KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 12 zuwa Juma'a 18 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. ATLETICO ta kai bantenta, Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2)

    Lafari ya hura usur na ƙarshe a wannan wasa.

    Atletico Madrid ta kai matakin kusa da ƙarshe na gasar Champions League karo na farko a cikin shekara 9.

  2. AN TASHI WASAN Liverpool

    Shi ke nan an yi wajerod da Liverpool bayan muzanta su da PSG ta yi.

    An ci su gida da waje.

    PSG ce ta taka bal sosai fiye da Liverpool a dukanin falle biyu na karawar, ba ma za a kwatanta ba.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Liverpool 0-2 PSG (Jimilla 0-4)

    An ci gaba da wasa amma magoya bayan Liverpool da yawa sun fita daga fili saboda takaici.

  4. ƘWALLO A RAGA: Liverpool 0-2 PSG

    A cikin ƙarin lokaci an ƙara wa Liverpool.

  5. An ƙara minti 6 a wasan Liverpool, Liverpool 0-1 PSG (Jimilla 0-3)

  6. Ƙarin lokaci, Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2)

    An ƙara minti takwas!

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  7. PSG na zamani, Liverpool 0-1 PSG (Jimilla 0-3)

    Liverpool ta gaza yin komai.

    Duk da cewa PSG ta ɓaras da wasu damarmaki amma tana wasa yadda ya kamata.

    Abin akwai ƙayatarwa!

  8. Saura minti 5, Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2)

    Saura minti biyar a tashi wasa duk da dai za a ƙara wasu mintuna a ƙarshe.

  9. KATIN KORA - Eric Garcia, Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2)

    An ba ɗan wasan Barcelona Eric Garcia katin kora kai-tsaye, yanzu Barca za ta ci gaba da wasa da mutum 10.

  10. AN BAI WA BARCELONA JAN KATi, Atletico Madrid 1-2 Barcelona

    An bai wa Eric Garcia jan kati, kenan Barcelona za ta koma karawar da ƴan wasa 10 - a wasan farko ma an ba ta jan kati.

  11. ƘWALLO A RAGA! PSG ta ci ƙwallo a Anfield, Liverpool 0-1 PSG (Jimilla 0-3)

    Ousmane Dembélé (Paris Saint Germain) ya buga ƙwallo da kafar hagu ta faɗa raga, bayan samun tamaula daga Khvicha Kvaratskhelia.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  12. ƘIRIS! Gola ya ceci Barca!

    Joan Garcia ya taimaki Barca ta hanyar kaɗe ƙwallo daga ƙafar Robin Le Normand.

    In da an zura wannan ƙwallon da shi ke nan wasa ya ƙare!

  13. HAR YANZU BA CI A WASAN LIVERPOOL DA PSG, Liverpool 0-0 PSG

    Tuni aka koma zagaye na biyu a Champions League tsakanin Liverpool da Paris St Germain a Anfield.

    A wasan farko an doke ƙungiyar Anfield 2-0 a Faransa, yayin da PSG mai riƙe da kofin bara ke fatan kai wa daf da karshe a gidan Liverpool

    Liverpool na fatan yin abin kirki bayan da take ta biyar a teburin Premier League ba ta samu lashe Carabao Cup an fitar da ita FA Cup, kenan za ta kare a kakar nan ba tare da ɗaukar kofi ba.

    Liverpool ce ke rike da kofin Premier League da ta lashe a bara a kakar farko karkashin koci, Arne Slot.

  14. BARCELONA TA CI ƘWALLO, Atletico Madrid 1 - 2 Barcelona

    Barcelona ta kara ƙwallo na uku a ragar Atletico, yanzu kowacce tana da uku-uku a raga.

    Sai dai ana duba ko an yi satar gida kan ƙwallon ya faɗa raga a VAR,

    Ta tabbata da satar gida an soke ƙwallon, sakamakon ya koma Atletico Madrid 1 - 2 Barcelona 2

  15. HUTUN RABIN LOKACI

    An tashi hutun rabin lokaci a Anfield!

    Har yanzu Liverpool na sa rai, amma sai idan za ta iya farke ƙwallo biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

  16. KATIN GARGAƊI, Liverpool 0-0 PSG (Jimilla 0-2)

    Ruwan sama da ake yi ya sa fili yana da santsi, kuma an bai wa Alexis Mac Allister katin gargaɗi bayan ya yi sulu ya kwashe ɗan wasan PSG.

  17. HUTUN RABIN LOKACI, Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2)

    An tafi hutun rabin lokaci a wasan Atletico da Barca

  18. , Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2)

    Duk ƙungiyar da ta yi nasara a wannan wasa tsakanin Atletico Madrid da Barcelona za ta kara ne da wanda ya yi nasara tsakanin Arsenal da Sporting a wasan yammacin Laraba.

  19. CANJIN ƊAN WASA, Liverpool 0-0 PSG (Jimilla 0-2)

    PSG ta yi canji bisa tilas.

    Nuno Mendes ne ya kwanta a cikin fili, yanzu an sauya shi da Lucas Hernandez.

  20. ƘWALLO A RAGA: Atletico Madrid 1-2 Barcelona (Jimilla 3-2), Ademola Lookman (Minti na 31)

    Ana taka ƙwallo yau!

    Diego Simeone ya ce wa ƴan kallo su kwantar da hankalinsu, sai kuwa ga shi Ademola Lookman ya zura wata ƙayatacciyar ƙwallo.

    Ademola Lookman

    Asalin hoton, Getty Images