da wutar ta rutsa da su.

    Wakilin BBC ya ce Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne bayan wani layin wutar lantarki ya faɗi, lamarin da yasa wutar ta bazu cikin sauri zuwa wani yanki mai cike da bishiyoyi .

    Matsanancin zafi mai maki digiri 40 na ma'aunin Celsius da ake ci gaba da samu, ya haddasa gobarar daji a sassa daban-daban na kudancin Turai.

  13. Me ya sa aka jinkirta jana'izar Khamenei duk da tanadin Musulunci na gaggauta binne mamaci?

    HAMSHAHRI

    Asalin hoton, HAMSHAHRI

    Tun ranar Juma'ar makon da ya gabata ne aka fara gudanar da tarukan jana'izar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, har zuwa ranar Alhamis, inda za a binne shi a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.

    An ajiye akwatunan gawar Khamenei da wasu mutum huɗu daga cikin iyalansa a wani wuri na musamman a Tehran a safiyar Asabar 4 ga Yulin 2026. An lulluɓe akwatunan da tutar Iran, inda aka sanya su cikin gilashi kuma makarar sun fi yadda aka saba yi tsawo.

    Mahukuntan Iran sun ce ba don dalilan tsaro kaɗai aka sanya gawarwakin cikin gilashin ba, har ma domin amfani da tsarin sanyaya yanayi da zai taimaka wajen kiyaye su.

  14. Sojojin Najeriya sun kama ƴar Chadi bisa zargin kai wa Boko Haram giya da ƙwayoyi

    Soja

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na sashi na 3 na rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabas sun samu nasara kama wata ƴar ƙasar waje da uke zargi da kai wa mayaƙan Boko Haram ƙwayoyi da giya.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun sojojin Mohammed Goni ya fitar, ya ce sun yi amfani ne da bayanan sirri wajen bibiyarta, inda a ranar Alhamis 9 ga Yuli suka kamata ɗauke da tarin miyagun ƙwayoyi da giya da sauran haramtattun kayayyaki da ake kyautata zaton za ta kai wa ƴan Boko Haram ne.

    "An kama wadda ake zargin, Misis Rachael Samuel mai shekara 48, wadda ƴar garin Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi na Jamhuriyar Chadi ce. Binciken farko ya nuna cewa tana kai kayan ne zuwa wurare da ke cikin tsibiran Tafkin Chadi, inda aka san zama mafakar 'yan ta'adda ne."

    Daga cikin ƙwayoyin da sauran kayayyakin da aka kama matar da su akwai buhu bakwai na tabar wiwi da giya da sauransu.

  15. Da gaske an daina karɓar takardar naira 100 a Najeriya?

    Naira

    Asalin hoton, CBN

    A baya-bayan nan ƴan Najeriya sun shiga ruɗani game da sahihancin takardar kuɗi ta naira 100.

    Rahotonni daga wasu yankunan ƙasar sun nuna cewa wasu a ƙasar sun daina karɓar tsohuwar takardar kuɗi ta naira 100.

    Najeriya na amfani da nau'uka biyu na takardar kuɗi ta naira 100, waɗanda duk hukumomin sun amince da su.

    Tun asali akwai takardar naira 100 da ake amfani da ita, sai dai a shekara ta 2014 babban bankin Najeriya ya fitar da wata sabuwar takardar naira 100 wadda aka yi wa sauye-sauye, a wani ɓangare na murnar cikar ƙasar shekara 100 da samuwa.

  16. Yadda aka binne tsohon jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Kafafen yaɗa labaran gwamnati a Iran sun ce an binne jagoran addini na ƙasar da aka kashe, Ayatollah Ali Khamenei, a hubbaren Imam Reza da ke Mashhad, wuri mafi tsarki a Iran, bayan taron jana'iza da ya jawo dubban mutane.

    An gudanar da jana'izar a Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran bayan mako guda na jerin gwanon jana'iza da tarukan alhini da kuma zaman makoki, a daidai lokacin da rikici ya sake ɓarkewa tsakanin Iran da Amurka bayan wani lokaci na tsagaita wuta a yaƙin da ya shafe wata huɗu ana yi.

  17. Amurka za ta tattauna da ministocin ƙasashe 60 kan masu tsattsauran ra'ayi

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya gayyaci ministoci daga ƙasashe sama da 60 zuwa wani taron koli da za a yi a birnin Washington, a mako mai zuwa domin tattauna abin da ma’aikatarsa ta kira ‘sake farfadowar masu tsattsauran ra'ayin kawo sauyi na kasa da kasa ’.

    Ana dai sa ran taron zai haɗa ministoci da manyan jami’ai daga yankuna daban-daban na duniya, ciki har da turai da Asiya.

    Sai dai kafafen yaɗa labarai na Amurka sun bayar da rahoton cewa abu ne mai wuya a sami shugabannin turai masu yawa a taron, saboda ba sa kallon masu matsanancin ra'ayi kawo sauyi a fagen siyasa a matsayin babbar barazana

    Masu sukar wannan mataki dai na cewa Amurka na zuzuta girman barazanar da ake dangantawa da masu matsananincin ra'ayin kawo sauyi.

  18. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai kan jana'izar Ali Khamenei da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.