KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 03 - 09 Agusta 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na 03 - 09 Agusta 2026

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Pochettino ya amince da tsawaita kwantiraginsa a matsayin kocin Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mauricio Pochettino ya cimma yarjejeniyar ci gaba da zama kociyan tawagar ƙwallon ƙafa ta maza ta Amurka har zuwa shekarar 2030.

    Tsohon kociyan kungiyoyin Tottenham da Chelsea, wanda ya fara riƙe muƙamin a watan Satumbar 2024, ya jagoranci Amurka — ɗaya daga cikin ƙasashen da za su ka karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya — ​​zuwa matakin ƙungiyoyi 16 na gasar, kafin daga bisani Belgium ta doke su.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka (US Soccer) ta bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar ta ƙunshi faɗaɗa ayyukan Pochettino da tawagarsa ta masu horaswa, inda za su rika bayar da shawara da tallafi ga hukumar kan batutuwan da suka shafi ci gaban tsarin tawagar ƙasa baki ɗaya.

  2. Chelsea ta ɗauki ɗan wasan tsakiya, Barco daga Strasbourg

    ...

    Asalin hoton, getty

    Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Strasbourg, Valentin Barco, kan kwantiragin shekara bakwai.

    Matashin mai shekara 21 ya zama ɗan wasa na shida da Chelsea ta ɗauka a wannan bazarar, bayan zuwan Morgan Rogers da Danny Welbeck da Emmanuel Emegha da Maxence Lacroix da kuma Marco Palestra.

    Ɗan wasan tsakiyar zai haɗe da sauran tawagar Chelsea a rangadin shirye-shiryen tunkarar kakar wasa mai zuwa, inda za su kara da ƙungiyar Juventus ta Italiya a Hong Kong a ranar 5 ga watan Agusta.

    Chelsea ba ta bayyana kuɗin da aka kashe wajen ɗaukar ɗan wasan ba.

    Barco ya buga wa Argentina wasa ɗaya a gasar cin kofin duniya ta 2026, inda suka zo na biyu bayan Spain - kuma Jude Bellingham ya mare shi bayan nasarar da suka samu kan Ingila a wasan kusa da na ƙarshe.

    Barco, wanda ya fito daga makarantar horar da matasa ta Boca Juniors, ya koma Brighton a shekarar 2024 kan kuɗi £7.9m.

    Sai dai ya shafe shekara ɗaya ne kawai a yankin kudancin ƙasar, sannan ya koma Strasbourg a lokacin bazara mai zuwa bayan ya kammala wa'adin zaman aro a ƙungiyar.

  3. Newcastle ta sayi golan Braga Hornicek kan fam miliyan 25.7

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Newcastle United ta Ɗauki mai tsaron raga Lukas Hornicek daga Sporting Braga kan kuɗi £25.7m.

    Duk da cewa tuni Newcastle ta dauki Ewen Jaouen, mai shekaru 20, daga ƙungiyar Reims a wannan bazara, ƙungiyar ta kuma kasance tana neman mai tsaron raga na farko wanda ya riga ya ƙware sosai a fagen.

    Hornicek, mai shekara 24, ya tafi sansanin horar da ƴan wasa na Newcastle da ke ƙasar Spain a ƙarshen mako domin kammala yarjejeniyar komawarsa da kuma sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar, bayan da ƙungiyar ta biya kuɗin da aka ƙayyade na sakin ɗan wasan daga tsohuwar ƙungiyarsa.

  4. Hukumar ƙwallon kafar Ingila za ta janye goyon bayanta ga shugaban FIFA

    Infantino

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila za ta rubuta wa shugaban Fifa Gianni Infantino takardar janye goyon bayan da take ba shi a daidai lokacin da ya samu koma baya a shirinsa na sayar da hannun jari a gasannin Fifa ga masu zuba jari masu zaman kansu.

    Wannan ya zo ne yayin da UEFA ke barazanar ɗaukar matakin shari'a kan shawarwarin kuma hukumar ƙwallon ƙafar Wales ta janye goyon bayanta a bainar jama'a ga yunƙurin Infantino na ci gaba da shugabancin Fifa.

    A watan Maris mai zuwa, Infantino zai tsaya takara a karo na huɗu kuma na ƙarshe a matsayin shugaban FIFA kuma zai buƙaci ƙuri'u 106 daga mambobin Fifa 211 domin ya yi nasara.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa matsayin hukumar FA na Scotland kan makomar Infantino ya ci gaba da kasancewa daidai da na rashin kwarin gwiwar UEFA a kansa.

    Hukumomin ƙwallon ƙafa na Turai, da na Arewacin Amurka da Tsakiyar Amurka da Caribbean sun riga sun ƙalunblanci shugabancin Infantino a bainar jama'a, inda Uefa da Concacaf suka fitar da kalamai suna sukar shirye-shiryen.