Fitattun ƴan Najeriya da aka daɗe ana damawa da su a siyasar ƙasar

hOTUNA

Asalin hoton, Getty Images,BBC, OTHERS

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A tarihin Najeriya, an yi gwamnatoci da dama da suka yi mulki suka shuɗe. An yi juyin mulki dabam-daban, an yi jam'iyyu, sun yi tashe sannan suka ɓace, sannan shi kan shi kundin tsarin mulkin ƙasar ya sha sauye-sauye.

Sai dai wani abu da yake ɗaukar hankali shi ne yadda wasu mutane suka daɗe suna taka rawa a siyasar ƙasar, lamarin da ya sa wasu matasan suke zargin an hana su samun damar shiga a dama da su a harkokin siyasar ƙasar.

Duk da haka wadannan dadadduna ‘yan siyasa sun zama tamkar madubi a wannan zamani.

Sai dai zai yi wahala a samu waɗanda suka yi siyasar Jamhuriya ta daya da suka rage a yanzu, amma akwai tsirarun waɗanda suka yi Jamhuriya ta biyu, kuma daga ciki akwai waɗanda ake jin ɗuriyarsu har yanzu.

BBC ta suba wasu ƴansiyasa da suka fi daɗewa a fagehn siyasar ƙasar.

Sai dai daga cikinsu akwai waɗanda wataƙila saboda yawan shekaru, an fi jin su ne kawai a wajen bayar da shawara kan harkokin siyasa da mulki, yayin da wasu kuma ke cigaba da damawa sosai a harkar.

Alhaji Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai yana daga cikin ƴansiyasar Najeriya daga arewacin ƙasar da suka daɗe suna siyasa, kuma moryarsu ke amo sosai.

An haife shi a shekarar 1925. Tun kafin Najeriya ta samu ƴancin kai ya shiga fafutukar siyasa a ƙarƙashin jam'iyyar NEPU ta Malam Aminu Kano.

Lokacin da Shehu Shagari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1979, na naɗa Tanko Yakasai a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan hulɗa da Majalisar Dokoki.

Lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin Shagari a shekarar 1983, mutane da yawa sun fita daga siyasa bayan kamun da suka sha a wajen sojoji, amma bayan an sake su bayan Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari, sai Tanko Yakasai ya ci gaba da kasancewa a siyasa.

Haka kuma bayan muƙaman da ya riƙe a matakin tarayya da jam'iyya, ya riƙe wasu muƙamai a jam'iyya da gwamnati a matakin jiharsa ta Kano.

Har zuwa yau yana daga cikin dattawan da ake sauraro idan ya yi magana kan harkokin ƙasa. A kusan shekaru ɗari na rayuwa, yana daga cikin kaɗan da suka haɗa Najeriya ta zamanin turawa da Najeriya ta yau.

Jim Nwobodo

Jim Nwobodo ya zama Gwamnan Jihar Anambra a shekarar 1979 a Jamhuriya ta Biyu a zamanin Shehu Shagari.

Juyin mulkin 1983 ya kawo ƙarshen gwamnatinsa, amma bai kawo ƙarshen siyasarsa ba.

Ya sake zama sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas tsakanin 1999 zuwa shekarar 2003

Har yanzu ana girmama shi, musamman a harkokin siyasar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Sule Lamido

Sule Lamido ya shiga Majalisar Wakilai a shekarar 1979 a ƙarƙashin jam'iyyar PRP a Jamhuriya ta Biyu.

Ya kasance cikin masu fafutukar dimokuraɗiyya a lokacin mulkin soja.

Daga baya ya zama Ministan Harkokin Waje sannan Gwamnan Jihar Jigawa, inda ya yi wa'adi biyu.

Har yanzu yana daga cikin dattawan siyasa da ake sauraro idan ya yi magana kan makomar Najeriya.

Bamanga Tukur

Bamanga Tukur (CON) tsohon ɗansiyasa ne da aka haifa a ranar 15 ga Satumban 1935.

Ya yi gwamnan tsohuwar Jihar Gongola wadda ta ƙunshi jihohin Adamawa da Taraba a yanzu.

Ya sake tsayawa takarar shugaban Najeriya a zaɓen shekarar 1992 a jam'iyyar NRC, amma bai samu nasarar samun tikiti ba.

Daga bisani ya sake riƙe wasu muƙaman siyasa, ciki har da shugaban jam'iyyar PDP a lokacin da take tashe.

