Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 30/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Imam Saleh

  1. Rufewa

    To jama’a, a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labaran a wannan shafi namu na Kai Tsaye daga sashen Hausa na BBC. Amma za mu sake dawowa gobe Alhamis, domin ci gaba daga inda muka tsaya.

    Sannan za ku iya latsa nan domin samun ƙayatattun labaran da muka wallafa a shafin na mu a wannan rana.

    Imam Saleh, ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An sako matuƙan jirgin Masar takwas bayan watanni biyar a hannun ƴan fashin teku

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta bayyana cewa an sako wasu matuƙan jirgin ruwa takwas ’yan ƙasar Masar, waɗanda ’yan fashin teku na Somaliya suka yi garkuwa da su tsawon watanni biyar.

    Ma’aikatar ta ce an kwashe watanni ana gudanar da tattaunawar diflomasiyya tsakanin gwamnatocin Masar, Somaliya da Yemen, kafin a samu nasarar kubutar da matuƙan.

    A watan Mayu ne aka yi garkuwa da matuƙan jirgin ruwan mai suna M.T. Eureka, a lokacin da suke tafiya a yankin Yemen. Daga nan ne ’yan fashin tekun suka karkatar da jirgin zuwa ruwan Somaliya, kusa da yankin Puntland, inda suka tsare ma’aikatan jirgin.

    Tun da farko a ranar Laraba, hukumomin yankin Puntland na Somaliya sun tabbatar da cewa ’yan fashin teku sun kashe ma’aikatan jirgin ruwa biyar ’yan ƙasar Pakistan, Indiya da Myanmar, bayan sun yi garkuwa da wani jirgin dakon mai.

  3. An kashe mutum 52 a sabon faɗan da ke ci gaba da ƙazanta a Tigray

    Akalla fararar hula 52 ne suka rasu a ciki da wajen garin Alamata da ke yankin Tigray na Habasha, bayan shafe kwanaki 3 ana gwabza kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen yankin.

    Wata kungiyar mayakan sa-kai mai goyon bayan gwamnati ta bayyana a ranar Litinin cewa dakarun tarayyar Habasha sun kwace ikon garin Alamata.

    Wakilin BBC ya ce wani likita a asibitin Alamata ya shaida masa cewa wadanda harin ya rutsa da su mazauna garin ne da kewaye, mamatan sun hada da yara da jarirai 'yan kwanaki 10 a duniya da kuma tsofaffin mata.

    Rikicin baya-bayan nan ya sanya fargabar sake tsundumar kasar cikin yakin basasa da aka kawo karshen shi a shekarar 2022.

  4. Iran ta gargaɗi UAE kan karɓar baƙuncin Netanyahu

    Sakataren tsaron Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ambato sakataren Majalisar Tsaron Ƙasar, Mohsen Rezaei, na “gargaɗi” ga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) kan karɓar baƙuncin Firaministan Isra'ila.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa da harshen Larabci, ba tare da ambaton sunan ƙasar ba, Mista Rezaei ya rubuta a shafin X cewa, "Kamar yadda karɓar sansanonin sojin Amurka bai samar muku da tsaro ba, haka ma karɓar bakuncin 'makashin Gaza' ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba."

    Rahotanni sun ce Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ziyarci UAE a wannan makon.

    A cikin saƙon da ya wallafa, Mista Rezaei ya ce: "Ku ɗauki darasi daga yaƙin baya-bayan nan, ku daina ruruta yaƙe-yaƙe, sannan ku daina yin ikirarin da ba su da tushe kan tsibiran Iran."

    A wannan makon, UAE ta sake sukar abin da ta bayyana a Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin "mamayar tsibirai uku" da Iran ke yi.

    Dangantaka tsakanin Iran da UAE ta kasance mai cike da takun-saƙa a watannin baya-bayan nan, musamman bayan hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai wa Iran a lokaci guda.

  5. Ukraine ta fara katse wutar lantarki yayin da Rasha ke tsananta hare-hare

    .
    Bayanan hoto, .

