Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 03 - 09 Agusta 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na 03 - 09 Agusta 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Barcelona ta soke wasan da za ta yi a Morocco saboda Ceuta

    Barcelona ta soke wasan sada zumunta na shirye-shiryen kakar wasa da za ta buga a Morocco saboda rikicin iyaka da ke ci gaba a Ceuta.

    Gwarzuwar La Liga na Sifaniya ta shirya buga wasa da ƙungiyar Ittihad Riadi Tangier a arewa maso yammacin Morocco ranar 15 ga Agusta a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryenta na tunkarar sabuwar kakar wasa.

    A cikin wata sanarwa, kulob ɗin ya ce: "Dangane da halin rashin tabbas da kuma yanayin da ake ciki a yanzu, FC Barcelona na ganin cewa bai dace a buga wasan ba."

    Ko da yake Barcelona ba ta fayyace takamaiman dalilin soke wasan ba, BBC Sport ta fahimci cewa matakin yana da alaƙa da rikicin da ke faruwa a Ceuta, yankin Spain da ke iyaka da Morocco a gabar arewacin Afirka.

    A makon da ya gabata, kimanin 'yan ci-rani 78,000 ne suka tsallaka daga Morocco zuwa yankin Spain ta Ceuta ta gabar teku, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 100 tare da haifar da takun-saka tsakanin wasu ƙasashen Tarayyar Turai masu buɗaɗɗun iyakoki.

    Duk da cewa mafi yawan 'yan ciranin sun koma Morocco, ana kiyasin cewa tsakanin 3,000 zuwa 5,000 har yanzu suna Ceuta.

    A sakamakon rikicin, Italiya ta dakatar da tsarin yarjejeniyar Schengen da Spain, tare da goyon bayan Finland da Denmark, yayin da Jamhuriyar Czech ta nemi a dakatar da mambancin Spain a yarjejeniyar na wani lokaci.

    Haka kuma Barcelona ta soke wani wasan sada zumunta da za ta buga da Preston North End bayan sansanin atisayen da ta yi a Birtaniya, inda ta buga wasa da Birmingham City.

    Ana sa ran ƙungiyar za ta kara da Nottingham Forest a ranar Asabar a birnin Udine na Italiya, sannan kuma za ta karɓi bakuncin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Al Ahly da ke Masar a ranar 19 ga Agusta.

    Tawagar Hansi Flick za ta fara kare kambunta na La Liga ne da wasa da Elche a ranar 23 ga Agusta.

  2. Crytal Palace ta ɗauki Tomiyasu tsohon dan wasan Arsenal

    Crystal Palace ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan ƙasar Japan, Takehiro Tomiyasu, bayan kammala gwajin da kulob ɗin ya yi masa.

    Ɗan wasan mai shekaru 27 ya kasance ba shi da kulob bayan ya shafe rabin kakar wasan da ta gabata tare da Ajax, kuma yana cikin tawagar Japan da ta halarci gasar Cin Kofin Duniya a wannan bazara.

    Tsohon ɗan bayan Arsenal, wanda ke iya taka leda a matsayin ɗan baya na gefe ko kuma tsakiya-baya, ya zama ɗan wasa na biyu da sabon kocin Palace, Pierre Sage, ya ɗauka bayan Oscar Mingueza.

    Kulob ɗin Crystal Palace bai bayyana tsawon lokacin kwantiragin da Tomiyasu ya sanya wa hannu ba.

    Palace na son ƙarfafa ɓangaren bayanta bayan babban ɗan wasanta na bayan na tsakiya, Maxence Lacroix, ya koma Chelsea.

    Tomiyasu ya buga wasanni 84 a dukkan gasa daban-daban tare da Arsenal tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, bayan ya taka leda a baya tare da Bologna da Sint-Truiden.

  3. Atletico ta fara tattaunawa da Tottenham kan Romero

    Atlético Madrid ta fara tattaunawa kan yiwuwar ɗaukar kyaftin ɗin Tottenham, Cristian Romero.

    Ɗan wasan na ƙasar Argentina, wanda ya sanya hannu kan sabon kwantiragin shekara huɗu da Tottenham a watan Agustan bara, ana sa ran zai bar kulob ɗin a wannan bazara.

