BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Ba za mu lamunci ana tattaunawa ana kai hare-hare ba - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 18ga watan Yulin 2026
Me ya bambanta ƴansandan jihohi da 'askarawan' da gwamnoni suka samar?
Tun kafin amincewa da ƙudurin kafa ƴansandan jihohi, gwamnoni da dama sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida, kamar ƴan sa-kai, jami'an tsaron yanki da kuma askarawa, domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Arsenal na son Rogers, Utd kuma Williams, Salah zai tafi Besiktas
Arsenal ta sanya Morgan Rogers na Ingila da Aston Villa, a matsayin babban wanda take son ɗauka domin ƙarfafa gabanta, yayin da Utd ke nazarin ɗaukar ɗan wasan gefe na Nottingham Forest, Neco Williams, shi kuwa Salah na shirin tafiya Besiktas.
Yadda mutumin da bai yi suna ba a siyasa zai zama Firaiministan Birtaniya
Saboda jam'iyyar Labour mai mulki ta yanke shawarar ba za ta gudanar da zaɓen shugabanci ba, sai dai za ta naɗa shi kai tsaye, ba a samu tattaunawa sosai kan manufofinsa ko salon mulkinsa ba.
Hanyoyi 4 da mace za ta iya ɗaukar ciki waɗanda suka saɓa wa al'ada
Akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun ciki da ba a saba gani ba, abin da wasu ke ganin ba zai yiwu ba.
Mary Habila: Abin da muka sani kan mutuwar budurwa a gidan minista Umahi
Minista David Umahi ya ce kafin Mary Habila ta rasu, ta sanar da saurayinta cewa hancinta na zubar da jini.
Yadda matasan Najeriya ke rububin zama ƴansanda - Mutum nawa ake ɗauka?
A ɗaukar da hukumar ta yi na baya-bayan nan wato na 2025/26, masu neman shiga aikin sun kai 616,873 daga faɗin Najeriya.
Wace ce Aisha Achimugu da kotu ta ƙwacewa kadarori na biliyoyin kuɗi?
Hukumar EFCC ta ce bincikenta ya gano cewa biliyoyin nairori da kuma miliyoyin daloli sun riƙa shiga da fita cikin asusun bankuna da kamfanonin da ke da alaƙa da 'yar kasuwar.
Amfani shida da Sallah ke da su ga lafiyar mai yin ta
Baya ga lada da kusanci ga Ubangiji, masana lafiya sun alaƙanta ta da inganta lafiya da tsaftar jiki.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 18 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 18 Yuli 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 18 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 17 Yuli 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Sakamakon wasannin Gasar Kofin Duniya 2026
Dukkanin bayanan da suka kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
Wasanni
Ko Sifaniya za ta sake taka irin rawar da ta taka a gasar kofin duniya ta 2010?
Sifaniya ta kai wasan karshe a gasar kofin duniya 2026, ƙwazon da kasar ke yi a bana ana danganta kamaiceceniya da wadda ta lashe kofin duniya a 2010. Ga rahoton da Mohammed Abdu ya haɗa.
KAI TSAYE, Nawa za a bai wa ƙasar da ta lashe Gasar Kofin Duniya?
Gasar Kofin Duniya: Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai game da Gasar Kofin Duniya ta 2026 da sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 13 zuwa 19 ga watan Yuli, 2026.
Milan na zawarcin Spence da Romero, Liverpool na son Sano
Inter Milan na tattaunawa kan sayen Djed Spence da Cristian Romero, yayin da Liverpool ke kan gaba wajen neman Kaishu Sano, ita kuwa Arsenal na son Ezri Konsa ne.
Dalilai uku da ke bai wa Argentina damar farke ƙwallaye har ta ƙara
Argentina mai rike da kofin duniya ta zo da wani salo a gasar cin kofin duniya 2026, inda ake zura mata ƙwallo a raga, amma sai ta farke ta kuma kai zagayen gaba. Shin menene dalilin hakan? Mohammed Abdu ya tsara mana rahoto kan wannan.
Me ya sa rashin nasarar Ingila a hannun Argentina ta zama mafi raɗaɗi?
Shekarun baƙin cikin Ingila yanzu za su wuce 60, na rashin lashe kofin duniya, amma rashin nasara a hannun Argentina a wasan daf da karshe, zai kasance mafi muni da raɗaɗi a Gasar Kofin Duniya da ta buga.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Badaƙalar kuɗi 5 da suka shafi kamfanin man fetur na Najeriya
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya sha fuskantar zarge-zargen badaƙalar kuɗi a tsawon shekaru, daga zargin ɓacewar kuɗin sayar da man fetur zuwa zargin badaƙalar tallafin man fetur.
Manyan kadarorin Emefiele da kotu ta ƙwace
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026
Jami'an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da ceto ɗaliban da shugaban makarantar da wani jami'in NECO a sanarwa da ya fitar.
Ko ratse wa Mashigar Hormuz za ta magance tsadar fetur a duniya?
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigila ta ruwa a duniya, wadda ta ƙara jan hankalin duniya musamman bayan ɓarkewar yaƙi a tsakanin Iran da Amurka.
Iran ta zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 16/07/2026
Majalisar wakilan Amurka ta dakatar da dukkan tallafin da ake bai wa Najeriya
A baya ƙudurin ya bai wa Amurka damar riƙe kashi 50% ne na tallafin, amma a yanzu majalisar ta ƙara shi zuwa kashi 100%.
Abu 5 da kake buƙata don zama ɗansanda a Najeriya
Ƴansandan za su gudanar da tantancewa da kuma gwaje-gwajen lafiya a kan masu neman zama ɗansadan da zarar sun isa kwalejin horarwar kuma nan take ake sallamar wadanda suka gaza tsallake gwajin da tantancewar.
Abubakar Malami: Jerin kadarori 48 da aka ƙwace daga tsohon ministan shari'a
EFCC ce dai ta shigar da ƙara ta buƙatar ƙwace kadarorin tsohon ministan guda 57 na dindindin da darajarsu ta kai naira biliyan 212.8.
Shari'o'i huɗu da jam'iyyar ADC ke fuskanta gabanin zaɓen 2027
Rikicin da ya dabaibaye ADC ya fi karkata ne kan tambayar waye ke da ikon jagorantar jam'iyyar da kuma tsare-tsarenta domin fuskantar babban zaɓen da ke tafe.
Yankuna 5 da suka fi haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa a Najeriya
Akwai wasu yankuna da ake yawan samun ambaliyar ruwa saboda yadda suke kusa da manyan koguna da madatsun ruwa, ko kuma saboda ruwa da ake saki daga wasu manyan madatsun da ke cikin Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya wajen kawo ƙarshen yaƙi da Iran
Sabuwar buƙatar da Donald Trump ya gabatar game da yaƙin Iran ta daɗe ne na sa'o'i 24 kacal, kuma ta nuna shugaban ƙasa da ke neman hanyoyi marasa al'ada domin fita daga wani mawuyacin hali.
Yadda ake muzguna wa direbobi don bayar da cin hanci a Najeriya
Masu harkokin sufuri a Najeriya sun yi zargin cewa, hanyoyin kasar sun zame masu wani waje da ake tilasta musu bayar da makudan kudade a duk rana matsayin cin hanci.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.































