    Ukraine ta fara aiwatar da shirin katse wutar lantarki cikin gaggawa a birnin Kyiv, a daidai lokacin da Rasha ke ƙara tsananta hare-haren da take kai wa cibiyoyin samar da makamashi.

    An kuma shirya katse wutar lantarki a yankunan Chernihiv da Zhytomyr.

    Birnin Kyiv ya turnuƙe da hayaƙi mai a safiyar Laraba, bayan sabbin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Rasha ta kai cikin dare.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce an kai hare-hare kan cibiyoyin samar da makamashi a sassa daban-daban na ƙasar, inda aƙalla mutane bakwai suka mutu.

    Ukraine ta fara shirye-shiryen tunkarar lokacin hunturu, lokacin da ake yawan buƙatar makamashi, inda ta gina ƙananan tashoshin samar da lantarki guda 15 da aka ƙarfafa domin kare su daga hare-haren Rasha.

  6. Sabon harin Isra'ila ya kashe mutum 5 da ke tafiya a motar Bas a Gaza

    .
    Bayanan hoto, .

    Jami’an lafiya a birnin Gaza sun ce wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya afkawa wata motar bas, inda mutane biyar suka mutu.

    Asibitin Al-Shifa ya bayyana cewa an kai masa gawarwakin mutane 5 tare da wasu 13 da suka jikkata a lamarin, wanda ya faru a unguwar Tel al-Hawa da ke birnin Gaza.

    Ya zuwa yanzu babu wani bayani daga rundunar sojin Isra’ila kan harin.

    Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma, kusan kullum sai Isra’ila ta kai hare-hare wuraren da take zargin na ƙungiyar Hamas ne, hare-haren da galibi ke haddasa mutuwa ko jikkatar fararen hula.

  7. Najeriya ta mayar wa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo Gwaggon Birinta

    .
    Bayanan hoto, .

    Najeriya ta mayar wa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo wani ƙaramin gwaggwan biri da aka ceto, a wani mataki da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce shi ne karon farko da ta kammala cikakken aikin ƙasa da ƙasa na yaƙi da safarar namun daji.

    Jami’an Kwastam sun ceto dabbar mai suna Bili, daga hannun wata ƙungiyar masu safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba a watan Agustan 2023.

    Daga nan ne aka kai ta Gidauniyar Pandrillus da ke Calabar, inda aka ba ta kulawa da jinya ta musamman. An kuma yi mata gwajin ƙwayoyin halitta domin tabbatar da cewa asalinta daga Jamhuriyar Kongo yake.

    Mai magana da yawun Hukumar Kwastam ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa tafiyar Bili ta komawa gida ta fara ne ta mota daga Calabar zuwa Legas, kafin daga nan a ɗauke ta da jirgin sama zuwa Pointe-Noire.

    Wata mai kula da gwaggwan birin da kuma likitan dabbobi sun raka ta zuwa gandun namun daji na Tchimpounga, inda za ta ci gaba da samun kulawa. Gandun na daga cikin manyan cibiyoyin kula da namun daji da aka ceto a Afirka.

    Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce an gudanar da aikin mayar da dabbar ne tare da haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyin kare muhalli, ciki har da hukumar da ke kula da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa kan safarar dabbobi da tsirran da ke fuskantar barazanar bacewa, da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya.

    Hukumar ta ce aikin ya yi daidai da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da ke samar da kariya mafi girma ga birrai da sauran nau’o’in namun daji da ke cikin barazanar bacewa.

    Lamarin na cikin abubuwan da ke ƙara nuna yadda safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba ke ƙetare iyakokin ƙasashe. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce masu safarar namun daji kan ratsa da dabbobin ta ƙasashe daban-daban, inda suke amfani da wasu ƙasashe a matsayin wuraren wucewa kafin daga bisani su kai dabbobin wuraren da za a sayar da su.

