Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 16 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Kotu ta yanke wa ɗan’uwan tsohon shugaban Syria, Assad hukuncin kisa

    Wata Kotu a Syria ta yankewa ɗanuwan tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad hukuncin kisa bayan samunsa da tafaka laifukan yaƙi da kuma cin zarafin ɗan adam.

    An kama Wassim al-Assad a watan Yuni bara.

    Mutane da dama na danganta shi da ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi , sai dai kotu ta ce bata same shi da laifi ba saboda rashin shaida.

    Hakuncin ya zo mako guda bayan yankewa Bashar al-Assad hukuncin kisa yayin da ya ke ci gabad a gudun hijira a Rasha.

    Ana ganin matakin a matsayin kokarin Siriya na yin adalci bayan kwashe shekaru ana gwabza rikici.

  2. Mawuyacin halin da sojojin Amurka suka shiga yayin yaƙar Iran

    Jirgin USS Lincoln ya daɗe yana kan ruwa yayin da yake aikin yaƙi da Iran.

    Wannan tsawaitaccen aiki ya janyo damuwa game da gajiya da matsalolin ƙwaƙwalwa da sojojin da ke cikin jirgin ke fuskanta.

  3. An kwance wani bam da ƴanbindiga suka dasa a Zamfara - Sojoji

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta a Arewa maso Yammacin ƙasar sun gano tare da kwance wani bam da ake zargin ƴanbindiga ne suka dasa a wani babban titin Jihar Zamfara, lamarin da ya hana afkuwar hasarar rayuka da dukiyoyi.

    A cewar rundunar, dakarun sun gano bam ɗin ne a ranar 17 ga watan Agustan 2026 a gefen hanyar Gurusu zuwa Gwashi da ke Karamar Hukumar Bukkuyum.

    Ta ƙarar da cewa, suna gano abin fashewar, sojojin suka killace yankin domin hana masu amfani da hanyar shiga cikin haɗari.

    Daga nan ne aka kira ƙwararrun masu lalata abubuwan fashewa domin gudanar da aikin.

    Rundunar ta ce masu lalata abubuwan fashewa sun samu nasarar kwance bam ɗin ba tare da wata matsala ba.

    Ta ƙara da cewa wannan nasara na nuna jajircewar dakarunta wajen tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi da kuma hana ƴanbindiga amfani da bama-bamai wajen kai hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro.

  4. Ɗaliban jami’ar ABU za su wakilci Najeriya a gasar jami’o’in duniya

    Ɗaliban jami’ar Ahmadu Bello (ABU) za su wakilci Najeriya a gasar ƙirƙire-ƙirƙire ta jami’o’in duniya ta ENACTUS da za a gudanar a birnin Sao Paulo na ƙasar Brazil

    Za a gudanar da gasar ne a watan Nuwamba, kuma sun samu wannan damar ne bayan da suka lashe gasar ta ƙasa da aka gudanar a Najeriya.

    Tawagar ENACTUS ta jami’ar ta zama zakarar Najeriya a gasar ta shekarar 2026, wadda aka gudanar a Legas daga ranar 11 zuwa 15 ga watan Agusta.

    Gasar ta haɗa ɗalibai daga jami’o’i da kwalejojin fasaha daban-daban na ƙasar.

    Nasarar ta ABU ta samu ne sakamakon wani aiki da tawagar ta gabatar kan magance matsalolin da ke addabar noman tumatur, musamman ƙwari da suke lalata tsirrai kafin girbi da kuma asarar amfanin gona bayan girbi.

    Mai ba da shawara ga tawagar, Farfesa M.K. Aliyu, ya ce nasarar ba ta rasa nasaba daga irin bincike, haɗin gwiwa da al’umma da kuma jajircewar ɗaliban.

  5. Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Zamfara

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta a Arewa maso Yammacin ƙasar sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane da ƴan ta’adda suka yi a yankuna daban-daban na Jihar Zamfara, inda suka kuɓutar da fararen hula daga hannun maharan.

    A ranar 17 ga watan Agustan 2026, dakarun sun kai ɗauki bayan samun rahoton sace mutane a kan hanyar Gurusu zuwa Anka.

    Rundunar ta ce sojojin sun bi sahun maharan cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta musu watsar da waɗanda suka yi garkuwa da su tare da tserewa.

    An ceto mutum bakwai da suka haɗa da mata huɗu da yara uku ba tare da sun samu rauni ba. Haka kuma a Karamar Hukumar Tsafe, dakarun sun mayar da martani bayan samun bayanan cewa ƴan ta’adda na ƙoƙarin yin garkuwa da matafiya a kusa da ƙauyen Magazu.

    Bayan artabu tsakanin ɓangarorin biyu, maharan sun tsere zuwa cikin daji yayin da aka kuɓutar da waɗanda suka kama.

    Wasu daga cikin waɗanda aka ceto sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci. Rundunar ta ce dakarunta za su ci gaba da matsa wa ƴan ta’adda lamba domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a a yankin.