    Haka kuma Inter Milan ta nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekaru 28, wanda ya buga dukkan wasanni bakwai na Argentina a hanyarta ta kaiwa wasan ƙarshe na gasar kofin duniya a watan da ya gabata, inda ta sha kashi a hannun Spain.

    Sai dai Romero ya daɗe yana cikin jerin 'yan wasan da kocin Atlético Madrid, Diego Simeone, ke son ɗauka, kuma ana ganin kulob ɗin na Spain na ƙoƙarin sake yin wani yunƙuri domin sayen ɗan bayan.

    Tottenham na sane da sha'awar da Atlético ke nuna wa Romero, kuma cimma yarjejeniya da ɗan wasan kan sharuɗɗan kansa ba zai zama matsala ba.

    Kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, ya bayyana kwanan nan cewa zai "girmama muradin" duk wani ɗan wasa da ke son barin ƙungiyar.

    Romero ya rasa ƙarshen kakar wasan da ta gabata saboda raunin gwiwa, yayin da Tottenham ta tsallake faɗa wa ajin ƙasa ne a ranar ƙarshe ta kakar.

    An kuma kori Romero daga fili sau biyu a kakar wasan da ta gabata, lokacin da Tottenham ta kammala kakar a matsayi na 17.

    A wani labarin kuma, abokin wasansa a tsakiya-baya, Micky van de Ven, na dab da amincewa da sabon kwantiragin shekara biyar da Tottenham.

  4. Sai mun kammala batun Guimaraes kafin Jaissle ya shigo

    Kocin Newcastle United, Matthias Jaissle, ya bayyana cewa an riga an yanke hukunci kan makomar Bruno Guimaraes tun kafin ya fara ganawa da kyaftin ɗin ƙungiyar da ke shirin barin kulob ɗin.

    Arsenal na gab da kammala cinikin fam miliyan 75 na ɗan wasan tsakiya bayan samun gagarumin ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin.

    Jaissle ya yi ɗan gajeren zance da Guimaraes a sansanin horaswar Newcastle da ke Spain a farkon wannan makon, amma daga baya ɗan wasan mai shekaru 28 ya yi bankwana cikin tausayawa da abokan wasansa da ma'aikatan kulob ɗin.

    A jawabinsa na farko ga manema labarai bayan an naɗa shi a matsayin babban kocin Newcastle, Jaissle ya ce: "Na yi ɗan gajeren zance da shi, amma an riga an yanke hukuncin. Tattaunawa ce mai daɗi. Shi ƙwararren ɗan wasa ne kuma mutum ne na kirki. Abu ne mai wuya, amma yanzu yana fuskantar sabon ƙalubale a rayuwarsa, kuma mu ma dole ne mu tunkari lamarin yadda ya kamata."

    Ya ƙara da cewa: "Muna da cikakken yarda da 'yan wasan da muke da su a yanzu, amma kuma za a samu wasu sauye-sauye a ƙungiyar."

  5. Madrid ta musanta neman Olise

    Real Madrid ta musanta rahotannin da suka danganta ta da ɗan wasan gefe na Bayern Munich da tawagar Faransa, Michael Olise, a watan Yunin 2026.

    Kulob ɗin na Sifaniya ya ce bai taɓa tuntuɓar dan wasan ba kai tsaye ko a fakaice, ko wakilansa, ko wani daga cikin mutanen da ke kusa da shi, bayan da rahotanni suka bayyana cewa Madrid na tunanin gabatar da tayin sama da euro miliyan 200 (£173m) domin sayensa.

    A cikin wata sanarwa, kulob ɗin ya ce: "Real Madrid tana son jaddada kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninta da Bayern Munich a matakin hukumomi, kuma tana nuna rashin jin daɗinta kan yaɗa jita-jitar da ba ta dace ba."

    Kulob ɗin ya ƙara da cewa: "Duk wata yiwuwar ɗaukar ɗan wasan da wata ƙungiya ke yi, dole ne da farko a tattauna batun tsakanin ƙungiyoyin biyu da abin ya shafa."

  6. Man City ta yi watsi da ta yin da Barcelona ta yi kan Rodri £38.5m

    Manchester City ta yi watsi da tayin farko na fam miliyan 38.5 daga Barcelona domin sayen ɗan wasan tsakiyarta Rodri.

    City na shirye ta sayar da ɗan wasan na Sifaniya, amma za ta nemi sama da fam miliyan 60.