    A shekarun baya-bayan nan, Najeriya ta zama muhimmiyar hanyar wucewar safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba a Afirka. Masu safarar dabbobi na amfani da ƙasar wajen safarar pangolin, hauren giwa da kuma birrai masu rai, kafin daga bisani a kai su wasu ƙasashe.

    Kwastam ta ce tsakanin watan Janairu da Satumban 2026, ayyukan da ta gudanar na yaƙi da safarar namun daji sun kai ga cafke kayayyaki da dabbobi har sau 22. A yayin ayyukan, an ceto dabbobi masu rai 699 tare da kama mutane 11.

    Kayayyakin da aka cafke sun haɗa da kilogram 220 na ƙwarangwal ɗin pangolin, hauren giwa guda 48 da kuma sama da kilogram 219 na hauren giwar da aka sarrafa.

    Masu rajin kare muhalli sun ce mayar da dabbobin da aka ceto zuwa ƙasashensu na taimaka musu wajen samun kulawar da ta dace, tare da aika saƙo ga masu safarar namun daji cewa ketare iyakar ƙasa ba yana nufin za su tsira daga hukuma ba.

  8. Sojojin Najeriya sun kai hare-hare 364 don tabbatar a tsaro a sassan Najeriya

    .
    Bayanan hoto, Dakarun Sojin Najeriya

    Shalkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce dakarunta sun kai hare-hare 367 a sassa daban-daban na ƙasar a watan Satumban 2026 don tabbatar da tsaro.

    Bayanai sun nuna cewa rundunar Operation Enduring Peace ce ta kai mafi yawan hare-haren, da jimillar hare-hare 147, sai Operation Fansan Yamma da hare-hare 115, sannan Operation Whirl Stroke da hare-hare 55.

    Operation Hadin Kai ta samu hare-hare 33, yayin da Operation Savannah Shield kai 13, sannan Operation Udo da ta kai hari huɗu.

    Rundunar Operation Delta Safe kuwa ba ta kai hari ko da gua ba a tsawon watan na Satumba.

    Da yake bayyana nasarorin da sojojin suka samu a sassa daban-daban na ƙasar ranar Laraba, daraktan watsa labarai na rundunar Manjo Janar Michael Onoja, ya ce dakarun sojin na mayar da martani cikin gaggawa.

    Ya ce sojojin na arangama da maharan cikin gaggawa, inda suke amfani da ƙarfin makamai da dabarun yaƙi, tare da dakile hare-haren cikin nasara.

  9. Dangote ya ƙaddamar da ginin matatar mai a Kenya

    .
    Bayanan hoto, .

    Attajirin Afirka kuma ɗan Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da aikin gina wata matatar mai a gabar tekun Kenya.

    Shugaban Kenya, William Ruto, ya ce matatar, wadda ake sa ran gina ta zai lakume dala biliyan 18 a yankin Lamu, za ta taimaka wa ƙasar wajen rage tasirin sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya.

    Aliko Dangote ya ce: "Wannan na nufin Afirka ta zo domin gina Afirka. A yau, ba kawai muna haƙa rami ne domin gina matatar mai ba, a'a, mun buɗe sabon babi na ci gaba a Afirka."

    Wani wakilin BBC ya ce aikin gina matatar ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka gudanar da zanga-zanga saboda damuwar da wasu ke nunawa kan yiwuwar illar da aikin zai iya yi wa muhalli.

    Sai dai duk da haka, Dangote na ci gaba da aikin ginin, duk da umarnin da wata kotu ta bayar na dakatar da aikin.

  10. Rundunar sojin Najeriya ta samar da ƙarin bataliyoyi 3 don samar da tsaro a Zamfara

    Dakarun Sojin Najeriya
    Bayanan hoto, Dakarun Sojin Najeriya

    Rundunar Sojin Najeriya ta fara aiki da sabbin bataliyoyin sojinta uku a Jihar Zamfara, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta mayar da martani cikin gaggawa.