  6. Sojojin ruwa sun ceto mutum 22 daga hannun ƴan fashin teku a Akwa Ibom

    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce ta ceto fasinjoji 22 da ƴan fashin teku suka yi garkuwa da su tare da ƙwato wani jirgin ruwa na fasinja da aka sace a hanyar ruwa tsakanin Calabar da Ibaka a jihar Akwa Ibom.

    Rundunar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne bayan samun rahoton harin da aka kai wa jirgin a ranar 11 ga watan Agusta.

    A cewar daraktan yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Abiodun Folorunsho, maharan sun tare jirgin ne jim kaɗan bayan ya wuce yankin Enwang, inda suka yi awon gaba da jirgin tare da sace fasinjojin da ke cikinsa.

    Ya ce jami'an sansanin FOB Ibaka sun haɗa gwiwa da Operation Delta Safe da kuma ƴansandan ruwa domin gano waɗanda aka sace da kuma kwato jirgin.

    Rundunar ta ce an kai waɗanda aka ceto asibitin FOB Ibaka domin yi musu gwajin lafiya da ba su agajin gaggawa kafin mayar da su Calabar tare da jirgin da aka ƙwato.

  7. Najeriya za ta kwaso ƙarin ƴan ƙasarta daga Afrika ta Kudu kan ƙyamar baƙi

    Gwamnatin Najeriya na shirin kwaso wasu ƙarin ƴan ƙasarta 83 daga Afirka ta Kudu, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan ƙaruwa da zanga-zangar ƙyamar a ƙasar.

    Ana sa ran mutanen za su isa Legas ranar Laraba, inda wasu mutane masu zaman kansu suka ɗauki nauyin tikitin dawowarsu.

    Dawowar tasu na zuwa ne a lokacin da ƙungiyoyin masu zanga-zanga ke ci gaba da neman a fitar da baƙin da ba su da takardun zama, har ma suka sanya ranar 30 ga Satumba a matsayin wa’adin da suke son su fice daga ƙasar.

    Fiye da mutum 150 ne suka gudanar da zanga-zanga a Durban, suna kira ga ƙasashen yankin kudancin Afirka su magance matsalar ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.

    Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce sama da mutum 80,000 ne aka kora ko kuma suka koma ƙasashensu da kansu yayin da take tsaurara matakan kula da shige da fice.

  8. EFCC ta gurfanar da wanda ake zargi da damfarar maniyyata aikin Hajji

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta gurfanar da wani mutum a gaban wata babbar kotun jihar Oyo bisa zargin shi da damfarar maniyyata ikin hajji naira miliyan 56.4.

    An gurfanar da mutumin ne kan zarge-zarge 57 wadanda ke da alaƙa da fashi da kuma yaudara.

    Hukumar ta lissafo sunayen wasu mutane 10 wadanda ta ce mutumin da take zargi ya damfara.

    Bayanin shari’ar da EFCC ta shigar ya nuna cewa mutumin ya karɓi kuɗin naira miliyan 56,491,000 daga mutane daga watan Nuwamban 2022 zuwa watan Yulin 2024.

    Mutumin ya riƙa shaida wa mutanen da yake karɓar kudi daga wurin su cewa shi jami’in hukumar kula da mahajjata ne ta jihar Kaduna.

    EFCC ta ce ya karɓi kuɗaɗen a hannunsu ne bisa hujjar cewa zai taimaka musu wajen tsara tafiyarsu zuwa aikin hajjin shekarar 2023.

    Hukumar ta ƙara da cewa mutumin ya ba su rasiɗin shaidar biyan kuɗi na ƙarya daga jihar Kaduna da kuma ƙasar Saudiyya.

  9. Iran ta ce ba za ta buɗe Hormuz ba har sai Amurka ta cika sharuɗɗan yarjejeniya

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya sake jaddada cewa Iran ba za ta buɗe Mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta aiwatar da dukkan sharuɗɗan da ke cikin yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ƙasashen biyu.

    Qalibaf ya ce Iran na buƙatar a cire takunkumin da aka ƙaƙaba mata, a saki ƙadarorinta da aka ƙwace, a kawo ƙarshen takunkumin man fetur, tare da dakatar da duk wata barazanar soja kafin a buɗe mashigar.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa Iran a shirye take ta mayar da martani mai tsanani idan aka sake kai mata hari.

    Kalaman nasa sun zo ne bayan jami’an Rundunar Juyin Juya Halin Iran sun bayyana irin wannan matsayi, yayin da wa’adin kwanaki 60 da yarjejeniyar ta tanada ya ƙare ba tare da cimma cikakkiyar yarjejeniyar ba.

    A nasa ɓangaren, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba ya sha’awar tsawaita yarjejeniyar wucin gadi da Iran.