Atiku Abubakar

Duk da cewa a lokacin Jamhuriya ta biyu bai riga ya shiga harkokin siyasa ba tsundum, Atiku Abubakar ya kasance yana fafatawa ta bayan fage duk da cewa a lokacin yana aiki a Hukumar Kwastam.

Rahotanni sun bayyana cewa ya sa hannu a lokacin fafatukar yaƙin zaɓen Babana Kinkibe a matsayin gwamnan jihar tsohuwar Gongola.

Daga baya ya shiga tafiyar siyasar Marigayi Shehu Musa Yar'Adua, inda ya koya dabarun siyasar ƙasa.

A shekarar 1999 ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Tun daga lokacin ya kasance cikin manyan ƴansiyasar Najeriya, yana ci gaba da fafatawa a zaɓukan shugaban ƙasa tare da kasancewa babban jigo a siyasar, musamman a ɓangaren adawa.

Bola Ahmed Tinubu

Lokacin da Shehu Shagari yake mulki, Bola Ahmed Tinubu matashi ne mai fafutukar siyasa a tafarkin Cif Obafemi Awolowo.

Ya kuma shiga cikin fafutika a Jamhuriya ta Uku, inda ya kasance gaba-gaba cikin masu fafutikar bayyana cewa Abiola ne ya lashe zaɓen Jamhuriya ta Uku da aka rushe.

Ya zama sanata, daga baya Gwamnan Jihar Legas, sannan ya gina wata babbar tafiyar siyasa da ke tasiri a yankin Kudu masu Yamma, tafiyar da ta taimaka wajen zamansa shugaban ƙasa.

A shekarar 2023 ya zama Shugaban Najeriya, kuma tuni ya fara shirye-shiryen sake neman zaɓen domin wa'adi na biyu.

Kabiru Gaya

Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya ya fara siyasa ne a Jamhuriya ta Biyu, inda ya kasance a cikin jam'iyyar National Party of Nigeria wato NPN.

Daga baya sai ya koma jam'iyyar National Republican Convention wato NRC, inda ya takarar gwamnan Kano, sannan ya samu nasara.

Ya yi mulkin jihar Kano daga Janairun 1992 har zuwa watan Nuwamban 1993.

A babban zaɓen 2007 ne Kabiru Gaya ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Kudu, sannan ya sake komawa a zaɓen 2011, har zuwa shekarar 2023 da aka doke shi.

John Odigie-Oyegun

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

John Odigie-Oyegun bayan ya bar aikin gwamnati, ya shiga harkokin siyasa kuma ya zama gwamna na farko da aka zaɓa a jihar Edo State a ƙarƙashin jam'iyyar Social Democratic Party wato SDP tsakanin shekarar 1992 zuwa 1993.

Daga baya ya shiga ƙungiyar National Democratic Coalition (NADECO), wadda ta yi adawa da mulkin soja na Ibrahim Babangida bayan ya soke zaɓen ranar 12 ga Yuni, 1993.

Bayan dawowarsa daga gudun hijira, Cif Oyegun ya ci gaba da fafutukar siyasa, sannan daga baya ya zama ɗaya daga cikin jagororin jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP), wadda daga baya ta rikide zuwa Action Congress.

A shekarar 2014, Cif Oyegun ya shiga wata haɗakar jam'iyyu da ta kafa All Progressives Congress (APC), inda ya zama shugaban jam'iyyar na ƙasa na farko. A ƙarƙashin wannan jam'iyya ne marigayi Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasar Najeriya.

Yana cikin waɗanda suka shiga haɗakar siyasa domin kafa jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), da nufin kayar da shugaban ƙasa mai ci Bola Tinubu da kuma jam'iyyar APC.

Rabiu Musa Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwas ya fara siyasa a ƙungiyar Peoples Front a ƙarƙashin jagorancin Shehu Musa 'Yardu'a, sannan a shekarar 1992 zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai, inda ya zama mataimakin shugaban majalisar.

Tun daga lokacin ne ake damawa da shi a harkokin siyasar Najeriya, har zuwa yanzu da yake takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar NDC.

Sauran waɗanda suka daɗe a siyasar su ne: Shugaban majalisar datttawan Najeriya na Jamhuriya ta Uku Iyorchia Ayu da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Abiola Babagana Kingibe da Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Kanti Bello da Liyel Imoke wanda daga bisani ya yi gwamnan jihar Cross River da sauran su.