Dalilan da suka sa na nace kan zaɓen Muslim-Muslim - Sheikh Jingir
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ya yi tsammanin zai sha suka lokacin da ya yi wasu kalamai game da takarar Muslim-Muslim.
Jingir ya kuma ce ba ya da na sanin matsayarsa.
Taliban ta hana yara mata sama da miliyan biyu samun ilimin sakandare
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin yara mata miliyan biyu da dubu dari hudu ne a Afghanistan aka hana su samun ilimin sakandare tun bayan dawowar Taliban kan mulki shekaru biyar da suka gabata, tare da yin kira da a kawo ƙarshen irin wannan wariya nan take.
Tun daga watan Agustan shekarar 2021, gwamnatin Taliban ta ƙaƙaba wasu jerin takunkumai kan mata, inda ta hana su samun ilimi da kuma yin aiki a mafi yawan ma'aikatun gwamnati da sauran wurare a ƙasar.
Hukumar kula da ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD (UNESCO) ta ce 'yan mata da mata na Afghanistan suna da haƙƙin samun ilimi da 'yancin yin aiki kamar sauran takwarorinsu maza.
Taliban na kare wannan manufa da tace ta yi daidai da tsarin addinin Musulunci.
Girgizar ƙasar Colombia ta kashe sama da mutum 200
Asalin hoton, Getty Images
Fiye da mutum 200 ne suka mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta afku a Colombia ranar Litinin, yayin da kusan mutum 200 har yanzu ba a san inda suke ba.
Ana ci gaba da gudanar da aikin neman waɗanda suka tsira a ciki da kewaye biranen Cali da Pereira da ke yammacin ƙasar, waɗanda suka kasance cikin wuraren da girgizar ta fi shafa.
Kimanin gidaje 5,000 sun lalace, yayin da gine-ginen bene masu yawa da dama suka koma kufai.
An kuma rufe filayen jiragen sama shida na yankuna daban-daban, yayin da hanyoyi da dama suka lalace, baya ga tangardar da ake samu wajen samar da wutar lantarki da ruwan sha.
Rundunar ƴansanda ta tabbatar da kashe jami'anta 10 a artabu da ƴanbindiga a Kebbi
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami'anta 10 a wani artabu da ƴanbindiga a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Litinin 10 ga watan Agusta, a yankin Rafin Makuku da ke ƙaramar hukumar Sakaba.
A sanarwar da kakakin rundunar na ƙasa CSP Ani Iniedu ya fitar, ya ce jami'anta sun tare ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai ne yayin da suke ƙoƙarin wucewa daga jihar Zamfara zuwa Kebbi, inda suka yi musayar wuta.
Rundunar ta ce an kashe aƙalla ƴanbindiga 17 tare da lalata babura huɗu na maharan.
Sai dai jami'an ƴansanda 10 sun rasa rayukansu a artabun, yayin da wasu biyu suka samu raunuka inda a yanzu suke samun kulawa.
Rundunar ta kuma ce wasu fararen hula biyu sun mutu a yayin musayar wutar.
Sojojin Najeriya sun ce sun daƙile shirin kwanton ɓaunar ƴanbindiga a Filato
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na rundunar Operation ENDURING PEACE da ke aiki a Jihar Filato sun samu nasarar daƙile wani kwanton ɓauna da ake zargin ’yan bindiga ne suka shirya a ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa, yayin wani samame da suka kai bisa bayanan sirri.
Sanarar da rundunar ta fitar ta ce sojojin sun gudanar da aikin ne bayan da aka kama wani da ake zargi dan bindiga ne, wanda ya bayyana wa jami’an tsaro inda ya ɓoye makaminsa a ƙauyen Nwur.
Yayin da dakarun suka tasa ƙeyar wanda ake zargin zuwa wurin domin gano makamin, wasu daga cikin abokan aikinsa suk kai musu hari.
Sai dai sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa da karfin wuta, lamarin da ya yi sanadin kashe daya daga cikin maharan.
Wanda aka kama tun farko shi ma ya mutu a yayin musayar wutar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu.
Bayan kammala artabun, sojojin sun binciki yankin inda suka ƙwato makamai, harsasai da sauran kayan da maharan suka bari yayin tserewa.
Rundunar ta ce tana ci gaba da sintirin neman sauran masu aikata lafin tare da jaddada ƙudurinta na hana masu aikata laifuka samun mafaka da kuma kare rayuka da dukiyoyin
An yanke wa tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad hukuncin kisa
Wata kotu a Syria ta yanke wa hambararren shugaban kasar Bashar al-Assad hukuncin kisa ba tare da ya bayyana a gaban kotu ba, bayan ta same shi da laifin aikata laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a lokacin yaƙin basasar ƙasar.
Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa Assad, wanda ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa bayan an hamɓarar da gwamnatinsa a watan Disamban 2024, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkin da iyalansa suka yi tsawon shekaru biyar.
Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Najeriya ta buƙaci a kama Sheikh Jingir
Asalin hoton, KNSG
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Najeriya ta yi Allah wadai da kalaman da malamin addini Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi, inda da ta ce za su rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna a tsakanain addinai.
Hukumar ta buƙaci Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, Hukumar DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa su kama tare da gurfanar da Sheikh Jingir kan zargin furta kalaman ƙiyayya da tunzura jama'a.
Shugaban hukumar, Tony Ojukwu a wata sanarwa, ya ce kalaman malamin, waɗanda suka yaɗu a wani bidiyo, suna yin kira ga siyasar wariya ga wasu addinai da kuma amfani da kalmar “kafirai”.
Ya ce hakan ya saɓa wa ƙa'idojin daidaito da zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya, kuma hakan na iya haddasa tashin hankula.
Hukumar ta kuma yi kira ga malamai, sarakuna da 'yan siyasa da su guji kalaman rarrabuwar kawuna, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen zaɓen 2027.
Davido ya rubuta wa Trump wasiƙa kan zaɓen jihar Osun
Asalin hoton, Getty Images
Shahararren mawaƙin Najeriya, Davido ya rubuta wa shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin jawo hankalinsa kan halin siyasar da ake ciki a jihar Osun.
Ya rubuta wasiƙar ne a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar a ranar Asabar inda ya buƙaci shugaban na Amurka ya sanya ido sosai kan zaɓen da za a gudanar.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Davido ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar tashin hankali da wasu yiwuwar kawo cikas ga zaɓen cikin lumana da adalci.
"Mutanen Osun suna da ƴancinsu da na ƙundin tsarin mulki ya basu na kaɗa ƙuri'a, cikin lumana kuma ba tare da tsoro ba," in ji shi.
Mawaƙin ya kuma yi kira ga Amurka da ƙasashen duniya da su mai da hankali kan zaɓen, yana mai cewa, "Ba ma son a zubar da jini. Ba ma son tsoratar da jama'a. Abin da muke so shi ne zaman lafiya, gaskiya da kuma sahihin zaɓe."
An soke tashin jirgin sama saboda wani ƙaramin yaro da ya ƙi zaunawa
Asalin hoton, Getty Images
An soke tashin wani jirgin saman ƙasar Canada bayan wani ƙaramin yaro ya ƙi zama a kujerarsa tare da ɗaure bel a lokacin da za a tashi.
Jirgin na kamfanin Porter Airlines na kan titin da zai tashi a filin jirgin sama na Victoria International Airport da ke British Columbia, lokacin da ma'aikatan jirgin suka lura cewa yaron ya ƙi zama a kujerarsa.
Kamfanin jirgin ya ce iyayen yaron da ma'aikatan jirgin sun yi ta ƙoƙarin ganin an zaunar da yaro amma abin ya ci tura, inda daga bisani jirgin ya koma domin a sauke yaron da iyayensa tare da kayansu.
Saboda wannan jinkiri, jirgin ya fasa tashi saboda an rufe titin tashin jiragen saman da ƙarfe 12:30 na dare.
Hakan ya sa fasinjojin da ke cikin jirgin mai ɗaukar mutum 132, suka kwana a filin jirgin, maimakon su isa birnin Toronto. Ba a bayyana shekarun yaron ba, ko kuma adadin fasinjojin da ke cikin jirgin a lokacin.
Kamfanin ya nemi afuwar fasinjojin bisa abin da ya faru, tare da tabbatar da cewa an sake shirya musu wani jirgin da ya tashi washegari.
Dokokin jiragen sama na buƙatar fasinjoji su zauna a kujerunsu kuma su ɗaure bel musamman a lokacin tashin jirgi da saukarsa.
Ministan harkokin cikin gidan Pakistan ya tafi Tehran domin ganawa da jami’an Iran
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ruwaito cewa ministan harkokin cikin gidan Pakistan, Mohsen Naqvi, ya bar ƙasarsa zuwa Tehran domin ganawa da jami’an Iran.
Pakistan ce ke taka rawa a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar da ke tsakanin Iran da Amurka, kuma jami’ai daga Tehran da Islamabad na yawan gudanar da ganawa a kai a kai.
A watan da ya gabata, ministan harkokin cikin gidan Iran, Eskandar Momeni, ya kai ziyara Pakistan.
Haka kuma Pakistan ta gayyaci wasu manyan jami’an Iran, ciki har da ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Araqchi, su ziyarci ƙasar, sai dai har yanzu ba a bayyana ranar da za a kai ziyarar ba.
Isra'ila ta kai hari kan motar asibiti a kudancin Lebanon
Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta zargi Isra'ila da kai hari kan wata motar daukar marasa lafiya a kudancin kasar, lamarin da ya jikkata mutum biyu tare da lalata motar asibitin.