    Rodri mai shekaru 30 ya shiga shekararsa ta ƙarshe a kwantiraginsa a Etihad, kuma har yanzu bai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya ba, lamarin da ya sa ake ta rade-radin makomarsa a wannan bazarar.

    Da farko dai ana ganin Real Madrid ce za ta zama ƙungiyarsa ta gaba, amma yanzu Barcelona ce ke kan gaba a takarar neman sa, bayan wasu majiyoyi sun shaida wa BBC Sport a ranar Alhamis cewa ɗan wasan ya amince kulob din ya fara tattaunawa da Manchester City. An gabatar da tayin ne kuma a ranar Juma’a.

    Da farko majiyoyin Barcelona sun shaida wa BBC Sport cewa babu tabbacin za a cimma yarjejeniya, amma yanzu alamu na nuna cewa lamarin na ci gaba da ɗaukar sabon salo.

    Kulob din ya bayyana a ranar Juma’a cewa har yanzu suna tattaunawa da wakilan ɗan wasan, sannan daga baya suka gabatar da tayinsu na farko.

    Majiyoyin BBC sun ce tattaunawar da aka yi da Real Madrid ta kawo ƙarshe.

    Rodri bai buga mafi yawan wasannin kakar 2024-25 saboda mummunar raunin da ya samu a gwiwa, sannan bai buga wasu wasannin ba ne saboda ciwon da ya ji a naman cinyarsa.

    Sai dai dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2024 ya dawo cikin ƙoshin lafiyarsa a gasar cin kofin duniya a lokacin bazara, inda ya jagoranci Spain zuwa lashe kofinta na biyu tare da samun lambar gwarzon ɗan wasan gasar.

  7. Trafford ya koma Leeds daga Manchester City

    Kungiyar Leeds United ta ɗauki mai tsaron ragar Manchester City, James Trafford, a yarjejeniyar da ta kai har fam miliyan 45.

    Dan wasan na Ingila ya bar filin wasa na Etihad ne bayan shekara guda kacal da dawowarsa daga Burnley a kan kudi fam miliyan 27 a lokacin bazarar bara. Trafford, ya kasance cikin tawagar Ingila ta gasar cin kofin duniya a wannan bazara amma bai samu damar buga wasa ba.

    Ya buga wa City wasanni 17 a kakar wasan da ta gabata - huɗu a gasar Premier League - amma ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da kungiyar ta samu a gasar Carabao Cup da FA Cup.

    Matakin da ɗan wasan mai shekaru 23 ya ɗauka na komawa West Yorkshire ya biyo bayan zuwan mai tsaron raga Gianluigi Donnarumma - wanda ya taɓa lashe gasar Champions League - a watan Satumba; zuwansa ya kawo ƙarshen fatan Trafford na zama babban mai tsaron ragar Manchester City.

    Wannansauya sheƙa ya kafa sabon tarihi dangane da kuɗin da aka biya don ɗaukar mai tsaron raga dan ƙasar Birtaniya, inda ya zarce fam miliyan 30 da Everton ta biya Sunderland domin ɗaukar Jordan Pickford a shekarar 2017.

    Haka kuma, hakan ya sanya shi cikin jerin masu tsaron raga mafi tsada a tarihi, inda Kepa Arrizabalaga (fam miliyan 68) da Alisson (fam miliyan 62) ne kawai suka fi shi tsada.

  8. Van de Ven ya kusa cimma yarjejeniyar sabon kwantiragi da Spurs

    Micky van de Ven ya kusa cimma yarjejeniyar sabuwar kwantiragin shekara biyar da Tottenham Hotspur.

    Ɗan wasan bayan na tawagar ƙasar Netherlands ya koma ƙungiyar ne daga Wolfsburg a shekarar 2023, bisa yarjejeniyar shekara shida da za ta ƙare a shekarar 2029.

    Majiyoyin BBC Sport sun bayyana cewa Van de Ven yana ta nazarin makomarsa a arewacin Landan kafin a naɗa Roberto de Zerbi a matsayin koci a watan Maris.

    Zuwan kocin ɗan ƙasar Italiya—wanda ya taimaka wajen ganin Spurs ta ci gaba da zama a gasar Premier League—ya taka muhimmiyar rawa wajen sanya ɗan wasan mai shekaru 25 ya yanke shawarar tsawaita zamansa a ƙungiyar.

