Yadda yaƙin Iran ke neman dawowa ɗanye kan Mashigin Hormuz

Hoton jiragen ruwa a teku

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Amurka ta kaddamar da jerin hare-hare da ta bayyana a matsayin masu ƙarfi kan Iran bayan wasu hare-hare da aka kai wa jiragen dakon mai na kasuwanci uku a Mashigin Hormuz.

Hukumar rundunar sojin Amurka, CENTCOM, ta ce manufar farmakin ita ce, Tehran ta gane kurenta kan hare-haren da ta kai kan wasu jiragen ruwa na kasuwanci a wannan yanki na ruwa na duniya.

A martanin da ta mayar, Iran din ta yi Allah-wadai da matakin sojan na Amurka, tana mai cewa hakan ya saba wa yarjejeniyar fahimtar juna da kasashen biyu suka sanya wa hannu a watan da ya gabata.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya yi gargadi cewa Tehran za ta dauki matakai masu tsauri domin mayar da martani.

Wannan sabon takun-saka ya biyo bayan hare-haren da aka kai wa jiragen dakon mai uku a cikin sa'o'i 24 tsakanin ranar Litinin da Talata.

Hukumar Kula da Kasuwancin Ruwa ta Burtaniya, UKMTO, ta ce jiragen da aka kai wa harin sun lalace, amma babu mutumin da ya rasa ransa ko ya jikkata.

Wani jami'in Amurka ya bayyana hare-haren a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, yana mai cewa Iran za ta fuskanci sakamakon abin da ta aikata.

Hukumar sojin Amurkar ta ce matakan da Iran ta dauka suna da hadari kuma sun saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hare-haren na Amurka sun zo ne sa'o'i kadan bayan a ranar Talata Baitul Malin Amurka ya soke wani sassauci da ya yi kan takunkumin da Amurkar ta sanya wa Iran a kan manta.

Sassaucin na daga cikin yarjejeniyar fahimtar juna da Washington da Tehran suka cimma a watan da ya gabata.

Baitul Malin na Amurka ya ce an ba kamfanoni wa'adin zuwa ranar 17 ga watan Yuli domin kammala mu'amalolin da aka amince da su a karkashin rangwamen.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce matakin ya nuna rashin gaskiya da rashin amincin gwamnatin Amurka, tare da jaddada cewa za ta kare muradunta da tsaron kasarta.

Duk da kara tsanantar rikicin, wani jami'in Amurka ya ce masu tattaunawar kasarsa za su ci gaba da kokarin cimma cikakkiyar yarjejeniya da Tehran.

Kasashen yankin ma sun mayar da martani:

Qatar da Saudiyya sun zargi Iran da kai hare-hare kan jiragen dakon mai masu alaka da kasashensu yayin da suke bi ta Mashigin Hormuz.

Qatar ta ce Iran ce ke da cikakken alhakin harin da aka kai wa wani jirgi mai suna Al-Rekayyat, tare da yin kira ga Tehran ta dakatar da duk wani mataki da ke barazana ga tsaron yankin da kuma samar da makamashi a duniya.

Ita ma Saudiyya ta zargi Iran da kai hari kan jirgin dakon mai, mai suna Wadyan, tana mai cewa hakan barazana ne ga zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa da kuma tsaron makamashi a duniya.

Iran ta yi watsi da zarge-zargen.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce irin wadannan zarge-zarge ba su dace da kyakkyawar makwabtaka ba.

Ya ce jiragen ruwa da ke amfani da hanyoyin da ba a tsara tare da hukumomin Iran ba, ko kuma wadanda ke yin katsalandan ga tsarin sa ido a kansu, na kara hadarin aukuwar hatsari tare da kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro a mashigin.

Hukumar Kula da Kasuwancin Ruwa ta Burtaniya ta ce wani jirgin dakon mai ya ba da rahoton tashin gobara bayan wani makami da ba a san ko daga ina ya fito ba ya afka wa dakin injinsa a ranar Litinin.

A wasu hare-hare biyu da aka kai ranar Talata, wani ya fada kan wani jirgin ruwa yayin da yake fita daga Mashigin, amma ya ci gaba da tafiyarsa, yayin da wani jirgin kuma wanda shi ma harin ya fada kansa, ya dan lalace kadan.

Sabon rikicin na barazana ga yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimma a watan da ya gabata, wadda ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Yarjejeniyar ta kunshi kawo karshen tashin hankali, da tabbatar da cewa Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, tare da samar da wani asusun dala biliyan 300 domin sake gina tattalin arzikin kasar.

Haka kuma, yarjejeniyar ta tanadi tattaunawa tsakanin Iran da Oman tare da sauran kasashen yankin game da makomar tafiyar da harkokin Mashigin Hormuz.

Mashigin na daga cikin muhimman hanyoyin safarar makamashi a duniya, inda kusan kashi daya cikin biyar na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta cikinsa.

Iran ta kulle Mashigin bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata a farkon wannan shekara, sannan ta fara neman karin iko wajen kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

Rahotannin kafafen yada labaran Iran sun ce a karkashin sabuwar yarjejeniyar, Tehran da Oman za su rika hada kai wajen tafiyar da Mashigin, ciki har da yiwuwar sanya wani haraji da jiragen ruwa za su rika biya domin amfani da hanyar.