    A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Birged ta 1 ta Sojin Najeriya da ke Gusau, ya fitar ranar Talata a shafin X, an ce sabbin bataliyoyin da aka fara aiki da su su ne Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 12 da ke Bakura, da Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 23 da ke Kaura Namoda, da Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 28 da ke Anka.

    Ana sa ran bataliyoyin za su faɗaɗa ayyukan rundunar sojin a wuraren da suke gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da tsaron yankunan da aka ɗora musu alhakin kula da su.

    Da yake jawabi a yayin bukukuwan fara aiki da bataliyoyin, Babban Kwamandan Runduna ta 8 ta Sojin Najeriya kuma Kwamandan Sashen Haɗin Gwiwa na Rundunar Yaƙi ta 2, Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar BP Koughna, wanda Mukaddashin Kwamandan Birged ta 1, Kanal Joseph Umaru, ya wakilta, ya sake jaddada ƙudurin rundunar sojin na ƙarfafa ayyukan tsaro a jihar.

  11. Rikici ya ɓarke tsakanin matuƙan jirgin sama ɗauke da fasinja 170

    Jirgin sama

    Wani jirgin sama da ke tafiya daga Dubai zuwa Tel Aviv, ɗauke da kimanin fasinjoji 170, ya yi saukar gaggawa a Saudiyya bayan da aka ruwaito cewa faɗa ya ɓarke tsakanin matuƙan jirgin.

    Wasu jami'an Isra'ila biyu sun ce ana kyautata zaton mataimakin matuƙin jirgin ya daba wa babban matuƙin wuƙa.

    Yayin da ƙarin bayanai ke fitowa daga fasinjojin jirgin, lamarin na ƙara zama mai ban mamaki da firgitarwa.

    Jirgin ya aika da saƙon gaggawa cewa ana ƙoƙarin ƙwace shi. Sai dai bayanan da ke fitowa yanzu na nuna cewa ana zargin ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ne da yunkurin ƙwace shi, ba wani fasinja ba.

    Fasinjojin da ke cikin jirgin sun bayyana cewa jirgin ya fara gangarowa da sauri, inda ya sauka da kimanin ƙafa dubu 17 cikin ƴan mintuna.

    An ce rikici ya ɓarke tsakanin matuƙin jirgin da mataimakinsa, inda aka daba wa aƙalla ɗaya daga cikinsu wuƙa.

    Wani fasinja ya ce daga bisani wasu mutane suka kutsa cikin ɗakin matuƙan jirgin domin taimakawa wajen shawo kan ɗaya daga cikinsu, kafin su ɗaure shi.

    Hotunan bidiyo da aka ɗauka da wayar salula sun nuna mutane da dama a cikin jirgin jikinsu na ɗauke da jini.

    Yanzu masu bincike za su tantance ko ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ya yi niyyar kifar da shi da gangan, da kuma ko akwai wata manufa ta siyasa a bayan lamarin.

    Jirgin na ɗauke da kusan Isra'ilawa 100.

    Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra'ila, Itamar Ben Gvir, ya bayyana lamarin a matsayin harin ta'addanci, yana mai cewa manufar ita ce kashe dukkan mutanen da ke cikin jirgin.

    Wani bidiyo da kafofin yaɗa labaran Isra'ila suka wallafa ya nuna wani da aka ce yana cikin jirgin yana bayyana cewa wani mutum ɗauke da wuƙa ya daba wa ɗaya daga cikin matuƙan jirgin.

    BBC Verify ta binciki bidiyon, kuma ba ta gano wata alamar cewa an sarrafa shi da fasahar AI ba.

    Haka kuma, ba a ga alamar cewa an wallafa bidiyon a intanet kafin faruwar lamarin ba.

    Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun ƙulla hulɗar diflomasiyya a shekarar 2020 ƙarƙashin yarjejeniyar Abraham Accords da Amurka ta shiga tsakani.

