G-100: Sabuwar haɗakar da ke da nufin kawar da Tinubu daga mulki

Asalin hoton, Multiple
Ƴan Najeriya na ci gaba da muhawara kan sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta G-100 da ta ɓulla a ƙasar da nufin haɗa kan ƴan hamayya.
Ɓullar ƙungiyar ta sa siyasar ƙasar ƙara ɗaukar sabon salo, yayin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2027.
Ƙungiyar ta ce ta fara tattaunawa domin haɗa kan jiga-jigan hamayyar ƙasar domin samar musu da mafita.
Malam Salihu Lukman ɗaya daga cikin jiga-jigan ƙungiyar ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar na shirin gudanar da wani babban taronta a mako mai zuwa domin fara babban aikin da ke gabanta.
Wannan na zuwa ne yayin da kusan ɗaukacin manyan jam'iyyun adawar Najeriya ke fama da rikice-rikice na cikin gida, inda wasu ke fuskantar shari'o'i a kotu gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.
Tuni wa'adin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗiba wa jam'iyyun siyasa na miƙa sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa ya ƙare.
Jam'iyyun hamayya a Najeriya sun sha ƙulla ƙawance da nufin kawar da jam'iyyar mai mulki, ciki har da ƙawancen da APC ta ƙulla a 2014, wanda ya taimaka mata karɓe mulki daga PDP a 2015.
Sai dai a baya-bayan nan yunƙurin da ƴan hamayya suka yi na haɗewa a jam'iyya ɗaya domin tunkarar babban zaɓen 2027 ya ci tura, inda ba tare da daɗewa ba suka sake tarwatsewa zuwa cikin wasu jam'iyyun daban-daban.
Mece ce ƙungiyar G-100?
Wata gamayyar ƴan hamayya ne su kimanin 100 da suka taru wuri guda, ƙarƙashin inuwa ɗaya da nufin samun mafita.
Malam Salihu Lukman ya shaida wa BBC cewa an kafa ƙungiyar ne kimanin mako biyu da suka gabata, amma sai a ranar 18 ga watan Agusta ne za a ƙaddamar da ita a hukumance.
Wasu daga cikin ƴansiyasar da ke cikin ƙawancen haɗakar sun haɗa da Salihu Mohammed Lukman da Hon. Nnena Ukeje da Elder Simon Achuba da Dr. Akilu Indabawa da Hon. Annie Ekeh da Prof. Anthony Kila da Dr. Awalu Anwar da Dr. Emeka Ejikonye da Dr. Ibrahim Moddibo da Dr. Ladan Salihu.
''Kuma tuni muka samu ganawa da duka ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakan su a jam'iyyun adawa da kuma shugabannin jam'iyyun domin sama wa hamayya mafita a ƙasar'', in ji Salihu Lukman.
Mece ce manufar ƙungiyar?
Salihu Lukman ya ce haɗakar da manyan manufofi, waɗanda take ganin za su taimaka wajen inganta ƙarfin hamayyar ƙasar.
''Ɗaya daga cikin manyan manufofinmu shi ne mu samu ƴan hamayyar su ƙarfafa dangantaka tsakanin ƴan hamayyar ta yadda za su yarda su dunƙule wuri guda'', in ji shi.
Haka kuma ya ce babban manufar haɗakar ita ce samun haɗin kai domin tsayar da ɗan takarar adawa guda ɗaya da zai ƙalubalanci Tinubu da APC.
Masu lura da al'amuran siyasar Najeriya sun jima suna cewa yadda jam'iyyar APC ta yi ƙarfi a ƙasar, akwai buƙatar ƴan hamayyar su dunƙule wuri guda domin tunkarar ta.
Jam'iyyun da ƙawancen ke zawarci
Dangane da jam'iyyun da suka amince da shiga wannan haɗakar kuwa, Malam Salihu Lukman ya ce Jam'iyyu guda shida suka amince da shiga haɗakar.
''Jam'iyyun sun haɗa da ADC da NDC da PDP ɓangaren Tanimu Turaki da PRP da SDP da kuma APM,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.
''Imaninmu shi ne Allah ba zai bar ƙasar nan a halin da take ba, kowa ya san halin da ƙasar ta ke ciki kuma mun yarda cewa shugabannin nan namu sun yi la'akari da halin da ƙasar ke ciki, sun kuma fahimci cewa su kansu suna neman mafita ba jama'a kaɗai ba, don mene ne amfanin ka yi takara ba ka kai gaci ba?'' in ji Malam Salihu Lukman.
Saboda haka ne Malam Salihu ya ce ƙungiyar G100 ta kira taron tabbatar da wannan gamayya, wanda zai gudana a ranar Talata 18 ga watan Agusta domin kammala shirye-shiryen tsayar da ɗan takara ɗaya da jam'iyyun adawa za su sanya a gaba don kawar da APC daga mulkin Najeriya.
Ko haƙarsu za ta cimma ruwa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan yunƙuri na haɗakar ƴan adawar shi ne na baya-bayan nan a `fagen siyasar Najeriya mai neman yin taron dangi a tsakanin su domin fuskantar jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
To sai dai Dr Yakubu Haruna Ja'e shugaban Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami'ar Jihar Kaduna ya ce a siyasance matakin zai ƙara wa siyasar ƙasar armashi.
''Mataki ne da zai sa siyasar ƙasar ta ƙara ɗaukar ɗumi da jan hankalin masu bibiyar siyasa'', in ji shi.
Dangane da ko haƙarsu za ta cimma ruwa, masanin siyasar ya ce komai zai iya faruwa.
''Za su iya cimma burinsu, amma sai idan sun cire son kai, sun saka ƙasar a gaba'', in ji shi.
"Amma abin tsoron shi ne kar ya zama sun yi kitso da ƙwarƙwata, an kitsa ƙawancen da wasu da ba hakan ba ne a ransu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Sai ya ce jam'iyyun hamayyar na da matsalolin da za su iya zame musu tarnaƙi ga wannan ƙudiri.
''Idan ka duba mafi yawan jam'iyyun na fama da rikicin cikin gida, don haka idan ba su yi da gaske ba, hakan zai iya yin tasiri a sabuwar haɗakar da suke shirin ƙullawa, wanda kuma idan hakan ta faru ya wargaza adawar ma gaba ɗaya'', in ji masanin siyasar.