  10. Malaman KASU kimanin 200 ne suka bar jami'ar - ASUU

    ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) reshen jami'ar jihar Kaduna (KASU) ta ce malaman jami'ar kimanin 200, ciki har da furofesoshi ne suka bar jami'ar sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta ƙulla da ASUU a 2025.

    Shugaban ASUU-KASU, Dakta Abubakar Abdullahi, ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Litinin, inda ya ce mafi yawan malaman da suka fice sun samu aiki a sabbin jami'o'i da ke ciki da wajen jihar Kaduna.

    Ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar, wadda ta fara aiki tun watan Janairun 2026, ya sanya malaman KASU cikin mafi ƙarancin albashi tsakanin ma'aikatan jami'o'i a Najeriya.

    ASUU ta bai wa gwamnatin jihar Kaduna da mahukuntan jami'ar wa'adin makonni biyu su fara aiwatar da yarjejeniyar, tare da gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya jawo yajin aikin sai baba-ta-gani a jami'ar.

  11. Kashi 40 cikin 100 ne na asibitoci suka da tsabta - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce kashi 40 cikin 100 ne kawai na cibiyoyin kiwon lafiya a duniya ke da banɗakuna masu tsabta da sauran muhimman kayayyakin tsafta da suka dace da marasa lafiya da ma’aikatan lafiya.

    A cikin wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da UNICEF suka fitar, an nuna cewa kashi 11 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya ba su da wata hidimar tsafta kwata-kwata, lamarin da ke shafar kusan mutum miliyan 936 a faɗin duniya.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa akwai babban bambanci tsakanin yankuna, inda kashi 23 cikin 100 ne kawai na asibitocin da ke yankin Afirka ta kudu da Sahara ke da ingantattun ayyukan tsafta, idan aka kwatanta da kashi 55 cikin 100 a yankunan Tsakiya da Kudancin Asiya.

    Baya ga tsafta, rahoton ya ce kashi 85 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya suna da wadataccen ruwa, amma ƙasa da kashi 60 cikin 100 ne suka cika ƙa’idojin tsaftace muhalli da hana yaɗuwar cututtuka, musamman a ƙasashe masu ƙarancin ci gaba

  12. Iran ta musanta kai hari kan ofishin Barzani daga ƙasarta

    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa harin da aka kai kan ofishin firaministan yankin Kurdistan na Iraq, Masrour Barzani, ya fito ne daga cikin ƙasar Iran.

    Araqchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da takwaransa na Iraq, Fuad Hussein, inda ya jaddada cewa Iran ba ta da wani bayani da ke nuna harin ya samo asali daga yankinta.

    A gefe guda, Fuad Hussein ya bayyana harin a matsayin wani abu mai haɗari da ka iya yin tasiri ga tsaron Iraq da ma yankin gaba ɗaya.

    Tun da safiyar ranar Talata, Masrour Barzani ya zargi Iran da kai harin jirgin maras matuƙi kan ofishinsa da kuma gidan shugaban hukumar leƙen asirin yankin Kurdistan.

    Shi ma mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya yi allawadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin wani lamari mai matuƙar tayar da hankali da ke buƙatar bincike da taka-tsantsan.

  13. 'Farin jinin Trump ya ragu matuƙa fiye da kowanne lokaci saboda yaƙin Iran'

    Wani sabon rahoto na kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kamfanonin dillancin labaran Reuters da Ipsos suka gudanar ya nuna cewa farin jinin Shugaban Amurka Donald Trump ya ragu matuƙa zuwa kashi 33 cikin ɗari, mafi ƙanƙanta da ya taɓa samu tun bayan komawarsa mulki.

    Kuri'ar ta kuma nuna cewa yaƙin Iran na daga cikin manyan abubuwan da ke damun Amurkawa, inda kashi 80 cikin ɗari suka ce suna fargabar yiwuwar yaƙin Amurka da Iran ya daɗe.

    Sai dai kashi 33 cikin 100 ne kawai suka amince da yadda Trump ke tafiyar da mulki, yayin da kashi 64 cikin 100 suka bayyana rashin gamsuwarsu da salon jagorancinsa.

    Adadin amincewar da ake yi wa Trump ya ragu da kashi 35 cikin 100 da aka samu a farkon wannan wata, kuma ya yi daidai da mafi ƙarancin matakin farin jinin da ya samu a wa'adinsa na farko a watan Disambar 2017.

    Tun bayan da Trump ya ba da umarnin kai hari kan Iran tare da Isra'ila, farin jininsa ya ci gaba da raguwa sosai a bana.

    Yaƙin da Amurka da Isra'ila suka yi da Iran ya kuma haddasa rufe mashigar Hormuz, wanda ke da muhimmanci ga kasuwancin kusan kashi ɗaya cikin biyar na ɗanyen mai a duniya, lamarin da ya sa farashin man fetur ya tashi a Amurka.

  14. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku daga yanzu zuwa ƙarfe 4 na yamma in sha Allah.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.