    Yarjejeniyar ta daidaita hulɗar ƙasashen biyu. Kafin wannan yarjejeniya, an hana jiragen Isra'ila bi ta sararin samaniyar Saudiyya.

  12. Kotu ta ɗaure mai shekara 50 kan yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe a Jigawa

    Wata babbar kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wani mutum mai shekara 50 hukuncin shekara 10 a gidan gyaran hali kan yi wa ƙaramar yarinya ƴar shekara 11 fyaɗe.

    Kotun, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Muhammad El Usman ta samu mutumin mai suna Abubakar Biniya da laifi.

    A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar shari’a a jihar Jigawa, Abbas Rufa’i Wangara ya fitar, wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin ne a watan Janairun 2024 a unguwar Galadanchi da ke Ringim.

    Masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Shari’a sun gabatar da shaidu shida tare da miƙa hujjoji biyar ga kotun, ciki har da rahoton likita, domin tabbatar da zargin.

    Wanda ake tuhuma ya bayar da shaida domin kare kansa, amma bai gabatar da wata shaida ba.

    Da yake yanke hukunci, alƙalin ya ce kotun ta yi la’akari da roƙon sassauci da Biniya ya yi da kuma kasancewar wannan ne karon farko da aka same shi da aikata laifi kafin ta yanke hukuncin.

    Baya ga ɗaurin shekara 10 a gidan gyaran hali, kotun ta umarci Biniya ya biya yarinyar diyyar naira 500,000.

    Kotun ta kuma bayar da umarnin saka sunansa a rajistar masu aikata laifukan cin zarafi ta hanyar lalata ta Jihar Jigawa, wadda Ma’aikatar Shari’a ta jihar ke kula da ita.

    Haka kuma, ta umarci a yi sanarwa a gidajen rediyo, kamar yadda sashe na 3(2), (4) da (5) na dokar hana cin zarafin mutane ya tanada.

    Kotun ta bai wa ɓangarorin da ke shari’ar wa’adin watanni uku su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

  13. 'Wasu matan ba su san suna ɗauke da cutar da ke sa mace gemu ba'

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Gemu ko gashin bakin da kuke gani a fuskar wasu mata, ba haka kawai ba ne. Larura ce!

    An ware duk watan Satumba domin faɗakar da mutane cewa kimanin kashi 10% na mata suna da larurar rikicewar sinadaran jiki wato PCOS a taƙaice.

    Albarkacin wannan wata, mun zanta da wata mai wayar da kai kuma da ke da wannan cuta domin jin suke fama.

  14. Abin da Mufti Menk ya cewa Rahama Sadau

    Rahama Sadau da Mufti Menk

    Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta koka kan salon wasu kamfanonin tsara tafiye-tafiye na ɗaukar bidiyon masu ibadar Umrah da suka je ƙasa mai tsarki ta kamfaninsu a wani ɓangare na tallata kamfanonin nasu.

    Rahama Sadau ta bayyana damuwarta ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana sha’awar zuwa Umra cikin rukunin jama’a amma salon kamfanonin da ke nema zama ruwan dare na matuƙar sanyaya gwiwa.

    Ta ce ya kamata Umrah ta kasance ibada maimakon mayar da ita wata dama ta samar da hotuna ko bidiyon da za a wallafa a shafukan sada zumunta.

    Saƙon nata ya ja hankalin mutane da dama inda fitaccen malamin addinin Musulunci Mufti Menk, ya yi martani kan saƙon nata inda kuma ya ba ta shawarar kamfanin da za ta iya zuwa umarah ta hannunsu wanda ya ce yana bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin sirri.

    Sai dai y ace a zamanin da ake ciki, mutane da dama kan samu ƙwarin gwiwar zuwa Umrah ne bayan sun ga wasu sun je amma a caerwa shi “abin da ya fi dacewa shi ne kada ɗaukar hotunan ya zama abin da aka fi mayar da hankali a kai.”

