Maƙiya ya neman sake ƙaddamar da yaƙi - Iran

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce mostin da maƙiyan ƙasar ke yi a fili da kuma a ɓoye na nuna cewa har yanzu ba su yi watsi da manufofinsu na kai hare-hare a ƙasar ba, suna neman su ƙaddamar da yaƙi.
Qalibaf ya bayyana haka ne a cikin saƙon murya na uku da ya fitar, inda ya yi nuni da cewa wata guda kenan da tsagaita wuta, yana mai cewa yanayin siyasar da ke kewaye da shugaban Amurka, Donald Trump, na da tasiri wajen yanke hukunci game da Iran.
Ya ce ana ci gaba da matsin tattalin arziki da na siyasa kan Iran domin tilasta mata ja da baya, amma ya yi ikirarin cewa sojojin ƙasar sun yi amfani da wannan lokacin tsagaita wuta wajen sake gina ƙarfinsu da shirinsu na aiki.
Shugaban majalisar ya kuma soki wasu ɓangarorin siyasa a cikin gida, yana zarginsu da yin watsi da yanayin tsaro tare da mayar da hankali sosai wajen sukar gwamnati. Ya ce irin waɗannan sukar na iya cutar da haɗin kan ƙasa.


