  9. Vini Jr da Real Madrid sun cimma yarjejeniyar shekara shida

    Ɗan wasan gefe na Brazil, Vinicius Jr, ya amince da sabuwar kwantiragin shekara shida tare da Real Madrid, wadda za ta ci gaba da riƙe shi a filin wasan Bernabeu har zuwa shekarar 2032.

    Dan wasan mai shekara 26 ya shiga shekarar ƙarshe na kwangilarsa, kuma Arsenal ta nuna sha'awar ɗaukar sa a ƴan makonnin da suka gabata.

    Sai dai, a ranar Alhamis Real Madrid ta sanar da cewa ɓangarorin biyu sun amince su tsawaita kwantiraginsa har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2032.

    Ya koma Real daga Flamengo ta Brazil a shekarar 2018, kuma ya tsawaita kwantiraginsa shekara uku da suka gabata.

    Real da wakilansa sun shafe watanni 18 suna tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya, kuma yanzu ya tsawaita zamansa a ƙungiyar da a baya ya bayyana a matsayin ƙungiyar da ya yi mafarkin buga wa wasa.

  10. Forlan ya amince ya zama kocin riƙon ƙwarya na tawagar Uruguay

    Tsohon ɗan wasan gaba na Manchester United, Diego Forlan, ya amince ya zama babban kocin tawagar Uruguay na wucin-gadi.

    Forlan zai maye gurbin Marcelo Bielsa, wanda ya yi murabus bayan Uruguay ta kasa tsallakawa daga matakin rukuni a gasar cin kofin duniya.

    Ana sa rantsohon dann wasan mai shekara 47 zai jagoranci tawagar ƙasar a wasannin sada zumunta na wannan kaka, kafin a nada koci na dindindin a ƙarshen wannan shekarar ko farkon shekarar 2027.

    Baya ga jagorantar babban tawagar ƙasar, an kuma an naɗa Forlan a matsayin kocin tawagar Uruguay ta ƴan ƙasa da shekara 20.

    Tsohon kocin Leeds United,Bielsa, ya fara jagorantar Uruguay ne a watan Mayun 2023, inda ya yi nasara a wasanni 15 kacal cikin 39 da ya jagoranta, bayan ficewarsu daga gasar cin kofin duniya da wuri wanda ya ba da takaici, kocin ɗan kasar Argentina mai shekara 70 ya bayyana cewa zamansa a matsayin koci "bai bar wani tasiri ko sakamako mai amfani ba".

    Forlan ya zura kwallaye 36 a wasanni 112 da ya buga wa Uruguay, kuma ya lashe kyautar ƙwallon zinare yayin da tawagar ta kai matakin kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010 a Afirka ta Kudu.

    Ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon kafa a matakin ƙasa a watan Maris na shekarar 2015.

    Ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa ne a shekarar 2018 bayan ya buga wa ƙungiyoyi 10 wasa, inda inda ya fi taka rawar gani a Villarreal da Atletico Madrid.

  11. Doku ya tsawaita kwantiraginsa da Man City

    Ɗan wasan gefe Jeremy Doku ya zama ɗan wasan Manchester City na baya-bayan nan da ya tabbatar da ci gaba da zamansa a ƙungiyar bayan ya rattaba hannu kan sabon kwantiragin da zai ƙare a shekarar 2031.

    DAn wasan na ƙasar Belgium, ya koma City daga Rennes kan kubɗi fam miliyan 55.4 a shekarar 2023, kuma majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ɗan wasan mai shekara 24 zai ci gaba da zama a filin wasa na Etihad, inda ake sa ran za a fitar da sanarwa a hukumance a mako mai zuwa.

    Doku ya buga wa City wasanni 48 a kakar wasan da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye takwas, tare da taimaka wa ƙungiyar ta lashe gasannin FA Cup da Carabao Cup a kakar wasa ta ƙarshe da Pep Guardiola ya jagorance ta.

    Ya zama dan wasa na huɗu a City da ya tsawaita kwangtiraginsa a bazarar, bayan ɗan wasan tsakiya Phil Foden da masu tsaron baya Josko Gvardiol da Abdukodir Khusanov.

  12. Real Madrid ta kammala ɗaukar Diomande daga RB Leipzig

    Kungiyar Real Madrid ta kammala daukar ɗan wasan Ivory Coast, Yan Diomande, daga RB Leipzig kan kudin da ka iya kai wa fam miliyan 120 .