A cewar ma'aikatar, ma'aikatan ceto sun isa wurin da aka kai wa motar hari a birnin Nabatieh ne kafin wani hari na biyu ya afka musu, wanda ya lalata motar ɗaukar marasa lafiyar.
Ma'aikatar ta yi allawadai da ci gaba da kai hari kan ma'aikatan agaji, tana mai cewa hakan ya saɓa wa dokokin jin kai na ƙasashen duniya
Haka kuma Hukumar Kare Fararen Hula ta Lebanon ta ce wani jirgi mara matuƙi na Isra'ila ya kai hari kan jami'anta yayin da suke ƙoƙarin kashe gobarar daji a yankin Nabatieh, lamarin da ya tilasta musu ficewa daga wurin duk da cewa ba a samu wanda ya jikkata ba.
Wannan hari na baya-bayan nan na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakanin Isra'ila da Lebanon.
Shugaban Chadi Mahamat Deby zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Deby, ya sanar da cewa zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa a matsayin wani mataki na samar da haɗin kai, yafiya da sulhu a ƙasar.
Ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kan Chadi, inda ya buƙaci 'yan ƙasa su guje wa rarrabuwar kawuna tare da fifita muradun ƙasa.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kira a saki tsohon firaministan ƙasar kuma jagoran ƴan adawa, Succès Masra, wanda ke zaman hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan an same shi da laifukan da suka haɗa da tayar da ƙiyayya da hannu a kisan kai, zarge-zargen da ya musanta.
Wasu 'yan ƙasar na fatan cewa afuwar da shugaban zai yi za ta haɗa da Succès Masra da kuma wasu jagororin adawa takwas da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru takwas bayan shirya zanga-zangar da gwamnati ta haramta.
Har yanzu shugaban bai bayyana sunayen waɗanda za su amfana da afuwar ba ko kuma ranar da za a sake su.
Amurka na siyasantar da saka mana takunkumi - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Iran ta zargi Amurka da siyasantar da saka mata takunkumi tana mai cewa Washington ta fi mayar da hankali kan ƙaƙaba wa Tehran takunkumi maimakon amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen warware saɓanin da ke tsakaninsu.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Amurka ta maye gurbin siyasa da tunani na hankali da abin da ya kira "ƙaƙaba mata taƙunkumi", yayin da yake mayar da martani ga kalaman Sakataren Baitulmalin Amurka.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya ce Baghaei ya yi waɗannan kalamai ne bayan wani jami'in Amurka ya yi magana kan ci gaba da matsa wa Iran lamba ta hanyar saka mata takunkumin tattalin arziki.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Baghaei ya ce duk lokacin da Amurka ta kasa ciyar da manufofinta gaba ta hanyar diflomasiyya, sai ta koma amfani da takunkumi.
Ya ƙara da cewa idan takunkumin bai samar da sakamakon da Amurka ke nema ba, maimakon sake duba dabarunta, sai ta ƙara tsaurara takunkumin.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da taƙaddama tsakanin Tehran da Washington kan batutuwa da suka haɗa da shirye-shiryen nukiliyar Iran da kuma takunkuman da Amurka ke ƙaƙaba wa ƙasar.
An buƙaci ƙungiyoyin ma’aikatan jiragen sama su dakatar da yajin aiki
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta yi kira ga ƙungiyoyin ma’aikata da su dakatar da yajin aikin da ya haddasa soke tashin jirage a filayen jiragen saman Legas da Abuja.
Yajin aikin da ƙungiyoyin NLC, ATSSSAN da TUC suka fara ya samo asali ne daga rikici kan batun haɗa ma’aikata cikin ƙungiyoyi da kuma biyan wasu kuɗaɗen doka ga hukumar kula da sufurin jiragen sama.
NCAA ta ce ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, na ƙoƙarin warware matsalar, kuma ta buƙaci ɓangarorin su rungumi tattaunawa domin a dawo da zirga-zirgar jirage yadda aka saba.
A sakamakon rikicin, kamfanonin United Nigeria Airlines da Air Peace sun dakatar da wasu ayyukansu na zirga-zirga, lamarin da ya jefa fasinjoji da dama cikin mawuyacin hali a filayen jiragen saman Abuja da Legas.
Duk da haka, NCAA ta tabbatar da cewa matakan tsaron jiragen sama ba su fuskanci wata barazana ba.
Ganawar Pezeshkian da Mojtaba Khamenei ta tabbatar da haɗin kan Iran – Gwamnati
Asalin hoton, Getty Images
Kakakin gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta ce ganawar da shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian, ya yi da Mojtaba Khamenei wata alama ce ta ci gaba da goyon bayan da jagoran ƙasar ke bai wa gwamnati.