  15. Rukunin ƙarshe na sojin Amurka na ficewa daga Iraƙi

    Sojojin Amurka na ƙarshe na janyewa daga Iraki, abin da ke kawo ƙarshen kasancewar dakarun Amurka a ƙasar tsawon sama da shekara 20.

    Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yaba da rawar da sojojin suka taka, tana mai cewa sun yi nasarar murƙushe ƙungiyar ISIS a Iraki da ma yankin baki ɗaya.

    Pentagon ta ce janyewar sojojin ta kuma nuna sauyin da ake samu zuwa tsarin tsaro da Iraki za ta jagoranta, tare da samun goyon bayan Amurka ta hanyar hulɗar ƙasashen biyu kamar yadda aka saba.

    Sai dai masana harkokin tsaro a Iraki na gargadin cewa Iran da ƙungiyoyin da take marawa baya za su iya amfani da kafar da janyewar sojojin Amurka za ta haifar domin ƙara faɗaɗa tasirinsu.

    Sojojin Amurka sun fara mamaye Iraki ne shekara 23 da suka gabata, inda suka jagoranci ƙawancen ƙasashe wajen hambarar da gwamnatin Saddam Hussein.

    Daga bisani sojojin Amurka sun sake komawa ƙasar a shekarar 2014 domin yaƙi da ƙungiyar IS.

  16. Ina cikin ƙoshin lafiya kuma na shirya yin aiki gadan-gadan - Tinubu

    Bola Tinubu da manyan jami'an gwamnati

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce yana cikin ƙoshin lafiya kuma a shirye yake ya koma bakin aiki.

    Ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan isarsa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas bayan kammala hutun aiki na tsawon wata ɗaya a Turai.

    Da yake magana da manema labarai, Shugaba Tinubu ya kuma yi watsi da jita-jitar da ake yi cewa yana fama da rashin lafiya bayan shafe tsawon lokaci yana hutun aiki a Turai.

    Manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi cikinsu har da gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila, kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, da kuma manyan jami’an tsaro.

    Ya kuma ce jita-jita wani abu ne da aka saba gani a siyasa, amma ya jaddada cewa yana nan cikin koshin lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki.

    A cewarsa, ya ji daɗin hutun nasa, kuma babu wata matsala da yake fama da ita.

  17. Rasha ta sake kai gagarumin hari kan Kyiv

    Rasha ta sake kai wani mummunan hari ta sama kan yankin Kyiv babban birnin Ukraine cikin dare, inda ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marassa matuƙa.

    Wani babban jami'i ya ce gidaje da dama sun rushe a wata gunduma sakamakon harin, kuma an gano gawar wani yaro a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen.

    Ya ce an ceto wasu daga cikin iyalan yaron da suka samu raunuka a harin.

    Rahotanni sun ce harin ya kuma lalata rumbunan ajiya da wasu muhimman kayayyakin more rayuwa, lamarin da ya haifar da katsewar wutar lantarki da kuma tangarda wajen samar da ruwa.

    A baya-bayan nan dai Rasha ta ƙara yawan hare-haren da take kai wa birnin Kyiv cikin dare da kuma rana.

  18. Dangote zai ƙaddamar da aikin gina matatar mai a Kenya

    Dangote

    Nan gaba a yau ne, Attajirin Afirka Aliko Dangote, zai aza harsashin gina wata matatar man fetur a gabar tekun Kenya.

    Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya ce matatar wadda za a gina a yankin Lamu za ta taimaka wajen kare kasar daga sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya.

    Wakilin BBC ya ce ginin matatar ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da ke ikirarin cewa filin da za a gina matatar mallakinsu ne.

    Masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwa kan yiwuwar illa ga muhalli da aikin zai iya haifarwa.

    Sai dai kuma duk da haka, Dangote na ci gaba da fara aikin ginin duk da umarnin wata kotu da ya bukaci a dakatar da aikin.

    ..
    ..
    ..
  19. Barka da Hantsi

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Laraba - tabawa ranar samu daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.