    Ɗan wasan mai shekaru 19, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara bakwai, kuma kuɗin da za a biya a kansa na iya zarce fam miliyan 115 da Real ta amince ta biya Borussia Dortmund kan Jude Bellingham a watan Yunin 2023.

    Ƙungiyar Paris St-Germain ce ke kan gaba wajen zawarcin matashin ɗan wasan, amma zakarun gasar Champions League ɗin sun janye daga shirin ɗaukar sa a ranar Lahadin da ta gabata bayan an ƙi amincewa da tayin fam miliyan 102.5 da suka yi. Idan har Real ta biya dukkan kuɗin da ya kai fam miliyan 120 kan Diomande, zai zama ɗan wasa na huɗu mafi tsada a tarihi, bayan Neymar da Kylian Mbappe na PSG, da kuma Alexander Isak (tsohon dan wasan Newcastle da ke buga wa Liverpool wasa a yanzu).

    Haka kuma, Diomande shi ne dan wasa na Afirka mafi tsada, inda ya zarce fam miliyan 72 da Arsenal ta biya Lille kan ɗan ƙasar Ivory Coast, Nicolas Pepe, a shekarar 2019.

  13. Everton ta ɗauki dan wasan tsakiya Norgaard daga Arsenal

    Everton ta ɗauki ɗan wasan tsakiya Christian Norgaard daga Arsenal kan kwantiragin shekara biyu.

    An rawaito cewa ɗan wasan na Denmark mai shekara 32 ya koma Everton ne kan kudi fam miliyan 7.

    Norgaard, wanda ya koma Arsenal a bara daga Brentford kan fam miliyan 15, bai shiga cikin jerin ƴan wasan Gunners da za su fafata a wasan sada zumunta da Real Betis a ranar Laraba ba.

    Ya buga wa Arsenal wasanni 20 a kakar wasan da ta gabata, amma bakwai kawai ya buga a gasar Premier League, a lokacin da ƙungiyar ta arewacin London ta lashe kambunta na farko cikin shekara 22.

    Haka kuma, a wannan bazara Everton ta ɗauki dan wasan tsakiya Hayden Hackney daga Middlesbrough kan farashin fam miliyan 16.5, tare da ɗan wasan gefe mai shekaru 20 Tyrique George, wanda aka ɗauko daga Chelsea kan farashin fam miliyan 18 bayan ya shafe rabin kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a Everton.

  14. Infantino ya nemi afuwa kan shirin sayar da hannun jarin gasannin FIFA

    Gianni Infantino ya nemi afuwa kan "kurakurai" da ya yi a shirin da ke cike da ce-ce-ku-ce na sayar da hannun jari a gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu, amma zai ci gaba da zama shugaban Fifa bayan ya sami goyon bayan manyan jami'ai a wani taro da aka yi a Moroko.

    Infantino ya kira mambobin kwamitin gudanarwa zuwa ofishin Fifa na Afirka da ke Rabat a ranar Laraba bayan sukar da ake yi masa kan shirin nasa da tuni aka soke, inda hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta duniya ta fitar da sanarwar goyon baya awanni huɗu bayan kammala taron.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, Uefa ta ce a ƙarshen mako ta rasa ƙwarin gwiwa kan Infantino, inda ta bayyana shirin nasa a matsayin "yarjejeniya mara kyau, mai cike da ruɗani, kuma mara tabbas".

    Tun da farko dai, mahukuntan FiFA, sun musanta wani labari da jaridar Times ta wallafa, wanda ke cewa Infantino ya yi wa ƙasar Moroko alƙawarin cewa za ta karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030 idan har ta mara masa baya.

    FIFA ta bayyana labarin a matsayin "ƙarya," tare da cewa za a yanke hukunci kan inda za a gudanar da wasan ƙarshen gasar ta haɗin gwiwa tsakanin Spain da Portugal da Moroko "a lokacin da ya dace."

  15. Palace na shirin ɗaukar Tomiyasu yayin da ta ke nazari kan March

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace na shirin ɗaukar Takehiro Tomiyasu kan cinikin kyauta bayan ya nuna kwazonsa a lokacin szaman gwaji da ya yi da ƙungiyar, sannan kuma suna duba yiwuwar ɗaukar dan wasan gefe Solly March.