Mohajerani ta bayyana cewa taron ba wai martani ne kawai ga jita-jitar da aka yaɗa ba, illa wata shaida ce ta dangantakar da ta ginu kan amincewa, haɗin kai da goyon baya.
Ta yi nuni da jita-jitar da aka yaɗa game da yiwuwar murabus ɗin shugaban ƙasar da kuma martanin Mojtaba Khamenei, waɗanda daga baya Pezeshkian da kuma jagoran Iran suka musanta, suna masu kiran su ƙarya da jita-jita.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka bayyana cewa shugaban ƙasar ya yi wata ganawa ta tsawon sa’o’i bakwai da jagoran Iran, yayin da wasu ɓangarorin siyasar ƙasar ke sukar yadda gwamnatin Pezeshkian ta tafiyar da yaƙi da kuma tattaunawar diflomasiyya.
Mohajerani ta kuma ce jagoran addinin ƙasar ya sha bayyana goyon bayansa ga shugaban ƙasa da gwamnati a lokuta daban-daban.
Ta ƙara da cewa ya kamata a bambanta tsakanin suka masu amfani da kuma matakan da ke haifar da rashin amincewa da ƙara rarrabuwar kawuna a siyasar ƙasar.
Trump ya sauya jirgi akan hanyarsa daga Turkiyya saboda tsoron harin Iran
Asalin hoton, Reuters
Rahotanni sun ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya sauya jirgi a kan hanyarsa ta dawowa daga Turkiyya bayan halartar taron ƙasashen NATO, saboda tsoron hari daga Iran.
A cewar jaridar Washington Post, mutane da dama ciki har da wasu ‘yan jarida da ma’aikatan Fadar White House sun yi tunanin cewa Trump yana cikin jirgin shugaban ƙasa, Air Force One, wanda ya hau a gaban kyamarorin talabijin a Ankara.
Sai dai rahoton ya ce jim kaɗan bayan ya shiga jirgin, an sauya shi a ɓoye zuwa wani ƙaramin jirgin saman soja mai suna C32A ta hanyar amfani da motar da ake kai abinci jiragen sama, kafin a tafi da shi zuwa sansanin sojin Amurka da ke Birtaniya.
Jaridar ta ce Fadar White House ta ci gaba da ba da rahotannin cewa shugaban na kan hanyarsa ta komawa Amurka ne a cikin Air Force One, alhali kuwa an sauya jirgin da yake ciki.
Trump ya je Turkiyya ne domin halartar taron NATO cikin wani sabon jirgin alfarma da Qatar ta bai wa Amurka, wanda aka tanada domin amfani da shugaban ƙasa.
Har zuwa yanzu, Fadar White House ba ta fitar da wata sanarwa ba game da rahoton da Washington Post ta wallafa..
Alhakin rufe mashigar Hormuz ya kan Amurka - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Iran ta ce ya kamata ƙasashen duniya da su ɗora wa Amurka alhakin duk wata illa ta tsaro da tattalin arziki da ka iya tasowa sakamakon toshe tasoshin ruwanta a mashigar Hormuz.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawar waya da takwaransa na Jamus, Johann Wadephul, inda ya ce matakan da Amurka ke ɗauka a yankin ne suka haddasa rashin tsaro a mashigar.
Araqchi ya ce Iran na ci gaba da tattaunawa da Oman domin nemo wata amintacciyar hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.
Ya kuma zargi Amurka da Isra'ila da haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin ta hanyar hare-haren soji da yake cewa suna kai wa Iran.
A cewar kafafen yaɗa labaran Iran, ministan ya jaddada cewa samar da tsaro a mashigar Hormuz na bukatar kawo ƙarshen abin da ya kira matakan tsoma bakin Amurka ba bisa ƙa'ida ba, ciki har da toshe zirga-zirgar jiragen ruwa da sauran ayyukan da ya ce sun saɓa wa alƙawurran ƙasar.
Zan mayar wa Netanyahu martani kan watsi da shirin zaman lafiyar Gaza - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce nan ba da jimawa ba zai mayar wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu martani, bayan Netanyahu ya yi watsi da shirin zaman lafiya na Gaza mai kunshe da batutuwa 15.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar White House, inda ya ce zai wallafa martaninsa a shafinsa na Truth Social.
Ya ce yana da amsar da yake ganin ta dace, kuma zai wallafa ta a shafin.
Duk da rashin amincewar Netanyahu da shirin, Trump ya ce har yanzu dangantakarsa da firaministan tana nan da kyau sosai.
Netanyahu ya ƙi amincewa da shirin, yana mai cewa Isra’ila ba za ta amince da janye dakarunta daga Gaza ba matukar Hamas ba ta mika makamanta gaba daya ba.
Assalamu alaikum
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.