    A makon da ya gabata ne BBC Sport ta rawaito cewa Palace da mai tsaron bayan nan Tomiyasu na tattaunawa kan kwantiragin dindindin, wanda zai ba ɗan wasan na Japan damar komawa gasar Premier League.

    Ana kuma fahimci cewa Palace na ci gaba da yunƙurin ɗaukar Tomiyasu kafin fara sabuwar kakar wasa.

    An riga an cimma matsaya kan sharuɗɗan yarjejeniyar, inda aka ɗora wa babban kocin Palace, Pierre Sage, alhakin yanke hukunci kan ko za a ɗauki tsohon ɗan wasan na Arsenal mai shekara 27.

    Ƙungiyar ta Eagles na kuma duba yiwuwar ɗaukar March, wanda ya bar Brighton a ƙarshen kakar wasan da ta gabata. An ba da shawarar daukar March, mai shekaru 32, zuwa Palace, kuma an tattauna batun yiwuwar hakan a tsakanin jami'an kungiyar a filin wasa na Selhurst Park.

  16. Arsenal na shirin ɗaukar kyaftin ɗin Newcastle

    Arsenal na shirin kammala yarjejeniyar ɗaukar kyaftin ɗin Newcastle United, Bruno Guimaraes, bayan dogon lokaci ana tattaunawa.

    A ranar 30 ga watan Yuli ne BBC Sport ta bayar da rahoton cewa ana sa ran Guimaraes zai koma ƙungiyar da ta lashe gasar Premier League bayan samun ci gaba a tattaunawar.

    Yanzu haka an kusa cimma cikakkiyar yarjejeniya, inda Guimaraes ke jiran izinin barin sansanin horaswa na Newcastle da ke La Manga a ƙasar Spain, domin kammala matakan ƙarshe na komawarsa filin wasa na Emirates.

    Arsenal na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da gwajin lafiyar ɗan wasan tsakiyar na Brazil a wannan makon.

    Babu tabbas kan kudin da za a biya, amma majiyoyi na nuni da cewa adadin na iya kai wa fam miliyan 80.

    Guimaraes, wanda ya koma Newcastle daga Lyon a shekarar 2022, ya bayyana ƙarara cewa yana son komawa Arsenal, kasancewar ɗan wasan mai shekaru 28 ya zama babban ɗan wasan tsakiya da Mikel Arteta ke matuƙar son ɗauka.

    Newcastle da Arsenal sun shafe wannan makon suna tattaunawa kan cikakkun sharuɗɗan yarjejeniyar, kuma yanzu ana ganin ana daf da cimma yarjejeniyar ta ƙarshe.

  17. An bai wa Vozinha izinin amfani da laƙabinsa a Colo-Colo

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Chile (ANFP) ta amince ta bai wa mai tsaron ragar Cape Verde, Vozinha, damar sanya sunan da aka fi saninsa da shi a bayan rigarsa ta ƙungiyar Colo Colo.

    Ɗan wasan mai shekaru 40 ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni shida da Ƙungiyar ta Chile (Liga de Primera) a ranar Litinin, bayan ya samu yabo a duniya saboda rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya.

    A bisa Ƙa'idojin gasar, ya kamata ya buga wasa da sunansa na asali, wato Josimar Jose Evora Dias, kasancewar dokokin ANFP sun tanadi cewa "ba a yarda a sanya sunayen laƘabi ko na barkwanci" a jikin rigunan wasa ba.

    Sai dai, Ƙungiyar Colo Colo ta samu izinin ya buga wasa da sunan da ya shahara da shi.

    Vozinha ya isa Santiago a ranar Lahadi inda magoya bayan ƙungiyar Colo Colo suka yi masa tarba ta musamman, sannan ya shiga atisaye tare da sababbin abokan wasansa bayan kwana biyu.

  18. Liverpool ta shirya ɗaukar Barcola kan farashin fam miliyan 100

    Liverpool ta riga ta biya fiye da fam miliyan 100 sau biyu domin sayen ƴan wasa - wato ɗan wasan tsakiya Florian Wirtz da ɗan wasan gaba Alexander Isak - kuma akwai yiwuwar za ta sake yin hakan.

    Ɗan wasan gefe na Paris St-Germain da tawagar Faransa, Bradley Barcola, ya zama babban ɗan wasan da Liverpool ke son ɗauka a wanbnan bazarar; ƙungiyar ta filin wasan Anfield ta shirya biyan kusan fam miliyan 100, yayin da PSG ta ƙaƙabawa ɗan wasan farashin fam miliyan 145.

    Liverpool, wadda ta zo ta biyar a gasar Premier a kakar wasan da ta gabata da tazarar maki 25 tsakaninta da zakarun gasar, Arsenal - na iya biyan Bayer Leverkusen jimillar kuɗin da ya kai fam miliyan 116 a kan Wirtz, bayan da ta riga ta karya tarihin kashe kudi a ƙungiyar ta hanyar biyan fam miliyan 125 domin ɗauko Isak daga Newcastle.

    Yanzu kuma, ana iya ganin kungiyar ta kashe maƙudan kudade domin dauko Barcola mai shekaru 23, wanda ya kasance cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya.\

    Barcola ya koma PSG daga Lyon a shekarar 2023 kan kuɗin da aka bayyana cewa ya kai fam miliyan 38.5, kuma tun daga lokacin ya lashe kofunan Ligue 1 guda uku, da gasar French Cup sau biyu, tare da Kofin UEFA Super Cup da kuma Kofin FIFA Intercontinental Cup.

  19. An yi wa Salah tarbar gwarzo a Trabzonspor

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Trabzonspor ta Turkiyya za ta tabbatar da siyan Mohamed Salah yayin da magoya bayanta suka yi masa tarba ta karamci a lokacin da ya isa Turkiyya.

    Ɗaruruwan magoya baya sun taru a wajen filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul ranar Laraba yayin da Salah ya fito sanye da kaya masu launukan Trabzonspor.

    Ɗan wasan gaban mai shekarA 34 ya bar Liverpool a Ƙarshen kakar wasa da ta gabata bayan shekara tara a Merseyside, inda ya zura ƙwallaye 257.

    Ba a tabbatar da albashin da Salah zai samu a Trabzonspor ba, amma tunda shi ɗan wasa ne mai zaman kansa, ƙungiyar Super Lig za ta iya ware wasu daga cikin kasafin kudinta don biyan albashinsa.

    Salah, wanda ya zura ƙwallaye 50 a gasar Champions League, zai buga gasar kwallon kafa na zakarun Turai da Trabzonspor a kakar wasa mai zuwa bayan ta ƙare a matsayi na uku, maki takwas a bayan zakarun Turkiyya Galatasaray.

  20. Kocin Cape Verde Bubista ya yi murabus yayin da Ivory Coast ta sake naɗa Renard

    Bubista ya yi murabus daga muƙaminsa na babban kocin tawagar Cape Verde domin komawa kƙungiyar RS Berkane ta ƙasar Moroko, yayin da Ivory Coast ta ɗauki Herve Renard domin ya sake jagorantar tawagarta a karo na biyu.

    Bubista ya jagoranci ƙasar tsibirin zuwa matakin ƴan 32 na gasar cin kofin duniya a watan da ya gabata, inda tawagar ta 'Blue Sharks' ta sha kashi da ci 3-2 a hannun Argentina—wadda daga bisani ta zo ta biyu a gasar.

    Kocin mai shekara 56 ya kuma kai matakin daf da na kusa da na ƙarshe (quarter-final) a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 tare da Cape Verde, bayan ya fara jagorantar tawagar a watan Janairun 2020.

    Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da ƙungiyar RS Berkane, wadda ta zo ta biyu a gasar firimiya ta Moroko a kakar wasan da ta gabata; zai maye gurbin Moin Chaabani, wanda aka naɗa a matsayin sabon babban kocin Tunisia.

    Renard ya taba lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (Afcon) sau biyu a matsayin koci, ciki har da nasarar da ya samu tare da Ivory Coast a shekarar 2015.

    A baya, ya jagoranci Zambia zuwa ga nasarar lashe kofin a shekarar 2012, abin da aka bayyana a matsayin wani gagarumin tarihi mai ban mamaki.

    Tun bayan barin Ivory Coast a watan Mayun 2015, Renard ya horas da tawagogin Moroko, da Saudiyya (sau biyu) da kuma tawagar mata ta Faransa, haka kuma ya jagoranci tawagar Tunisia a wasanni biyu a gasar cin kofin duniya ta bana.